chapter fifty

1.4K 92 7
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

50

Haka rayuwa yacigaba da tafiya Layla na samun kulawa sosae..ba bangaren su Ummi ba..ba kuma ga bangaren daddyn nata ba..wasu lokutan har tausayi yake bata yanda taga Yana kaunar cikin nn..sai yasa cikin a gaba yaita surutunshi shi kadai yana murmushi shi bai yadda ba yana mgn da babynshi...kullum zai kaita school snn zai maidata gida...duk take sha'awan cin wani abu kuwa tana kiranshi duk inda yake Kuma duk abinda yake haka zai bari yazo ya kawo Mata...suna rainon cikinsu sosae Kuma bai hanata karatunta tunda ba wani laulayi takeyi sosae ba..

Kayan babies Kam Taheer na siyansu tamkar bai San zafin neman kudi ba...duk abun da ya gani yai mishi kyau sai yayi order indai abindaya danganci yara ne...banda Wanda kusan kullum sai ya dauketa sunje shopping Kuma duk siyayyan na kayan babies ne...duk abinda zai siya kuma na Mata yake dauka...Layla tayi tayi dashi akan su ringa daukan unisex yanda ko ba mace ta Haifa ba zasuyi amfani dashi amma inaa...kullum cewa yake shi jikinshi na bashi mace zata Haifa dukda scanning din da sukai guda biyu duk namiji yake nunawa..

Lokacin da cikin nata ya isa antenal kuwa da kanshi yakeyi Mata komai...duk wasu tests da akeyi yana Mata...har su urinalysis Yana zuwa da Combi9 dinshi har gida yayi Mata...sauran tests din Kuma irinsu PCV..VDRL da bazasu yiwu a gida ba sai ya dauketa suje clinic dinshi ayi Mata...Layla dai na ganin tsabar soyayya da kulawa a wurin Taheer..at times har tunani take kilan tana haihuwa zai dena sonta ya dena kulawa da ita..sbd yanda taga yake bala'in son cikin nn abin har mamaki yake bata..

A bangaren su Ummi ma Kam baa barsu a baya wajen kulawa da ita ba...time to time ummi zatayi Mata girki irin na gargajiya Wanda tasan mai ciki zataso snn suje har gidan su Kai Mata..watarana Kuma su aika driver yakai ko Kuma Taheer din yaje ya amsan Mata...babu abinda zatace ma Allah daya wuce Alhamdulillah.. kullum cikin godiyan Allah take for such a blessing...fatanta Allah ya sauketa lfy itama taga me zata Haifa..tanaso taga babyn da ita zaiyi kama koda babanshi..

Lokacinda Hanna ta haihu cikin Layla nada watanni 5 ciff a duniya...zuwa lokacin Kuma cikin nata ya fito sosae...haka sukasha suna da katoton cikinta abunta...yarinya taci sunan mum din mahaifinta Aisha..zasuna kiranta da Hanan...

Bayan haihuwan nata da kadan Kuma sukayi exams na second semester...wnn karon zasuyi hutun 4 weeks kafin su juya another session...haka rayuwa yacigaba da tafiya musu har zuwa yanxu da cikinta ke wata takwas...yana shiga na takwas din dama ummi ta dage kan lallai sai Taheer ya maidota gida don ba iya kulawa da ita zaiyi ba..haka ya hada kayanta da nashi snn suka tattara suka koma gidan...shima hankalinshi zaifi kwanciya idan tana tare dasu don sau tari idan zaije clinic hankalinshi bai kwanciya ya barta ita kadai a gida..yanxu kuwa ko bai nan yasan zasu kula mai da ita sosae.
Dukda suna gidan kuma bai fasa kulawa da itan ba..duk abubuwan da yake Mata a baya ba Wanda ya bari..ko abinci indai yana gida saidai ya bata a baki..wasu lokutan har kin zuwa aiki yakeyi sbd ita..daidai da wanka saiya taimaka mata tun ummi na fada har ta hakura ta zuba musu idanu kawai...yanda yake rawan jiki kan cikin nn har mamaki yake bata..sai kace a kanshi zaa fara haihuwa..ita kuwa umma sam bata mamaki don ta riga tasan irin kaunar da Taheer din kema Layla..dn haka dolene tasan yaso cikin nn fiyeda komai...
Nafeesa kam har yanxu bata samu zuwa Abuja ba sbd karatun yara..tanata so tazo ko kwana biyu ne suyi sbd ta samu taga Layla amma umma tace suyi zamansu kawai..idan Allah ya sauketa lfy sai suzo..saidai suna wayan kusan kullum da ita...haka su Al'ameen ma duk sun kagu ta haihu suzo suga babynsu...

Yau Saturday da wuri Taheer ya baro clinic zuwa gida..tun da ta fita bai samu yin waya da itaba as yanata Kiran wayan nata bata answering..gaba daya sai hankalinshi ya tashi don yana tunanin ko wani abun ne ya sameta amma daya Kira umma sai ta tabbatar mai da cewa lfy Lou take saidai tun dazu tana daki tanata bacci...dukda haka shidai baiji hankalinshi ya kwanta ba don haka ya dawo gidan don yaga hakinda take ciki.

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now