BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

1.9K 163 12
                                    


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is dedicated to yhu Aisha Gazara Mrs. Bello, Allah ya kara dankon love yasa bad'i war haka mu gwangwaje, Allah ya barku tare har Aljannah, much love dear*

*028*

Kowa ido ya zuba mata yana kallo har shi uban gayyan kawai se ta mike ta fice da sauri, tsaki yaja kan ya kama hannun matarshi suka koma mazauninsu, nan aka fara niyyar cin Abinci serve ur self ne, kowa mikewa yakeyi ya d'ibi abinda ya san ze iya ci ga abincika kam kala kala, kai na dafe hango Rukayyah farouk, bushira, herpcert sabee'u, Maman two girls da cool ramcy tsaye kowacce rike da plates d'inta tana jiran layi ya zo kanta, ban hankara ba fa naji an bankad'e ni har takadda da birona yayi kasa, a zuciye na d'ago se naga Adama Aliyu, maman khalil, khadija Queen da Kawata Aisha ne tuni sunyi gaba bama su san sun bangaje ni ba, dariya na fara ganin suna kokarin yi ma maijidda da Zuwaira Musa satan layi.

Girgiza kai kawai nayi na juya kenan na hango maman habeebty, rabiya basiru, Aysha Adam, hussaina A sidi da khadeeja hussaini sun shige chan lungu suna dambe akan cinyar kaza🤣🤣🤣, juyawa nayi na fara neman Namesy na zahra iliyasu, faizadikko, ummu Ameer, ummu haneef da ummu Aslam Don su zo su raba su amma duk ☹️ ba wadda ya kulani se ma nunawa da sukayi basu sanni ba don kowacce ta ciko plate da kaji😋.

Ban hankara ba na juya naga abinci ya kare kap neman wadda ze tsammin nashi na fara, Hanifatulkhair(didi) na fara nufa ta juya kaman bata sanni ba tayi gaba abinta🥺 Mmn habeebty, mommy Anwar, Mrs Abmin, hajara Aminullah, hadixa da shafa'atu duk kowa ya hanani ya juyan keya😭.

High table na nufa da sauri kawai naga Smeenarl, meenerl, hasfatsafyan da sameera Ahmad sun kwashe na gaban Ango kam sun fece ganin yana ta yanga ko kallon inda abincin yake be yi ba, se bowl d'in fruit salad da ya d'auko tare da sa spoon ya d'ibo kaman ze sha kuma se ya juya ya kai bakinta, d'ago ido tayi ta kalleshi da ido ya nuna mata spoon d'in alamun ta sha, a hankali ta bud'e bakinta ya saka mata, su zarah ne suka takalo camera man suna nuna mishi high table, mastowa yayi ya fara haskasu ko a jikinshi se ci gaba da bata da yayi itace ma kunya duk ya hanata sakat dukda ma hankalin kowa be kansu se su inna suna yagan kaza suna kallon kwakwap.

A hankali tace "na koshi hamma" kasa kasa ya kalleta yace "are yhu sure?" Tace "Eh" kafanta ta ke ta lankwasawa tun kan ya fara bata fruits salad d'in ya lura, cikin kasa da murya yace "are yhu okey? Your legs me ya samesu?" Cikin daburcewa kaman wata marar gaskiya Tace "ba komai" Kau da kai yayi ba don ya yarda ba, ana gama asalin dinner aka fara shirin tashi yanzu ma tare zasu tafi, duk tayi ta duba su zarah bata gansu ba bata ma san sadda suka fice ba.

Ganin ya mike yana ta sallaman manyan bakin da suka zo yasa itama ta mike ta tsaya gefenshi iyakaci tayi murmushi shi ke aikin godiya da sallama, kan kace kobo hall kam ya watse kaman ba yanzu aka gama fad'an kaza ba😜 Su Mmn Nurr da kawata jamila idris (ummu Afreen) har guzuri seda sukayi, se tsiraran abokanshi da baza'a rasa ba, tsayuwan da tayi se ya kara karawa kafan gajiya, har wani jiri take ji yana kwasarta, juyowa yayi ya kalleta ya kuma kallon kafan kan ya kamata ya zaunar da ita.

Da tsananin mamaki take kallonshi don ganin ya durkusa kan gwiwanshi, zarazaran yatsunshi ya sanya a hankali a kan fatar kafanta wadda sanyin hannun ya sa ta d'an razana tsikar jikinta suka tashi, takalmin ya cire mata ya fara mammatsa mata kafan zuwa kan yatsunta lumshe ido tayi yayinda sauran abokanshi suka saki ihu, ko kula su be yi ba seda ya gama ya koma d'ayar kafan ya d'an mamatsa mata kan ya kawar da takalmin.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now