BABI NA BAKWAI

1.8K 135 17
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
              •Gureenjo6763 on wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is dedicated to all my friends (I mean readers of my book) duk wani me son littafin nan wannan page d'in nashi ne, kuyi yadda kuke so, Ina jin daad'in comments d'inku sossai, Allah ya bar zumunci ❤️❤️ big hearts from here*

                            *07*

Seda me napep d'in ya fara tafiya kan yace "hajiya ina muka nufa?" Cikin sanyin murya nace "gandun albasa" Haka kawai na iya furtawa kan na fad'a tunanin me yasa Dr. Abdulraheem taimakana? Ya gane ni ne? Ko kuwa dai taimakone irin ta addini da ya had'amu? Allah masanin gaibu, haka na ci gaba da sake sake ba tare da na ci gaba da kukan ba, gobe monday we are having his class as early as 8 so dole nayi bacci da wuri don na ci alwashin In shaa Allahu bazan sake missing class d'inshi ba.

Ya rab!! Yau ma mutumin nan bakake kaya ya saka, wai ko Lafiyanshi da bakaken kaya kaman wani shaid'an? Bari In kira zarah kwana biyu bamuyi lectures ba so bamu had'u ba, yau ma haka gashi bamuyi waya ba, wayana kirar Tecno M3 na fiddo na danna mata kira ringing biyu ta d'aga "hey besty ya kike?" Nace "Lafiya kalau besty ya gd?" Tace "kalau wallahi, kina raina besty tun d'azu nake shirin kiranki se kika rigani" Ina murmushi nace "ba wani nan kawai don kin ga na riga kira ne".

"Allah ba haka bane ki tambayi ummu kiji se maganan ki nake tun d'azu" ta karasa da shagwa'ba kan nayi magana naji muryan babbar mace cikin kamala tace "Assalamu Alaiki" diriricewa nayi wato seda zarah ta bai wa ummu wayar seda nayi gyaran murya nace "wa'alakumussalam ummu Ina yini?" Tace "Lafiya kalau ya mutan gidan?" Na amsa da "Lafiya kalau ummu" Tace "Toh ma shaa Allah, auta bata fitinarki da surutun ta na tsiyan nan ta hanaki karatu ko?".

Murmushi nayi kan nace "ko d'aya ummu Ai zarah na da daad'in zama" tana murmushi tace "Toh masha Allah, Allah yayi muku albarka a gaida mutanen gida" na amsa mata da zasuji mun gode, kan ta mikawa zarah wayan muka ci gaba da hira ta dinga jaddadamin In zo da wuri gobe In zo da wuri da haka mukayi sallama.

Ina isa gida nacewa umma "umma na dawo" ba tare da jiran amsanta ba na wuce d'akin mama a parlor na taddata itama haka na ce mata ba tare da na jira amsanta ba na fad'a d'aki tare da zubewa kan gado, yau umma ce da girki kuma bata yarda in taimaka mata da komai da kanta take kayanta hakan yasa na kwaso takarduna na fito tsakar gida na fara karatu ina cikin yin karatun su ikhram suka dawo daga islamiya.

Da gudu suka nufo kan taburman suka zauna ko wacce na ban labarin abunda ya faru yau, Ina ta murmushi nace "Kai ikhlas surutunku se ku, kuje ku tu'be uniform nan, baku da assignment na school ne?" Ikhram tace "muna dashi Anty Noor bari inje In kawo ki gani?" Ta mike kenan umma ta fito daga d'aki zare ido tayi kan ta daka musu tsawa "Kai baku da hankali??? Wa yace kuyi mata magana ban hanaku ba?" A tsorace yaran sukayi wurinta ta kuwa kama kunnensu ta murd'e suka saki kuka.

Idona na kanta amma hawaye ne ke zuba "Anya uwata ce" ba tare da ta kalli inda nake ba ta jasu sukayi ciki, karatun da banyi ba kenan na tattare takardun nayi ciki, har yamma ina d'aki ko parlor ban leko ba Ina ji suna ta hayaniya yayinda mama da umma ke hiransu suna dariya Ina ji baba ya dawo ban fita ba, a d'aki nayi magrib da isha kan na fita d'aukan abincina.

A kan taburma na tararda ahalin gidan zaune suna hiransu gwanin sha'awa baba na ta wasa da dariya dasu ikhram wadda hakan ya sani tunawa da yarantata da mahaifina me sona da kauna na, har na d'auko abincin na fito bayan mama ba wadda ya kalli inda nake dukda na musu sannu maman ce kawai ta amsa.

A parlorn na yada zango ina tunanin wani irin iyaye nake dashi da basu yarda da kaddara ba? Kode imaninsu be cika bane ba? Da sauri nace "Astagfirullah, Allah ka ganar dasu" da ba don mama ba na tabbatar da na jima da collapsing, a haka na tuttura abincin ba wai don Ina jin daad'inshi ba sbd kawai kar nayiwa kaina illah da yunwa, Ina gamawa na mike na fita da kwanon na dawo nayi sallahn isha na bi lafiyan gado.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now