BABI NA ARBA'IN DA BIYAR

1.9K 151 22
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                           *045*

"Marid ana iya ce musu maradah "rebellious" kaman yadda suka zo a cikin alqur'ani me girma, cikin sura As-saffat Aya ta 7 (37:7) in da Allah mad'aukakin sarki yace "And to guard against every rebellious (marid) devil" marid suna ne na larabci ana iya ce musu giant a turance, suna da karfi they are said to be very arrogant yawancin rayuwansu sunfi yinshi a ruwa, kogi, fadama da duk wani gulbi ko hanyar ruwa ko inda ruwa yake, me kyau ko marar kyau, suna da hatsari very dangerous In aka ta'basu ko mutum ya shiga taskunsu.

Su ba aljanu bane da suke shiga bil Adama domin soyayya kaman jinnul Ashiq sede suna iya kasacewa jikin mace ba tare da ta sani ba kuma sannan suna hana mace jin daad'in rayuwa kaman yadda kowa ke yi, wannan na daga cikin hatsarinsu basuyi rayuwar soyayya ko na aure da mace kaman ashiq ba haka kuma basu barta tayi rayuwan da kowa ke yi ba, suna iya zama a jikin mutum har ya mutu suna kunta ta mishi ba tare da ya sani ba duk da wani sa'in laifin mutanen ne.

Marid marada a jimlance suna iya  abubuwa dayawa kaman firewa(fly), dive, destroying abu komai girmanshi, jinsin aljanu ne da suke cikin waenda suka taimakawa Annabi Sulaiman (A.s) wurin kawo throne na queen of shibah, suna da kabila wato (tribe) suna da iyalai Don suna auren junansu su hayayyafa kaman mutane Haka kuma sune na biyun karfi da iko cikin jinsin aljannu In aka cire ifrit. Kaji yadda marid suke"

Cikin gamsuwa da bayanan baba fufore Malabo yace "Allah ya rabamu da sharrinsu" baba ya amsa da "Ameen" hira suka d'an ci gaba dayi baban na tambayanshi yanayin ummu yana bashi amsa anan ne ma ya fitar da abinda ke ranshi ya nuna 'bacin ranshi sossai akan abinda ummu tayiwa Iman kuma ji yake har lokacin ranshi be yi sanyi ba, baba ne ya katseshi da nasihohi akan girman iyaye sbd haka duk abinda zasu maka baka da abinyi se hakuri sede In sun haneka bautawa ubangijinka, "ba'a fushi da iyaye kaji" baba ya rufe da hakan, Kai ya gyad'a cikin gamsuwa nan suka ji ana kiran la'asar.

Sallah suka fita sukayi daga nan baba ya zauna rumfarshi na tsakar gida yara suka fara taruwa Don d'aukan karatu kaman ko yaushe, shi kuwa malabo ciki ya nufa direct d'akin hajja ya zauna suka fara hirar yaushe gamo dayake d'akin da ta sauke Iman yayi masauki minti minti se ya kalleta daga karshe ma hannunshi ya sanya ya kama nata ya riqe dukda sanyin da hannun yayi kaman ya fito daga kankara ko yana ciki.

Tsokananshi hajja ta dingayi wai ita tana kishi gaskiya itace baya sonta, sede yayi dariya kawai "ka kuwa shiga wurin mutan gidan kun gaisa?" Yace "a'a hajja" Tace "ya ko kamata ka tashi ka shiga In ba haka ba yanzu se kaji karamin magana ya zama babba" murmushi yayi yana mikewa yace "bari In gaishesu In zo kar su samin hajjana gaba" murmushi tayi ya fita me makon ya shiga cikin gidan se ya nufi waje ya d'auki mota ya shiga cikin gari.

Wurin da ake gashin kaza ya yada zango ya kuwa sayi dayawa har leda takwas ko wani leda kuwa kaji biyu ne ciki, se godiya me kazan yake cikin jin daad'in wannan ciniki, murmushi kawai yayi ya ja mota, gidan ya dawo ya dinga shiga part part suna gaisawa gidan se murnan ganinshi suke don malabo mutum ne me fara'a da son mutane in kaga yana rashin fara'a to yaga en mata ne musamman na jami'ar bayero. Duk inda ya shiga suka gaisa se ya ajiye musu leda d'aya, part d'in hajja ya shiga a karshe ya ajiye mata ledanta.

Godiya tayi mishi sossai, murmushi kawai yayi yace "Hajja ya kamata a cirewa Hayatee kayan nan a sa mata marar nauyi na san da idonta biyu tayi ta mitan ya takura mata kenan" murmushi hajja tayi tace "Toh kace mana kawai In baka wuri" dariya yayi yana dukar da kai fita tayi da ledanta a hannu, kallon iman ya tsaya yi cikin tausayawa da shaukin so yana sonta har be san adadi ba Haka kuma tausayinta, kab rayuwanshi be ta'ba tausayin mutum kaman yadda ya tausayawa Iman ba.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now