BABI NA ASHIRIN DA 'DAYA

1.8K 164 6
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                         *021*

Se da ta kwanta bacci tukun tunanin auren da baba yace za'a d'aura mata a jibi ya dawo mata, ta fara tunanin ko da wani irin miji kuma Allah ze had'ata? Me mutunci ne ko akasin haka, shi yace yana sonta ko baba ne ya roke shi ya aureta? Har ga Allah tana tsoro sossai irin sossai d'in nan wadda take so yake sonta ma ya aka kare bare kuma wadda bata sani ba be santa ba? Hawaye ne ya gangaro mata da sauri ta goge ta furta a fili "na gaji da kukan nan haka" ta mike ta fad'a toilet tayo alwala tare da fitowa ta tada sallah.

Ta jima tana nafilfili In tayi sujjada se tafi minti ashirin tana yiwa Allah kirari tana kai mishi kukanta seda taji ta samu natsuwa kan ta mike ta hau gado ba 'bata lokaci kuwa bacci ya saceta, ta manta when last tayi bacci cikin kwanciyar hankali taji baccin ya mata daad'i irin yau da kyar ta tashi sallan asuba ta lalla'ba tayi kan ta mike mama ce da girki hakan yasata nufan kitchen kai tsaye aiko ta samu har ta hura icce har kasa ta duka "Ina kwana mama?" Mama tace "Lafiya klau iman ya kika fito yanzu kije ki kwanta ki huta na san har yanzu jikinki be yi karfi ba".

Murmushi tayi kan tace "Mama na ji sauki fah, school ma zan shiga ina da aji karfe takwas" Mama tace "a'a wani makaranta kuma iman? Yaushe aka sallamoki daga asibitin? Baza ki kara hutawa ba" Shagwa'be fuska tayi tace "Mama na warke fah In ban je ba akwai matsala wallahi gashi yayi test ina asibiti" Mama ta girgiza kai kan tace "ke kika sani, kije ki zauna In fara sa miki ruwan wanka In yaso kika juye se in d'aura sanwar" juyawa tayi ta d'auki tsintsiya ta fara share kasar gidan.

Tsab tayi shara mai kyau ta gama kan ma ta gama Mama ta juye mata ruwan a bucket ta d'auka ta shige toilet bata wani 'bata lokaci ba ta fito ta shirya duk de kayanta yawanci materials ne atampha In za'a mata se na dubu ko dubu da biyar wato robber kenan shiyasa gwara ta d'inga material d'inta, cikin wani fari da jan material ta shirya dayake ta d'an yi rama se rigan ya nemi yi mata yawa.

A haka de ta sanya ta sa red robber himar d'inta ta fito da farin flat shoe d'inta da kuma karamin hand made side bag d'inta, sama sama ta sha kunun da mama tayi bata ma tsaya jiran d'umame ba ta fice, In tace zata hau keke napep ba abinda ze hanata makara hakan yasata hau machine takwas saura minti uku ya sauketa a kusan hall d'in da zasuyi lectures d'in.

Waro ido tayi ganin shi a kafa da alamu ya d'an tsaya office kuma a chan ya bar motan, da hanzari yake tafiya irin de tafiyar maza masu ji da jini a jika Ai bata san sadda ta fara gudu ba har yayi stepping kafanshi cikin class ya juya da nufin rufe kofa kenan ya hangota tana gudu se ya dakata tana isowa ya kauce ta shige kan ya ja kofanshi a bayanta ajiyar zuciya ta sauke tana hakki, se kuma ta d'aga kai don kallonshi se carab suka had'a ido, ko second idonshi be kai cikin nata ba ya kawar da kanshi tare da haurawa stage.

Da mamaki ta karasa ta zauna me ke damunshi haka? Ko de ita ne take ganin kaman 'bacin rai shimfid'e a fuskanshi? Kallonshi ta ci gaba da yi as usual black pants ne jikinshi da Armani shirt baki se wasu shegun timberland suma bakake sanye a kafanshi gashin nan ya sha gyara har ya gaji se yau taga abinda d'alibai da wasu lecturers d'in ke kiranshi yayi daidai da yanayin shi da komanshi. a kan lips d'inta ta furta.

"Youngest biologists" bata hangi zarah ba duk jujjuyawan da tayi kuwa se kawai ta bud'e littafinta ta fara jotting abinda yakeyi, tabbas ranshi a 'bace yake ranan Kuma cike yake da damuwa sbd jiya bayan isowanshi hamna ta iso, dukda yayi mamakin ganinta amma se be nuna ba, sema shareta yayi yaci gaba da harkokinshi dayake da ya dawo be shiga gida ba yasa bayan isha yayi wankanshi tare da shiryawa ya fito parlorn sama.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now