BABI NA TALATIN DA UKU

1.9K 157 12
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
         *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                             *33*

Murmushi yaki barin fuskanta har ta gama shiryawa tare da yafa katon mayafi ta rufe fuskanta ta zauna kan gado, a parlorn kuwa yana fita kaman ya sani Anty rahma ta fara mishi tsiya kara had'e rai yayi yana hararanta. Sauran friends d'inta da na ummu biyu da suka kawo kayan se wasu daga cikin en uwan iman se dariya suke.

'Dakinshi ya shige yana shiga Hamna da Umma na fitowa baki bud'e suke kallon kayan, har muryar hamna na rawa wurin cewa "wannan kayan fa Anty rahma?" Murmushi Anty rahma tayi kan tace "na Amaryarki ne mijinku ya mata" bata san sadda ta furta "kambalastii!! Yanzu duk wannan kayan er kutumar uban chan??? Wai me hamma ke nufi da ni ne? Wato kaskanci ya shirya nuna min to wallahi Allah ya isa ban yafe ba" tsabar takaici abinda zata fad'a ma bata sani ba.

Akwati shidda ya mata don bala'i ba irin mitan da batayi ba yayi rantsuwar baze kara ba amma shine yanzu yayiwa Banzar matarshi goma sha biyu kuma sunfi nata kyau, da karfi ta fashe da kuka tana kallon ummanta tace "wallahi umma ba zan yarda ba ki san yadda zakiyi dani Allah bazan yarda ba wani irin cin fuska ne wannan??? Ko fah kayan fad'ar kishiya be min ba, duk wacce za'ayi sede ayi ni kam se an raba kayan nan biyu an bani d'aya".

Dafe kai Anty rahma tayi tana kallon umma dake rungume da ita tana buga mata baya se kace wacce akaywa mutuwa, tana cewa "dole ma hakan za'ayi Ai wallahi duk cikinsu ba wadda ya isa ya wulakantamin ke ya zauna lafiya har shi Hamma Ahmad d'in, bari kiga In kira Addan, In ni Abdulraheem ya rainani Ai ita be isa ya rainata ba".

Ummu ta kira cikin masifa tace "Adda zama da d'anki fah ba dole bane ba In bakwa bukatar mu a family d'inku se mu tattara muyi gaba haba wannan wulakanci da kaskanci har Ina" ummu tace "me ya faru hafsat?" Umma tace "Ki zo gidanshi yanzu ki ganewa kanki" ba musu umma ta mike ko sashin Abba bata shiga ta fad'amishi ba ta fito ta shiga motanta ta ja se gidan.

Nan ta gansu tsaye cirko cirko Anty rahama kam mamakinsu ne ya kusa kasheta taya za'ayi a raba kayan da akayi Don Amarya a ba kishiyarta Ai Abinda baze ta'ba sa'buwa ba kenan, bayanin da sukeyiwa ummu ne ya sa ta dawowa tunaninta, bayan sun gama fad'ar Abinda zasu fad'a ummu ta kalli Anty rahama tace "ke rahama raba akwatunan biyu, hamna za'bi wadda ya miki" daga bakin kofa sukaji ance "excuse me!!!" Duk juyawa sukayi se suka ga Abba.

Se a lokacin Abdulraheem ya fito ashe tun fara abin yana jinsu yayi niyyar ya fita ya sassa'ba ma hamnan se kuma ya fasa jin sun kira ummu kar ta zo taga abinda yayi niyya laifinshi ya karu a wurinta shi wallahi yanzu har ga Allah tsoron Ummu yake, mamakin halinta na yanzu kuwa yana ga har kwanan gobe baze dena mamaki ba, the silent, loving and caring ummunshi ta dawo wuta yanzu, "Am rahama da kud'in wa kikayo sayayyan nan?" Inji fad'ar Abba, Anty rahama tace "Abba kud'inka" yace "good, d'auki kayan ku shigar mata" jiki a sanyaye su Anty rahama suka fara shigarwa.

Juyawa tayi kan Abdulraheem tace "Don ubanka In ni na tsuguna na haifeka kuma Nono na ka sha kayiwa hamna irin kayannan inga uban da ya isa ya hanaka" kanshi ya dukar kasa idanunshi na kad'awa a lokaci d'aya cikin sanyin murya yace "In Shaa Allahu" ya juya kawai ya shige d'akinshi, Abba karan kanshi se da yaji hawaye ya cika idanunshi me Rashida ta zama ne? Zarah kam kuka ta saka musu, juyawa Abba yayi ya tafi, ummu ta rufa mishi baya bata so hakan ba ta so Abdul ya ja da ita ta kikkifa mishi mari ko zata rage abinda ke cinta a rai, su hamnan ma basu so hakan ba haka dai suka juya suka shige suna kwafa, bayan sun gama shigar da kayan duk suka fice kowa rai ba daad'i suna kuma jima Iman tausayi Don kiyayyar uwar miji ba karamin abu bane.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now