BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI

2K 153 35
                                    


               🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                           *047*

Daga bakin kofan d'akin ya taka birki yana ambaton Innalillahi wainna ilaihi rajiun a lokaci d'aya yana lumshe idanunshi he's not that strong In aka zo batun Iman baze iya ba, baze iya ganin irin wannan azabtarwa da suke mata ba, baba ya mikawa magungunan ya sa kafanshi da niyyar juyawa baba fufore yace "Abdulraheem" dakatawa yayi zuciyarshi na tsananta bugawa, "shigo se ka taimaka mini" juyowa yayi ya shigo yana kau da kai, mama da ummu da kuma hajja gana kuka kawai suke.

Wani irin sauyawa halittarta yayi idanunta sun koma jajajir kaman an zuba musu ruwan borkono bakin kuma ya koma Ash bakinta baki kirin hannayenta da kafafunta duk a juye kitson kanta da kanshi ya dinga warwarewa gashin na bazuwa, cikin d'aga murya baba ya fara magana "Tun muna daad'i daad'i daku ku tattara ku fita harkar bayin Allah nan laifi ne sun muku amma shekaru ashirin da hud'u yaci ace kun gama d'aukar fansarku karku shiga hakkinsu kuma, ku fice tun kafin na fara kona ku da ayoyin Allah" wani irin dariya cikin murya marar daad'i ta sake har tana d'aura hannu kan baki tsabar dariya gashi muryan a shake kuma na maza.

Murmushi baba ma yayi yace "Ohk fine abinda kuka za'ba kenan? Alright" Wasu adu'o'i ya fara yana kai aya ya kama ayoyin Allah kaman na cikin suratul baqarah, saffat, A'araf da jinni da dai sauransu nan fah tun suna dariya har ta fara ihu na fitar hankali tana d'agawa sama tana fad'owa ita kad'ai In tayi ihu se d'akin yayi wani girgiza duk wani abu na fashewa seda suka fashe a d'akin komai seda ya juya upside down, cikin muryan maza me amo da karfi ta fara magana "dakata!!!! ka dakata!!!! Ka dakata naceee!!!" Kin shiru yayi se ma wani kwal'ba da ya bud'e wadda had'i ne na abubuwa dayawa irin su za'afaran, zaitun, habbatussauda, khaltuffa, dawa'ujinni da dai sauransu ya watsa mata wani kara tayi ta d'agu sama ta bugu da gini ta sake dawowa kan gadon ta fad'i tare da murd'ewa kaman maciji se ga Malabo na hawaye.

Cikin muryanta na asali tace "wayyo hamma" tana mika mishi hannu da sauri ya kama hannun yace "hayatee kece?" Tace "ka taimakeni ciwo wayyo" baba fufore yace "kauce Abdulraheem ba ita bace duk cikin munafurcinsu ne yau ko ni ko ku" Abdulraheem ze yi musu Don ganin yadda take kuka tana ta nanata wayyo wayyo se yaji muryan farko kaman ta mazan nan tace "ba fa zan barta ba Ina rantsuwa da jinin d'ana da kuma namijina yadda uwarta ta rabani dasu se na rabata itama da nata, sandin mutuwar markuzz mijina ma ya mutu Don haka se na ga bayansu".

Baya Abdulraheem ya matsa hawaye na ci gaba da zuba mishi yana gogewa duk wani me imani baze juri ganin yadda suke mata be zub da hawaye ba gabad'aya ta fice a hankalinta da kamanninta kaman ba ita ba, artabu aka ci gaba dayi tsakanin baba da wannan aljana Zulhaya'i seda suka kai ruwa rana gabad'aya ta wahalardasu Don daga baya neman illata baban ta fara amma dayake yace Allah so ba yadda ta iya dashi daga karshe ta fara kuka a galabaice tana neman ya tsaya zata fita kar ya gama koneta ta tuba.

Se sannan ya dakata yace "toh bismillah muna jiranki, ta Ina zaki fita? Tace "zan fita ta hanci" yace "kiyi alkawari bazaki kara ra'banta ko dawowa inda suke ba" Tace "nayi.... nayi" yace "ni kuma nayi alkawarin duk radda kika sake kusantar zuri'ar nan se na kasheki har lahira da ayoyin Allah" Kai ta dinga gyad'awa kan iman ta saki wani wawan atishawa har sau hud'u a jere kan ta koma ta fad'i kan gado, zama Malabo yayi bakin gadon tare da kama hannunta yayi kissing wasu Hawayen tausayinta na sake zuba akan kuncinshi, ajiyar zuciya manyan suka sauke baba ya kalli baba fufore yace "mun gode Allah ya saka maka ya biyaka da gidan Aljanna" murmushi yayi yace "kaman yadda Abdulraheem yake jika gareni Haka itama don haka ba godiya don nayiwa jikata Abu, yanzu shikenan Sun rabu da ita da izinin Allah, kai Abdulraheem zan baku wasu magunguna ka tabbatar tana anfani dasu zuwa en wasu lokuta kad'an".

NOOR IMANWhere stories live. Discover now