BABI NA ARBA'IN DA UKU

2.2K 169 20
                                    


                   🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
        *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*wannan page d'in is a dedication to duk wani masoyin littafin nan duk naga comments d'inku kuma naji daad'i sossai na gode da kulawarku, kaman yadda na fad'a a shafin da ya wuce shawara nake nema kuma Alhamdulillah kun bani had'in kai wurin fahimtar junanmu dama ba ta yadda za'ayi ayi tafiya tare ba'a fahimci juna ba, Toh masu cewa a bi littafi a tsanake kar ayi rushing su sukafi yawa Don hakan shawaran za'a d'auka zan dingayi ko wani bayan kwana d'aya Allah ya bani iko, Ameen na gode kwarai love you guys🥰🥰🥰*

                          *043*

Ita ta fara motsawa da asuba da niyyar tashi wadda hakan yayi sanadiyar tashinsa bud'e idanunshi yayi yana kallon ta dukda duhun dake d'akin yasa baya iya kallon fuskanta, a hankali ta zame wai Don kar ya tashi ta sauka bata shiga toilet d'inshi ba kawai ta nufi room d'inta, seda ta fita tukun shima ya mike ya fad'a toilet d'inshi wanka yayi kan yayi alwala ya fito bayan ya zura jallabiyarsa milk color daga cikin bayin.

Massallaci kawai ya fice, bayan ya dawo be duba d'akinta ba kawai ya shige room d'inshi kwana biyu be yi exercise d'inshi ba har ji yayi ya fara gaining weight hakan yasashi shiryawa cikin Armani sport wear d'inshi bakake ya d'aura karamin farin towel a bayan wuyanshi, ya duka ya saka wata adidas black and white canvas d'inshi kan ya mike ya fito be nufi gym room d'inshi dake kasa ba kawai se ya fice seda ya hau kan titin unguwan kan ya fara jogging a hankali kaman baya so.

Ta 'bangarenta kuwa Bayan ta idar da sallah tayi azkar d'inta ta mike direct ta nufi kitchen tunanin me zata girka kawai ta hau yi ita ba wani girkin zamani ta iya sossai ba zata iya kirga waenda ta iya su ma albarkacin waya, karshe de doya ta fere tayi musu shi da egg sauce ta had'a musu tea me cike da kayan kamshi ta juye a flask bata kai ba seda ta fito ta share parlorn duk girman shi tayi mopping ta samu karamin towel ta goge kan dining da wuraren electronics d'insu, kan ta koma ta d'auko abincin ta shiryasu kan dining.

'Dakinshi ta nufa ta gyare tas daga ciki har parlorn ta share tayi mopping duk ta gaji a haka dae ta kunna burner ta sa turarukan wuta daga parlorn har d'akinshi, Allah ya taimaketa nata d'akin ba dattin da yayi hakan ya sa bata share ba Don ta gaji wanka kawai ta fad'a tana fitowa ta shirya cikin wata atampha orange color me ratsin baki da fari d'inkin bubu mai aljihu kad'an ya kamata daga kirjinta amma duk sauran a sake yake atamphar ta amsheta ba kad'an ba powder ta shafa da lip balm, d'ankwalin ta d'auko da niyyan d'aurawa d'aga idon da zatayi se suka had'a ido da mutum.

Da farko razana tayi, da ta tabbatar shine se ta sauke ajiyar zuciya tana dafe kirji dariya yayi kad'an bottle water dake hannunshi ya karasa shanyewa tare da jefar da bottle d'in cikin dustbin dake gefen bayin, wurinta ya nufa yana murmushin shi me kashe zuciyar 'yan mata yace "matsoraciya" shagwa'be fuska tayi tace "to banji shigowarka ba fa Ai dole In tsorata" murmushi ya kuma yi yana tsayawa dab bayanta ta cikin madubin ya zura mata ido yana kallo itama shi take kallo da mamakin yadda akayi yayi zufa haka bayan sanyi akeyi seda ta kalli kayan jikinshi da kyau tunanin watakila gym ya fito ya fad'o mata.

Ajiye d'an kwalin tayi tana mikewa ta juyo suka had'a ido kawar da nata tayi kan ta zame kasa tace "mun tashi lafiya?" Yace "lafiya kalau Alhamdulillah hayatee, ya gajiyan aiki? Naga kin shaa Aiki dayawa haka sannu, Allah yayi miki albarka" murmushi ta sake tana jin daad'i har kasan ranta mikewa tayi ta kar'bi towel d'in hannunshi ta matsoshi sossai ta sanya ta fara goge mishi zufan fuskanshi tana cewa "Ameen hamma, Ai aikin ba wani me yawa bane abinda ya kasance dole ne ga kowacce matar gida" har lokacin murmushi ne kwance saman fuskanshi yace "hmmm banda kazamai da malalata" dariya tayi dukda ita har ga Allah bata san da wadda yake ba shi kuwa da Hamna yake nufi kuma ya fad'i hakan ne sbd ganinta da yayi bayansu ta jikin madubi tana tsaye parlorn tana watso musu mugun kallo, dayake labulen da ya raba d'aki da parlorn a d'age yake.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now