BABI NA SHIDDA

2K 158 1
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
                  •Gureenjo6763 on wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*Alhamdulillah🙏🙏 thnks for your prayers*

                          *06*

Bappa Mu'azu da kanshi ya kirani a waya yace in same shi a gidanshi dayake babban d'an kasuwane kuma ba laifi ya tara kud'i don duk cikin su baba ya fi kowa kud'i, bayan naje mun gaisa da matanshi sama sama don duk basu yarda nayi hulda da su bare yaransu da suke 'yan uwana wai zan 'bata su, har parlornshi ya kirani mu biyu kad'ai.

Nasiha sossai yayi min wadda na yarda na kuma tabbatar shine kad'ai me tausayina cikin 'yan uwan baban, daga karshe ya ce "me kike so a duniyan nan mamana?" Wani irin farin ciki marar misaltuwa ne ya rufeni na manta da duk wani 'bacin rai da damuwana inda ba 'bata lokaci nace "makaranta bappa" kai ya gyad'a cikin tabbatarwa yace.

"Na miki alkawari zakiyi karatu yadda kike so in sha Allahu kiyi ta adu'a sannan ki maida hankali banda abinda ba shine ba, zan san yadda zanyi convincing inna, don ta Amadu ba matsala bane" godiya sossai na mishi inda ya ban kudad'e ya kuma fad'amin yaranshi 'yan mata biyu zasuyi jamb so ze biya mana tare tunda Ina da neco da waec d'ina.

Cikin jin daad'i na dawo gida duk wadda ya kalleni a lokacin ze tabbatar da cewa Ina cikin farin ciki marar misaltuwa, mama kad'ai na ba labarin ta ji daad'i sossai kuma she was glad zan cika burina, maganan da naken nan a lokacin anyi auren duk 'yan uwana biyu mata, a lokacin da maganan yazo kunnen baba kin yarda yayi sossai suka kai ruwa rana da yayan nashi har seda inna ta sa baki kan ya amince nayi jamb.

Inda naci sossai ba 'bata lokaci ya nema min Admission a nan BUK na kuwa samu course d'in da nake so wato Bsc.Ed biology, bappa mu'azu shi ya bani kud'in yin komai har sabbin kayan sawa irin de na fita reni, haka duk sati yake turomin dubu biyar don baba ya rantse biyar nashi baze shiga cikin karatuna ba......

Hmmmm wannan shine labarina "SAUDA AHMAD" (NOOR IMAN)

*********

"Duk inda kike ki tabbatar kin dawo gida before fad'uwar ranar gobe" kitt ya kashe wayanshi tare da jefarwa kan kujera, ya gaji wallahi da hali irin na hamna amma ya ze yi tana da goyon bayan su ummu, komai tayi shine me laifi.

Ta 'bangarenta kuwa tsaki tayi tana kallon best friend d'inta Jawahir tace "wallahi mutumin nan ya takurawa rayuwata, haba!! Mutum ya tashi a turai yayi rayuwa a turai amma se ya d'inga yin wani abu irin na dakikan kauyawan Nigerians, if not because Ina son Abdul wallahi da na rabu dashi."

Jawahir tayi murmushi tana sipping cocktail d'inta tace "hmm Ai duk laifinki ne hamna ace mutum yayi ta baki shawara bakya d'auka!! Da nine da Allah se Abdul ya rena kansa, mutum se d'an banzan gadara da fi'ili?" Dariya hamna tayi kaman ba mijinta aka zaga ba tana  danna wayanta tace "hmm ban san me yasa jinin ku be zo d'aya da boo ba, bari kiga Inyi booking flight na san na kai mutumin karshe tunda har yayi magana In ban koma ba ma matsala ne".

Hararanta jawahir tayi "ke kam haka zaki kare wallahi, aikin banza In nice bazan koman ba inga abinda ze faru" waro ido hamna tayi tana girgiza kai "uhm uhm jawahir duk iskanci na wallahi Ina tsoron Malabo baki san halinshi bane shiyasa, kuma baza ki gane ba" mikewa jawahir tayi tayi gaba tana cewa "Allah ya hanani sani mtseww".

Booking flight hamna tayi kan ta bi bayan kawarta tana murmushi itama ko ba komai tayi missing d'in jikinshi sossai sati kusan uku rabonta da nigeria.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now