BABI NA GOMA SHA BIYU

1.8K 144 2
                                    


                   🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
                 •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                         *012*

A razane ta d'aga tana kallon mahaifin nata a lokaci d'aya jikinta ya d'auki rawa, me baba ke nufi ne da rayuwarta? Wai se Baba Yaga tarwatsewar zuciyarta kan hankali shi ze kwanta ne? Me yasa ita ta fito duniya a haka ne? Hasbunallahu wani'imal wakeel ta dinga nanatawa a zuciyarta har ta d'an ji sauki, tsawarshi taji a kanta "ke wai ba da ke nake magana bane kin min zuru kina kallona da ido kaman na mayu, Toh kiji da kyau na baki sati biyu ki fitar da mijin aure In ba haka ba wallahi masallaci zan kai hotonki duk wadda yace kin mishi ko wanene kuwa aura mishi zanyi kinji nace wallahi".

Kukan ma yau ta kasa tsabar kad'uwa da maganan baban, me ta tare mishi ne ita a duniyar nan? Ita Ina zata samu miji cikin sati biyu, da jiri da komai ta karasa d'akin mama ta zube akan gado se lokacin kuka ya zo mata sossai ta fashe dashi kaman ba gobe kirjinta na mata wani irin zafi, da ma zata mutu da ta huta.

Shirin fita lectures tayi amma bazata iya fita a haka ba, don ta san ko taje ba abinda zata fahimta, tuna maganan me acha'ban da ya ta'ba kawota gida tayi, tabbas tana mantawa da kai kukanta wurin me duka, iyakarta sallaloli biyar nan da suka zama wajibi a kanta ko alqur'ani se ta manta yaushe ta bud'e shi bare kuma ayi maganar nafilfili da kai kuka wurin Allah.

Mikewa tayi ta fad'a toilet tayi alwala dama da hijabinta kanta, Alqurani ta Zara tare da zama kan dadduma ta bud'e ta fara karantawa cikin natsuwa, tafi awa zaune tana karatun dukda taji shigowar mama kuma ta san ita take jira suyi magana, amma ta kasa tsayar da kanta har maman ta fice, kiran da ya fara shigowa wayarta ba kakkautawa ne yasata tsayar da karatun ta duba wayan.

"Hammad" shine sunan da ya bayyana a saman fuskar, murmushi tayi don sossai karatun ya sauke mata duk wani nauyi na zuciyarta, ya gusar mata da damuwarta, ya bata wani kwarin guiwar da da bata dashi, ya goge duk wani hawaye dake fuskanta haka ya hana wasu zubowa tabbas alqur'ani rahama ne ga masu karantashi, kwanciyar hankali ne ga duk wani tashin hankalin bawa.

Ta yarda kuma ta tabbatar yau, da wani irin kwarin guiwa ta d'aga wayan kan yayi magana ma tace "ya hammad Ina kwana? Ya gd? Dan Allah da gaske kana so na tsakani da Allah?" Shiru yayi na mintuna kan yace "lafiya kalau iman, kwarai na soki tsakani da Allah kuma har yanzu Ina sonki sede...." kan ya karasa ta katse shi "Toh baba yace in gabatar mishi da wadda nake so nan da sati biyu, happy?" Cikin rawar murya yace "kenan ni kike so?" Dariya tayi kan tayi maza ta kashe wayan cikin yanayin jin kunya.

*******

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun!" Ya dinga nanatawa tun da ta kashe wayan, kwata kwata daren jiya kasa bacci yayi yana tunanin ta yadda ze iya rabuwa da noor iman ba tare da tayi tunanin yaudararta yayi ba, be kuma son fad'a mata mahaifiyarshice ta sashi rabuwa da ita don kar ta tsani mahaifiyar tashi, da kyar ya samu ya harhad'a 'yan kalaman da yake son gayamata, amma ta fad'a mishi abunda baze iya tunkararta maganan rabuwarsu ba.

Mikewa yayi ya fad'a wanka sharp sharp ya shirya tare da d'aukan key d'in motanshi ya fice, kana ganinshi zaka san yana cikin damuwa ko be furta maka ba, direct gidan Uwais yayiwa tsinke ba tare da ya shiga ciki ba ya kirashi a waya "dan Allah in kana gida ka fito akwai maganan da nake so muyi" daga d'ayan 'bangaren Uwais yace mishi yana office ya sameshi chan.

Asibitin da Uwais ke aiki ya nufa minti minti yana dukan sitiyarin motar tare da taune lips, har Allah ya kaishi office d'in lafiya, zama yayi ya zubawa Uwais ido yana kallo har Uwais d'in ya sallami patient da yake dubawa yace "Lafiya kuwa abokina?"
Sighing yayi kan ya fara bawa Uwais labarin duk abinda ke faruwa.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now