BABI NA GOMA SHA SHIDDA

1.8K 175 4
                                    


                   🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
       •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

   
                             *016*

Dawowan mama ta samu tana bacci so bata d'auka wani abin ya faru ba, se kawai tayi zaman ta kan kujera, har magrib noor iman ta kai tana bacci don har zarah ta kawo musu abinci ta duba jikin nata duk tana bacci, se da aka idar da sallar magrib tukun ta farka a hankali ta mike zaune mama tazo taimakonta Tace "kar ki damu zan iya mama, na gode" ta fad'a har yanzu with bitterness in her tongue, bayi ta shiga tayi abinda zatayi kan tayi alwala ta fito a zaune ta rama sallar la'asar da magrib da ya d'an wuce bata wani jima da idarwa ba aka kira isha ta gabatar kan ta ci gaba da zama.

Mama ce Tace "zarah ta zo kina bacci ta kawo abinci yarinyar 'yar albarka ce tana sonki sossai shiyasa take d'awainiya damu haka, In zubo miki?" 'Dan murmushin yake tayi kan ta gyad'a kai tabbas zarah na sonta zata iya cewa bata ta'ba yin kawa dake sonta irin zarah ba, tsakaninta da Allah take sonta, pepper soup da irish pottage da yaji veggies da mama ta ajiye mata ne ya dawo da ita daga tunanin da ta fad'a, a hankali ta sa spoon ta fara ci kaman me taunan magani.

Tana mamakin me ya hana hammad zuwa yau? Ta duba wayanta kuma ko missed call d'inshi bata gani ba, da wannan tunanin ta gama cin abincin duk da daad'inshi don daga kamshin zaka san yayi daad'i amma bata wani ci sossai ba sbd bakinta d'aci yake mata.

Ta mike kenan don komawa gado tana d'an hira da mama sukaji an bud'e kofa da sallama duk juyawa sukayi suna kallon kofan hammad ne ya shigo, murmushi ta saki ganinshi taji d'an sauki a zuciyarta dukawa yayi ya gaida mama cike da ladabi kan ya d'ago yana mata ya jiki, ta amsa da "da sauki Alhamdulillah" mikewa mama Tayi ta fice.

A tare sukayi parking da hammad kuma a tare suka nufi bangaren amenity ganin ya nufi kofan d'akinta ne ya sashi fara tunanin waye kuma wannan, windown de ya kuma zagayawa ya tsaya yana kallonsu.

Be san ya saki murmushi ba ganin genuine murmushi a fuskanta tunda ta kwanta a asibitin ze iya cewa be ta'ba ganin tayi irin murmushin nan ba se yanzu, ganin mama ta fice daga d'akin yasashi gyara tsayuwa ya kasa kunne don jin me zasu ce, don ma Allah yayishi da kaifin ji.

"Saudat" da sauri ta d'ago ta kalleshi be ta'ba kiranta da sunanta haka ba sbd alkunyar sunan mahaifiyarshi hakan yasa gabanta fad'uwa kallonshi kawai tayi ba tare da ta amsa ba yace "saudat na so ki tsankani da Allah, Ina sonki a yanzu haka kuma na tabbatar har abada bazan dena sonki da kukan rashin mata ta gari ba, na tabbatar abinda zan fad'a will shattered your heart amma ba yadda na iya umarni ne daga wacce bazan ta'ba iya tsallake magananta ba kiyi hakuri, ki rungumi kaddararki Allah ya za'ba miki wadda ya fini".

Kasa kallonta yayi jiki a sanyaye ya fice ko waiwaye babu, wuri guda ta kafawa ido ko motsi ta kasa yi tsabar kad'uwar da take ciki har bata san mama ta shigo ba seda ta ta'ba ta.

Firgigit tayi tana kallonta "Lafiya kuwa iman?" Cikin rawar murya tace "Lafiya klau" Da sauri ta kwanta ta juyawa mama baya, gyara blanket mama tayi akan sallaya tayi kwanciyarta don Allah yayi ta da baccin wuri.

Murmushin takaici ya saki in disbelief yana juya idanu kaman mace, in ya fahimta daidai saurayinta ne yayi breaking up da ita while she's in sick bed with high Bp and heart attack, a fili ya ce "ya subhanallah" ya karasa da shafa kanshi yana lasan lips d'inshi da yaji sun bushe, baze iya kwatanta how broken she is in there ba, yana nan tsaye yana ta aikin kallon bayanta Pakistan ne a jikinta riga da wando pink se gyalenshi da ta d'aura akanta.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now