BABI NA BIYAR

2.2K 174 9
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          •Gureenjoh6763 on Wattpad•

*'yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                            *05*

Tsaye yake hannu a kwankwaso yana karewa room d'in kallo cikin takaici da  bakin ciki, tied vest ce baka sanye a jikinshi da black three quarter me zips dayawa a jiki, wadda hakan ya bayyana murd'ewar jikinshi da de gani ma'abocin gym ne damar bayyana.

Jikinshi gargasa ne bakake sidik a kwance gwanin sha'awa, hannunshi dake waist d'inshi d'aya ya d'aga ya shafa kwancaccen gashin kanshi da ya ji gyara tare da jan tsaki a lokaci d'aya, ya zaiyi ne wai wani irin mata Allah ya bashi? Me ta nema ta rasa da bazata iya natsuwa ta nemi lahirar ta ba se aukin yawace yawace da sunan business.

Tsaleliyar wayarshi ya zara ya danna kira, cikin yanga da wani irin iyayi da zaka iya rantsewa ko mace bazata iya irin yanganshi ba, yace "Ki zo Lil, am in my home" be jira amsanta ba ya sauke wayan tare da kwad'ata kan gadon kaman itace ta 'bata mishi rai, zarya ya ci gaba da yi cikin tafiyanshi da izza da jin kai, Allah ya gani be san ya ze yi da Hamna ba duk yadda ya d'auki lamarinta a da ya wuce nan.

Duk wani nasiha da wa'azi da yake 'bata nyaun bakinshi yake mata a banza shiga ta nan yake yi ya fita ta chan, ummu ma da yake iya gayamata matsalarshi ya fad'a mata amma wai yarantace zata dena, Ina yaranta a jikin me shekaru 25 ko Lil d'inshi dake 18 and half wallahi tafi hamna iya duk wani aiki na 'ya mace a gidan aurenta.

Hakurinshi ya kai makura akan hamna wallahi mafita kawai yake nema ko ta wacce hanya, bud'e kofan part d'inshi da akayine ya dawo dashi cikin tunaninshi, kurawa kofan brown oily eyes d'inshi yayi kaman me nazartar wani abu, se kuwa gata ta shigo to my biggest surprise Zarah ce tana kallonshi tace "Ya Abdul gani" tsaki yaja kan ya harareta yace "Ai ban da ido, gyaramin part d'in nan".

Tura baki gaba tayi zata fara diddira kafafu ya watsa mata harara da idanunshin nan nasa masu firgita 'yan mata da gigitasu da fidda su cikin natsuwarsu kai har wasu mazan ma, da sauri ta zare gyalen jikinta ta nufi corridor d'in site d'in don dubo kayan da zatayi anfani dasu a zuciyarta se mita takeyi.

Mutum da matanshi amma itace baiwa komai yake so lil kaza Lil kaza bata isa yin musu ba yaci ubanta In na muguntan na kusa dukda shi ba mutum bane me saurin kai hannu amma yana da zafi fiye da tunanin me tunani, ga riko amma In ka sanshi kuma yana da sanyi da tausayi fiye da zato haka kuma yana son 'yan uwanshi son da baya had'ashi da kowa, musamman ummu.

Ya tsani karya da munafunci haka baya da shishigi akan harkar da ba'a sanyashi ciki ba kai ko da kuwa na cikin gidansu ne. Dr. Abdulraheem Ahmad malabo kenan AKA Dr. Malabo sunan da friends d'inshi da students ke kiranshi.

A natse tayi komai har ta gama a gajiye sossai sbd ko gida bata karasa ba daga makaranta ya kirata yace tazo haka tasa driver pasa shiga layinsu yayi kwana ya shige layin gidan yayan nata dake duk cikin unguwa d'aya wato Nasarawa GRA, kwance ta ganshi akan duguwar kujera kafafunshi na lilo sabida tsawonshi da ya zarta kujerar idanunshi a lumshe hannunshi kwance kan flat tummy d'inshi.

Ita har ga Allah tausayi yake bata ace mutum da aurenka da komai amma kai baka san daad'in mata ba? Ajiyar zuciya ta sauke tace "hamma mi timmini, d'ume bo a yid'i?"(Hamma na gama me kuma kake so?) bud'e idanunshi yayi ya kura mata na mintuna kan yace cikin slang fulatancin shi "wala, dillo tan mi andi a somi, yah sewtu"(nothing, tafi kawai na san kin gaji, je ki huta).

Kai ta gyad'a kan ta fice ta shige mota driver yaja ya fice da ita zuwa gida, a gajiye ta shiga ciki a parlorn kasa taga hamma Hafeez da ummu zaune suna hira, zubewa tayi a jikin ummu tana cewa "wayyo ummu am na gaji" kyakyawar bafulatanan mace da tajiku da kud'i, don jikinta kawai ka kalla zaka tabbatar da haka photocopy d'in Abdulraheem don ba abunda ya bar mata kyakyawace ta ajin karshe dukda she's at her early 50's.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now