*****

"Wato baka ji fad'an dad d'inka ba ko?" Shagwa'be fuska hammad yayi kan yace "plzzz mom na san zaki iya ki rokar min shi don Allah ya kara min time" ta'be baki tayi kan tace "na fa riga na gama magana dad d'inku ya gama hakurin da ze yi da kai, ko na je korata ze yi" ajiyar zuciya ya sauke kan ya ci gaba da cin abinci jiki asanyaye, dole ya nemi mata cikin watannin nan.

Don Allah ya gani ba ze iya bari dad ya za'bar mishi wata kuchaka ba, da irin tunanin nan ya gama cin abinci ya mike ya fita, mota kawai yaja ya fara zaga gari yana neman mata, abin ma dariya yake bashi wallahi, duk wacce ya gani se ya kare mata kallo amma ba wacce keda quality d'in da yake so 100% ya zagaya har ya gaji ya dawo gida ran nan a chunkushe, part d'inshi kawai ya shige yayi kwance kan gado yana tunanin mafita.

*******

"Iman zo In aikeki gidan inna" cewar mama dake zaune a parlor tana kirgen kud'in da aka kawo mata yanzu na bashi, fitowa nayi ina tura baki nace "dan Allah de mama, nide ban son zuwa gidan Allah sbd kin san halinta Sarai a gareni" hararata mama tayi kan tace "Toh bari na yafa mayafi na je da kaina" daga jin yadda tayi maganan zaka san gatse ne, hakan yasa na koma d'aki na sanyo khimar kan doguwar rigana na material hannuna rike da takalami na fito na kar'bi sakon.

Tare da kud'in napep na fice, umma dake zaune kofanta tana gyaran farce na kalla nace "umma naje gidan inna" dukda na san ba amsani zatayi ba amma hakan ya zama kaman al'ada bana iya fita ban mata sallama ba ko da kuwa baza ta amsa ba, da kafa na taka zuwa bakin hanya, bana kallon kowa balle takaici ya kamani na zund'e ko ko kana nan magan ganun mutane.

Me makon na tari napep kaman yadda na kar'bi kud'in kawai se na tsinci kaina da hawa machine muka nufi court road, daidai wuraren BUK holdup ya rike mutane ga me machine d'in nawa se kutsa kai cikin ababen hawa yake duk ban lura ba sbd tunani na ya tafi gabad'aya wurin irin wulakancin da inna zata min a gidanta.

Kiiiii naji taka birkin d'an acha'ban a hankali nace "kayi a hankali malam Dan Allah" ba tare da yace komai ba ya taka birki ya tsaya, kaman ance In waiga se ko idona ya fad'a cikin nashi da sauri na kawar da kaina ina jin gabana na fad'uwa, hakan be hanani tuno wulakancin da ya min ba, ban san yadda akayi na tura baki gaba Ina kunkuni da ni kaina ban san me nake cewa ba.

Ta 'bangarenshi kuma kallo biyu ya mata ya kau da kai, Sarai ya ganeta itace ta shigo mishi class sau biyu bayan ya shiga, yadda ta tura baki tana kunkuni ya bashi dariya sbd ya san haushinshi take ji, hakan ya sashi sakin murmushi, "hasbunallahu wani'imal wakeel" ya furta akan la'bbanshi ganin yadda me acha'ban da take kai ya figi machine d'in kaman zasu kife sbd bada hannun da akayi.

Sake had'a idanu sukayi Ai ko ya sakar mata harara kan ya kau da kanshi shi har ga Allah haushin masu acha'ban nan yake ji da masu hawa Haka kawai suyi ta risking life d'inka a banza yanzu dan Allah duba amma ita ko a jikinta yayi tsaki yafi abinda yafi kan ya karasa cikin BUK ran nan a 'bace, wadda ya rasa dalili.

Ta'be baki tayi a zuciyarta tace ko me na mishi da ze wani harareni? Mtsewww, ba 'bata lokaci suka  karasa layin gidan inna ta sauka ta sallami me machine d'in ta shige gidan cikin fad'uwar gaba, daga bakin get take jin hawaniyar yara hakan ya tabbatar mata da akwai gwagwaninta da suke nan aiko tana karasa kutsa kai ta hangi goggo hindatu da kamila zaune cikin runfa suna lissafin kud'i, daga chan gefe inna da goggo saratu tsaye suna magana yaransu na nan tsakar gidan suna ta wasa.

Da fargaba ta karasa gaban su inna ta duka har kasa tace "sannu inna barka da rana" tun kan inna ta amsa goggo saratu ta kar'be zancen da cewa "au yau su jawaran ne a gidan innanmu?" Magananta ya dawo da hankalin su goggo hindatu kaina carab goggo kamila tace "jawara ko ashawo, saratu kin san duk abinda yarinyar nan ke aikatawa a bayero kuwa? Hmmm yawo ma batayi se da yaran masu dashi".

Goggo hindatu tace "Kai kamila wa ya fad'amiki?" Goggo kamila tace "kin san Ai abin duniya bata 'buya akwai wata makwabciyata da 'yar ta ke chan ita na sa ta dinga kularmin da wannan Shegiyar wai don zumuncin dake tsakani, in kinji abinda yarinyar take gayamin zaki sha mamaki aji ma bata shiga se malami ya shiga tayi ta karairaya don ya gani ya kyasa a sashi a layi".

Hawaye ne ya cika min ido tab ga zuciyata dake min zafi kaman ze bar kirjina, in naji irin waennan maganganun a bakin bare ba kasafai ya cika damuna ba kaman yadda nake jin zafin In naji a bakin 'yan uwana na jini, bud'an bakin inna se cewa tayi "mtseww d'an Allah ku dena damun kanku a kan yarinyar nan, Allah ya gani kunyi iya kokarinku, Allah na gode maka da ka amshi ran maigida be yi tsawon ran ganin wannan abun takaicin a zuriyarshi ba, ni na jima da sallamawa duniya ke saude bakya cikin jikokina wallahi don bazan iya ba.

Haba!! Matsalan yau daman ta gobe daban kullum ke de ke d'in de ce gur'batacciya a cikin zuriyarmu Anya ba chanzawa Aishatu ke akayi a asibiti ba?" Zuwa yanzu kuka Noor iman ke yi bilhakki da hawaye bibbiyu cikin rawan murya tace "inna ba laifina bane, da bawa na da daman za'barwa kanshi yanayin rayuwarshi da Wallahi ban za'bi irin wannan rayuwan ba, aka ce muku nima banda rai ne? Ko kuwa baku san kaddara ba..." buge min baki da goggo saratu tayi yasa ni yin shiru tare da ci gaba da kuka na yayinda inna ta saki salati.

"Eeeeh Lallai yarinyar nan yanzu na yarda da abinda ake cewa d'ari bisa d'ari, zagina kikayi? Nice ban san musulunci ba da har zaki gayamin kaddara, tashi ki bar min gida shegiya gayyar tsiya kika sake tako kafanki gidana se na ci mutuncinki, kuma zan kira ubban naki inji In shi ya d'aure miki gindin yin iskanci" ajiye mata sakon da mama ta bani nayi tare da ficewa Ina hawaye sossai.

Tafiya kawai na dinga yi ba tare da na san inda nake jefa kafana ba har na fita daga layin na ci gaba da takawa ba tare da na nemi abin hawa ba, tafiya yake yana duba abu a sit d'in baya, abu ya manta a office d'inshi har hakan yasashi shiga makarantan ranar lahadi, yanzu ma gidan Sauban ya nufa don bashi wasu takardu shine yake dubawa be hankara ba sitiyarin ya kubce mishi saura kad'an ya bugeta yayi saurin taka birki yana kallonta.

Amma ita bata san anyi ba hankalinta kwata kwata baya jikinta mamaki sossai ya kamashi ita kuwa lafiyanta? Randa ya fara ganinta kuka take yi tana tafiya akan hanya wadda har yayi sanadiyar da yasa ya bugeta, haushin da ta bashi ne ya hanashi fita ya bata hakuri sbd Shi a ganinshi me ze kawo mutum me hankali kan titi gatsal tana tafiya tana hawaye kaman wacce aka sako daga psychiatric.

Toh ga yau ma dukda be kai ga bugeta ba, amma me ya sata kuka bayan yanzu ya ganta lafiyanta kalau? Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa kanshi "Ina ruwana?" A hankali ya ci gaba da tafiya yana kallonta ganin ta nufi babban titi yasa yayi saurin parking ya fita da sauri yaje ya sha gabanta wadda hakan ya sata tsayuwa "hey!! are yhu alright?" kallonshi tayi se kuma ta kalli inda take da sauri ta goge fuskanta tare da kakalo murmushi ta gyad'a kai, ta'be baki yayi kan ya juya ya tari napep.

Empty one, ba tare da ya kalleta ba yace "get in" shiga tayi ya zare dubu sabuwa gal ya mikawa me napep d'in kar'ba yayi, ba tare da ya kara magana ba ya koma motarshi ya ja yayi gaba.

                    🖤Gureenjo🖤

NOOR IMANWhere stories live. Discover now