Chapter 57

227 20 12
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 57.

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

MANEER's POV.
Mommah! Mommmahhhhhh!! Mommmmmmahhhhhhhhh!!!!! Shine kiran tashin hankalin da Maneer ya dinga yiwa Mommah, wanda duk wanda yake gidan seda ya zabura saboda tsananin firgici, Mommah dake kan sallayar ta da sauri ta fito domin tasan wannan ba kiran lafiya bane.

"Lafiya kake Maneer? Me ya faru"
Bayan ta fito ta taradda shi yanata haki, yana nuna mata waje,
"Addaaahhh, Addahhhhhh cee...." Meenah da ke can kwance tanajin duk abunda ke faruwa da sauri ta cire drip in da ke hanun ta jin an ambaci sunan Addahn ta.

Abrar kuwa wani killer smile ta saki tare da k'ara juya kwanciyar ta, dama rashin jin hakan ne ya hanata yin bacci.

Meenah kam ganin Maneer ya k'i magana se kawai wajen da yake nuna musu da sauri tabi hanyar waje, hakama Mommah ta mara mata baya.

Cikin y'an mutanen da suka fara taruwa Meenah ta dosa bil hakk'i, ganin Poppah duk'e a gun da sauri Meenah ta k'arasa ta ganewa idon ta abunda bazasu iya jure kallah ba, ta ganewa idon ta abunda k'wak'walwarta bazata iya jure wa ba.

"Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un, Addah? Addah tashi gani nazo, dama ai na gayamusu zaki dawo, ki daina wannan wasar ki tashi.

Haka ta dinga jijjigarta gwanin tausayi, da alama bata ma cikin hayyacin ta.

K'arasowa Mommah kenan tayi mummunan katari,
" wannan y'a tace, meya sameki y'ata? Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un dan girman Allah ki tashi"

haka Mommah ta dinga jijjigar gawar da k'arfin Allah wanda sai da aka kira matan mak'wabta suka b'anb'are ta akai tare da shiga dasu gida tare da Meenah.

Nasiha akan juriya mutan gurin suka dinga yiwa Poppah akan ya daure ya jure, to idan yana nuna rashin juriyar shi inaga iyalan shi?

Tun yanzu yaga yanda suka rud'e to ai ya kamata yayi fighting da nashi yazo ya lallashe iyalan shi.

Haka dai har ambulance tazo aka saka gawar aka wuce.

A can cikin gida kuwa ko wanen su shiru yayi yayi zugum, saboda gani suke kamar wani bak'in mafarki ne suke.

Haka ma Gwammah da Grandpa duka sun tashi cikin mugun yanayi na jin wannan, hakama tuni Uncle Omar ya marawa ambulance baya tare da Poppah.

Meenah kuwa, tuno wata nagana da y'ar uwar tata tayi mata wanta take cewa;

" Meenah nikam inason Allah ya gwadamin kin sami miji saboda inason ayi mana aure tare mu haihu tare kamar yanda muka tashi kai d'aya kamar 2wince. Kai zan so na ga wanda zai d'aukar wa kanshi wannan rigima ta auren ki rigimammiya"

a daidai nan Meenah ta jefa mata pillow hakama ita ma Miemie ta cillo mata, aikuwa suka fara wasar jefa pillows.

Haka ma ta k'ara tuna maganar su ta k'arshe wacce take cewa;

"Wai ni za'a kawo wa lefe a yau? Wallahi se nakejin gabana yana tsanan ta fad'uwa,dan Allah Meenah ki zo muje kada y'an kawo lefen su fara zuwa su taraddani a nan"

haka margayiya Miemie ta dinga magiya akan su zaune tare da Meenah amma Meenah tak'i, ashe zaman su ya riga da ya k'are 😭😭a she komai ya kusan zuwa k'arshe, haka muryar ta ta dinga yimata echo.. rufe kunnuwan ta tayi tana batun zauce wa maganar da Mommah tayi ne ya dawo da ita a hayyacin ta.

A daidai nan Ambulance ta dawo da gawar tare da jami'an tsaro.

"Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un, y'ata wayyo na shiga ukku na ashe ba mafarki nake ba, wallahi na d'auka mafarki nake,"

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now