Chapter 30

286 26 5
                                    

🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
         By
   💐Teemahcutey💐

Page 30.

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

************
"Inalillahii" shine abinda yake ta nana tawa lokacin da ya shiga d'akin.

Shiga yayi da sauri domin kada ta illata kanta.
Ko da ya 'ida k'arasawa gabaki d'aya an hautsina room in, gashi duka fuskar ta jini da hanun ta, hakama duka gashin ta ya barbaje kamar wata mahaukaciya.
Ganin ya shigo d'akin yasa ta rugo aguje ta chakumeshi tana kuka.
"Haba Haba baby, yanzu da sun kasheni fah? Kaga duka sun haukata mun gashi kuma sun shafamin jini ajiki"

Ajiyan heart yayi saboda shi ya d'auka jima kanta ciyo tayi.

"Ashe ma aljanu keda d'akinnan naka? Hmm ni wlh ban tsoron su kawai dan naga sunada jinine a jikin su kuma suna rik'e da wuk'a" dagannan kuma se ta fashe da kuka tana batun fad'uwa.
Taro ta yayi tare da d'orata kan jikin shi.
Daria Meenah tayi tare da fad'ar muje Ammie na jiran mu.

Shikam Captain ya fara tsorata da wanga lamari na Meenah, daga d'ayan 6angaren kuma tausayin ta yake.

Janta yayi izuwa toilet nashi ya wanke mata jinin da ke kan fuskarta da hanunta, though be kai ga tab'in kayan jikin ta ba, janta yayi suka dawo d'akin shi. rebborm inta ya d'auka ya zaunar da ita akan stool ya saka mata rebborm in da k'yar....
kallan ta yake a mirror ya lankwashe kai kamar small boi
" gaskia baby wannan gashin ya yimiki yawa dole a rageshi" ya k'arashe maganar kamar yana magana da small girl. Dan shi kallan yarinya yake mata.

"Lalalaaaaa Allah a'a nikam ya baby, haramun, kuma nikam inasan abina. sedaii maby na fara retouching koda ze rage wannan yawan"

Dariya yayi tare da fad'ar muje ya mik'a mata hanun, nuk'e kafad'ar ta tayi alamar bazata bashi hanun ba, daria yayi tare da shiga gaba tana binshi a baya.
Ganin yana gaban ta sossai yasa ta ruga aguje ta shiga gaban shi.
Captain kam ya d'auka wani abunne kuma kawai se yayi murmushi ya girgiza kai.

A b'angaren Ammie kuwa gajia tayi da jiran su kawai ta ci abincin ta ta koma sama.

Ko da suka ida k'araso wa basuga Ammie ba wannan ya basu tabbacin cewa ta gaji da jiransu ta ci nata ta wuce.

Zama yayi akan dining.
Serving inshi tayi , yaci abincin sosai se santi yake zubawa, daga k'arshe ma kachokam ya d'auke jug in fruit salad in yakai a sight inshi wai kada a shanye, acewarshi yayi dad'i ainun.

***********
"Next week ya kamata ayi changing over cox dama sunyi requesting akan holiday, so kawai ba'a basu bane saboda dawo warka, amma yanzun tunda ka dawo zasu iya canga wa" shiru Dad in Captain yayi alamar yana sauraren abunda ake fad'a daga d'ayan 6angaren.
"To shikenan Dad insllh zan basu hutu. Sai ka dawo"

Ajiye wayan Dad yayi yana wani shu'umin murmushi.
Sake kiran wani d'aya daga cikin Amintattun shi, wato wanda a gidan shi na skt yake kula da CCTV cams na gidan, yayi digiri ya digirgire ta fanin computers.

Gaisawa sukayi daga bisani yace mishi;
" kada ka manta abunda na gaya maka, ka kawar da gabaki d'aya CCcams in gidan next week, kada suyi storing komai, bance a kashe su ba, amma kada su bada imformation in komai a wannan ranar"
Katse wayan yayi bayan ya kammala sauraron abunda aka fad'a daga d'aya bangaren.

(Dama a gidan alaji tijjani  ana rotation na aikin gidan duka, wani lokaci gabaki d'aya guard in Captain da sojoji ne ke tsaron gidan, kama da mai gadi har zuwa mai ban ruwa, at times kuma idan akayi rotation ana kawo wa'enda ba sojoji ba, normal mutane but masu ilimin komai da komai kama da mai gadi har i'zuwa mai ban ruwa) wannan kenan.

Two days latter.

A yaune Dad ya dawo daga Abuja.
Captain yaje dakko shi a Airport.
Maids in gidan da kuma kuku sunyi k'ok'arin gurin shirya mishi meals kala kala irin wa'enda yake buk'ata.

(Dama dik sadda Dad yake gari yanada professionals kuku in shi wa'enda sukayi digree ta fanin girke girke, kuma yawan cin su mazane wa'enda ke side nashi... gabaki d'aya ma'aikatan gidan y'an boko ne dik a inda kk aiki to kayi karatun wannan fanni.. so duk sadda Dad ze dawo ne wa'ennan mazajen kukun suke fara nasu aiki gadan-gadan ba kama hanun yaro)

Mutane ne burjik a zazzaune wasu tsaye wasu jirkice wasu karkace wasu kuma jingine, wasu mabuk'ata ne wasu kuma mabarata wasu maha'inta wasu kuma mabid'a da mahandama, kowa da tashi kalar damuwa.
Da ka kalle ko wanne daga cikin su to kasan yana tsumayen san ganin wani abu ko kuma motsin wani abu, kowa se zare ido yake dan san ganin ta hanyar da zasu 6ullo.
Fira suke irin na yanayin aiyukan yau da kullum.
Danno hancin motar yayi cikin unguwar tasu.
Aikuwa mutanen da ke gun gate in gidan a take suka tashi.
Mutane ne suka da baibaye motar tashi da k'yar ya samu suka shiga gate in gidan.
Mak'udan kudi Dad ya bada aka rarraba wa mutanen, dama haka mutane ke mishi sometimes idan sukaji ze zo... shikuma yana k'ok'ari gurin taimaka musu.

Direct part inshi ya wuce.

A b'angaren Ammie kuwa haka take ta fama da Meenah ala doli se tayi makeup ta sakata agaba. Da k'yar ta yadda ta amince ta shafa powder da janbaki.
" Yawwa ko kefa Ammie na? Kinyi kyau sosai"
"To nagode y'ar Ammie"
Murmushi Meenah tayi tare da k'ar6an wayar Ammie tayi d'akin ta.

Wani door naga Ammie ta nufa gefen makekiyar drower gadon ta, bod'e door in tayi se ga wani siririn corridor ya bayyana wanda aka k'awata shi da royal touch dec... gawani sanyin AC da k'amshin Air freshener dayake bugo hancin mutum. gurin ya had'u matuk'a musamman se wani blinking yake yi, tacigaba da tafia se ga wani tafkeken dining area ta bayyana agun.
Ananne dai na go cewa 6angaren Dad ne. Wato a d'akin nata akwai wata mahad'a da zata sadata da turakar mijin ta cikin sauk'i. (Nace hmmmm masu kud'i suna sha'aninsu)

Fad'in had'uwar sashen nashi 6ata lokaci ne, domin iya had'uwa kam ya had'u kamar fadar president.

Data ta bud'a ta shiga watsapp, pic inda sukayi da Ammie ta saka a status in Ammie, ta saka d'aya kan DP shikenan ta kashe datar ta fara game.

A b'angaren Captain kuwa zaune yake Gardiner shi yana d'an shak'atawa. Whatsapp ya shiga anan yayi tozali da kyawawan Pics in Meenah da Ammien shi.
" wow what a beautiful queens" shine abunda ya fad'a.
D'aukar wanda ya fi mishi kyau yayi ya saka a status nashi.... aiko before 20minuts sak'wanni se shigo mishi suke daga friends inshi.

they be like;

" wow ur sister is gorgeous"
"She's damn cute"
" buddy I love her"
" hey m coming for this little sis of urs"
"Call me inlaw from now in n"

Haka suke ta fad'a yawan cin frnds inshi
Shidai Captain ba wanda yayi wa reply..
Sosai suka dinga da munshi daga k'arashe ma kashe datan shi yayi tare da cillah ta gefe yana tsaki.
Ko me ya tuna oho?
Kawai tashi yayi ya nufi side in Ammie, direct d'akin Meenah ya wuce.
Ko daya shiga be taradda ita aciki ba, so zaga gidan ya shiga yi but ko ina be ganta ba, yanke hukuncin zuwa main Gardiner gidan yayi koda ze ganta acan d'in aiko cikin sa'a ya hangota tana kichiniyar d'ebo fruit.

Tsaki yaja ciki ciki yace;
"Ke go nd get ready in the next 30mnt we're going out" batare da ya jira amsar da zata bashi ba ya juya ya barta tsaye k'ememe.
Seda ta k'arasa abunda take kamun ta kwashe kayan ta ta koma cikin gida.
Wanka tayi, Bayan tayi wankan ta fito ta shirya cikin atamfa riga da skirt. D'aura d'an kwalin ta tayi ture kaga tsiya.
Gashinta data chupke abaya yayi wani kungu a bayan d'aurin nata gashinda ke gefen da Bayan wuyan ta duka ya kwanta kamar jaririya, dik wanda ya ganta zai d'auka attach ne tasa saboda yanda duniyar ta lalace ba'a gane masu gashin kwarai da wanda ba na kwarai ba.
Bata shafa komai a fuskar ta ba. wannan yasa ainihin kyawon ta na asuli ya k'ara bayyana.
Arabian Perfumes tasaka, kamun ta shiga d'akin Ammie ta fesa Oud masu matuk'ar k'amshin dad'i. Sosai tasaka turarrukkan domin Allah ya jarabeta da san turarruka musamman Arebian Ouds.
Ganin be futo yasa ta tashi domin zuwa side inshi. Domin batasan jiraaa musamman idan ta shirya.

(Nace ahhhh!! Su hajia Meenah manya🤣
Please Maryam jabour come carry ur husband se Meenah ta miki snatching 😜🤣)


❤️Teemahcutey❤️

Abun Alfahari Na✅Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ