Chapter 19

267 29 15
                                    



🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
By
💐Teemahcutey💐

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Page 19..

Tafiya yake yana sauri, Domin akwai meeting in gaggawa da aka hada musu ah nan VIENNAH AUSTRIA ah;
INTERNATIONAL COMMISSION FOR THE PROTECTION OF DANUBE RIVER ( ICPDR).
Akwai abunda suke suspecting ana shigowa dashi ta,DANUBE RIVER.

So bayan sun gama meeting inne aka umarcesu da cewa: "zasu fara operation na tackling SELVADOUR tare da mutanen shi on the next coming two days."

Direct bayan ya komah masau kinsa yagama kammala binciken sa ah Laptop, ya rufe ya tattara kayan shi ya koma EVENTHOTEL PYRAMIDE. Saboda tsaro da kuma yanayin aikin da hatsarin da ke cikinshi.

Around 8:32pm ya fito daga RESTAURANT STEIRERECK, bayan yagama cin abincin shi, direct masaukin shi ya koma ya chanja kayan shi izuwa, simpleTshirt ta kamfanin RALPH LAUREN, yasaka ash in colour tare da wando black, a PATEK PHILIPPE WATCH ya saka, a gaggauce ya dauki big boi's diamond studded shoes ya saka.
Sumar kan yi ya gyara kawai ya tajeta yasaka mata mayyukan da yasaba sakawa, atake yafara sheqi sumar ta kwanta luff luff.

Car keys in shi ya dauka tare da ficewa.

Though Captain idan yayi tafiya outside yana rental na motor saboda harkokin shi na yau da kullum.
On average, a rental car in Austria coasts $1414 per month, ($47 per day).

Per month captain yayi because besan lokacin koma warshi Nigeria ba.

Tafiya yake slowly acikin car inshi , Cox yariga da yakawo inda yakeso, parking motar yayi daga nesa.
******

Bayan wayewar gari suka nufi family house.

Fira suke gwanin sha'awa, bayan sun kammala cin abinci ne Poppah yace;

"bara na shiga dakin Gwammah,saboda na fahimce kamar batajin dadin jikinta"

tashi yayi ya shiga tare da barin su Mommah da su Miemie ah tsakar gidan tare da matar Uncle Umar.

Bayan ya shiga ne yake tambayar ta "mye ke damun ta kwana biyun nan dik sanda sukazo musu yini se ta shige uwar daka tace batajin dadi?"

" bakomai dannan" tafada tare da dorawa da " banajin dadi sossai ne"

"Mye ke damun ki ne Gwammah?" Poppah yafada.
"Haure na ke ciyo" tafada ataqaice.

"Toh bari gobe da safe Nayo sabko se na kaiki asibiti" inji Poppah
"Toh" dannan tafada tare da ballar goro.

Poppah zaro ido yay yace " Kaii! Gwammah wannan wane irin jarabar cin goro ne? Keda ke ciyon haure?"

Dariya tayi tare da cewa: oh!!!! Wanga yaro baka rabo da abin dariya, wai jaraba? Cin goron ne jaraba??? Hmmm dariya kawai tayi tare da girgixa kai.

Alal haqiqanin gaskiya Gwammah tana matuqar qaunar danta wato Poppah, Domin kuwa dik cikin ya'yan ta shine kadai idan ya ganta cikin damuwa yake qoqarin yawan matsa mata da tambaya akan mye ke damunta? Koh bata san gaya mishi dole ta gaya mishi saboda takurata da yake, sossai kuma yake qoqarin yaye mata damuwar ta ta hanyar sakata nishadi koh yayane, Domin Poppah yanada barkwanci musamman idan ya kebance da Mahaifiyar tashi, tofah dole ne se ya dinga sakata daria.
Hakan yasa take matuqar ALFAHARI da dan nata,. Sossai kuma take tausaya ma kanta hakama da duka yayanta da jikokin ta aduk lokacin da ta tuna da wani abu, dogon numfashi tajaa tare da furzarwa.

"Lafiya dai yar tsohuwa ta?" Poppah yafada da sigar tsokana, yaqara da " naga kina dogon nazari, dan Allah Gwammah kada kisa dogun damuwa koh tinani aranki plzz, sanin kanki ne bamasan abunda ze sameki balle ya daga miki hankali har ya kai da kwantar dake, so dan Allah ki rufamana asiri kada ki jama kanki wani ciyo da muma karan kanmu baki daya, Allah ya qara Lpia da nisan kwana"

Tin lokacin da yafara maganar ta tsareshi da ido, bayan ya dasa aya ne, tayi murmushi tace to "Allah yayi muku Albarka"
" Ameen" yace tare da tashi.

Kamun ya qarasa qofah wayar shi tafara ringing, ganin wacce ke kira yasa ya dawo ya zauna tare da daga wayar ya kara a kunne.

Yayi 10mnt yana sauraron Abun da ake fada daga dayan bangaren kamun yaja fasali tare da fadar;
" subhanallahi" me ya faru haka?? Abun har yakai haka? Ahh lallai, to ina dangin daddyn nata? Aah Toh dan Allah ki daina kuka banaso, yanzu abunda za'ayi tunda Abun yakai haka gobe gobennan kizo sokoto, tare da ita kuma ta hado kayan ta gabaki daya kuxo sokoto" Poppah ya fada tare da katse wayar..
*****

Cikin wani irin qasurgumin daji yake tafiya da motar shi, idan za'a kashe ka bazaka ce akwai mahaluqin da ke iya tinkarat wannan daji bah balle har ya shige shi.

Tafiya yayi acikin dajin mai nisa, kamin yakai inda motor bazata iya shiga bah sedai qafah, fitowa yayi yana ta tafiya,
Ah qallah seda yayi kusan 37mn yana tafiya kamun yakai gurin wasu manya manyan itace masu tsawo, tsayawa yayi tare da cire hulan shi, ta takalman shi ya ajiye gurin itacen, cigaba yayi da tafiya ya qara kai gurin wasu manya manyan duwatsu masu fadi da ramu aciki, anan ma ya cire rigan shi da wandon shi ya aza akan dutsen, ya rage daga shi se singlet da boxers, tsayawa yayi agurin ya qame qam batare da ya motsa bah, wani qara yaji mara dadin sauraron ji, atake yafara rawa yana juyi, rawa ya shiga Yi kamar wani mahaukaci sabon kamu, se da ya dauki kusan 10mnt yana rawar kamun wani baqin maciji ya fito daga cikin qasan manyan duwatsu,, dakata wa yayi da rawar da yake, macijin ne naga yazo gurin wannan mutumi, batare da mutumin yaji tsoro bah kawai macijin ya hau qafarshi ya laulayeta da jikinshi, Koh gexau wannan mutum beyi bah anan nagane cewa ya saba saboda be tsorata bah, se da macijin yay kusan 5mnt a kan qafarshi kamun yabace battttt.

Bayan bacewar macijin ne naga wannan mutumi ya fara hawa bisa wa'ennan manyan duwatsun, tafiya yake ba qaqqauta wa, yayi tafiya mai nisa saboda ma qananan duwatsu bane, dik mai imanin da ya kalle wa'ennan duwatsun se yayiwa Allah tasbihi, saboda tsananin girma da fadi da tsawo kai da ban tsoro dake garesu, ba qaramin mara tsoro ke iya kai kanshi kusa da wa'ennan duwatsun bah.
Ya jima yana tafiya akan duwatsun yayi nisa sossai,
Seda ya kai gurin wani rame me kamada qofah abisa dutsen kamun ya tsaya chaakkkkkkkkkkkkkk........



📝📝📝
Hii, Naji dadi matuqa da naga comments inku ah last update 💋nagode sossai domin kun qaramun qarfin gwuiwa, Domin kun tabbatar mun da cewa ba wahalar banza nake bah kuna biye dani 🤣 nagode sossai😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Allah ya bar qauna,

Plzz naga ruwan Comments,
Kowa ya gayamin ra'ayinshi...
Vote
Comment
Share💋
😘Teemahcutey ✍🏻
Typing...............................

Abun Alfahari Na✅Où les histoires vivent. Découvrez maintenant