Chapter 37

288 20 9
                                    




🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
             By
🌹Teemahcutey 🌹

Page 37.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

                ()()()()()()()()()()
"Good girl, gaskia kinyi k'ok'ari kawai the problem is that har yanzu ba kya iya controlling stearin motar da kyau, buh don't worrie u'll get use to it... nd naga kin cika son gudu sosai, don't do it know, coz ur still a learner kingane, nd mai koyo ba asan ya saba da gudu saboda ko kin saba kawai speed zakina dinga saka mata  which is bad for u females😉"

"Toh" a tak'aice Meenah tace saboda jin dad'in.

Seda suka d'auki kusan 1hour, kamun suka je Oasis aka siyo cake da icecream,

Dawo wa sukayi adai dai lokacin Ammie ta dawo, Parker wa sukayi gabaki daya su Meenah ne suka fara fitowa suka k'araso inda Captain da Afra ke zaune se wani zabga harara take, a haka ma Ammie tafuto sukayi mata Sannu da zuwa tare da wucewa ciki Meenah ta mara mata baya.

Wannan kenan.

7days later🌠
Allhamdulillah an sallamo Gwammah a daren jiya.
Gwammah ce zaune daram tare da Poppah, Mommah, Uncle Omar da kuma yaya Zarah da tazo jiya da safe.

Bayan dogon sharhi da Poppah yayi ya d'aura da "Allhmdllh Ala Kulli halin,mungode wa Allah mai kowa mai komai da ya kawomu wannan lokacin cikin k'oshin lafia, Allah ya k'arawa iyayen mu lafiya da Nisan kwana, alal hak'ik'anin gaskiya dama munaso muyi wannan magana amma mun d'aga ta ne har i zuwa samuwar lafiyar ki.... bayan abubuwa da suka faru da dama munason k'arin bayani daga gareki yake mahaifiyar mu... a lokacin da wannan abun ya faru dake Gwammah munyi magana da iskan Ameenatou wanda sukayi mana sharhi kamar haka: da farko sun gayamana cewa ke mayya ce kina aiki da manyan aljanu wanda shine yayi sanadiyar rasa mahaifin mu, sannan kuma kina so, kiyi amfani da Ameenatoun domin cimma wani boyayyen burinki, wanda mu bamu kai da sanin ko na menene ba, sun gaya mana abubuwa da dama wanda ya firgita zuk'atan mu, wanda se da na katsesu domin abubuwan babu dad'in ji ko kad'an. Saboda haka yake mahaifiyar mu manaso kiyi mana cikakken bayani akan yadda akayi kika fara MAITA, ko kuma kike son ki fara domin kuwa baki riga da kika shiga ciki tsundumdum ba.!
Shiru ne ya ratsa gurin na y'an dak'ik'u kamun Gwammah Taja dogon numfashi ta fara magana kamar haka:

"Daga farko Ina mai baku hak'uri game da wannnan abun da ya faru, ku yafe min da abunda zan gayamuku a yanzu, hakama zan d'ora muku da abunda baku sani ba game da mahaifin ku har izuwa yanda ya koma wa ubangijin sa.."

"Alhaji shehu wanda shine ya kasan ce miji a gareni, wasu shudadd'un lukutta da suka wuce, wani b'oyayyen sirri ne Wanda mahaifin ku ya b'oye muku, wanda ko ni da nake matar sa baya son ina tayar da wannan maganar, mahaifin ku sun kasance y'an biyu ne agurin iyayen su, Wanda su biyu ne kachal Allah ya baiwa iyayen su. Wanda mahaifin ku shine Shehu (Hassan) se Usman (hussain) sun girma cikin wadata da k'oshin lafia.. inda lokacin aure yayi aka za6owa kowa mata acikin su...(alokacin ba'a cika yin auren soyayya ba se dai na had'i) a duniya babu abunda mahaifin ku keso sama da qanin shi, ko rayuwar shi ze iya zarewa ya bashi saboda tsananin qauna, tun tasowar su suna k'anana suke da banbanci, domin kuwa shi Hussain Allah ya yi mishi baiwa wacce Allah beyiwa mahaifin ku ba, ba kasafai ake iya cutar shi a zauna lafiya ba, duk da ya kasance bayajin magana, a yanayin abubuwan da yake ne aka fara dangan tashi da yanada matsalar iska... domin kuwa ko mahaifiyar shi tayi mishi abunda bayaso to kuwa bazata kwana lafiya ba batare da ciyo ba, ko ciyon k'afa, ko hannu, ko kuma wuyan ta ya k'angare, magani suka shiga nema mishi amma da sukaga yana batun zarewa se suka k'yaleshi.... baya ragawa kowa idan ba d'an uwanshi hassan ba wato margayi mahaifin ku... ana cikin haka aka had'a mahaifin ku dani shikuma Husssain aka had'ashi da wata yarinya yar fullo mai suna FURERA. An saka auren mu lokaci d'aya batare da 6ata lokaci ba aka daura aure aka sadamu da gidajen mazajen mu.
Cikin k'ank'anin lokaci Hussain ya dinga samun matsala da matar shi wanda aka dangata haka akan cewa yanada macen iska (aljanah) cikin ikon Allah muka samu juna biyu a lokaci d'aya wanda nawa ya 6are.... bayan wasu shud'addun watanni Furera ta haihu ta haifo d'a namiji gwanin ban tsoro, alokacin bamu ta6a ganin balae irin na wannnan lokacin ba saboda duk wanda ya kalli wannan jaririn to baze qara burin kallan shi ba... Ya kasance bak'i wulik kamar baqar leda.. Gashi kuma tunda aka haifeshi beyi kuka ba kuma idanun shi jajawur abud'e kyammm yana kallan mutane... wani irin qatoton kaine dashi wanda ya datse daga gurin goshin shi... ana haka aka bada shawara ana tunanin maby d'an ruwa ne wato d'an aljani ne... so shawara aka yanke akan aje bakin gulbi a ajiye shi, to idan d'an ruwa ne zasu d'auke abunsu... duk wannan bidirin da ake Hussain yana gefe d'auke da d'an nashi yana kuka... Allah ya azomishi k'auna da tausayin d'an nashi..... a rana ta ukku da haihuwar shine aka yanke hukuncin kaishi gulbi saboda maganganu da suka fara yawa a bakin mutane... sosai mutan gidan ke kuka musamman mahaifin shi... bayan anje gulbin ne aka ajiye shi a ga6ar ruwan... an d'auki misalin minti ashirin atake jaririn yafara kuka se ya 6ace 6attt...😭😭 kuzo kuga kuka gun mahaifin ku da mahaifin jaririn... ana hakaa da k'yar suka dawo gida.
Haka muka cigaba da rayuwa yau dad'i gobe 6acin rai... ana haka Furera ta fara laulayin wani sabon ciki... a watan ta na haihuwa nima Allah ya azurtani da samun juna biyu har na kimanin wata hudu.. dayake cikin bezo da laulayi ba shiyasa bamu gane ba... a wani yammacin dare ne Fure ta fara nak'uda.. Cikin ikon Allah ta haifo jaririyar ta me kyau... da k'yar da sud'in goshi Hassan da Hussain suka shigo gurin ganin jaririyar saboda tsoron ganin jaririyar suke.. da salati abakin su suka shiga... zo kuga farinciki gurin Hussain da mahaifin ku....
Kar6an jaririyar mahaifin ku yayi mata hud'uba da FAD'IMATU ZAHRA'U.. wani sark'an azurfah mahaifinku ya d'akko wacce aka rubutawa Zahrah ya saka mata... sannan ya dauramata wani a hannu ya sakamata zoben azurfah... sosai yarinyar take shan magana saboda kyau da Allah yayi mata....a yammacin daren sunant ta wani Mummunan Al'amari ya faru,ranar munga bala'e domin kuwa cikin daren wani fad'a wanda bamu san menene mak'asudin yin shi ba ya tsinke tsakanin uwayen su mahaifin ku, muna tsaka da rabasu ba'ayi wata wata ba mahaifiyar su Hussain gurin gardama kawai ta jefawa mijinta tab'arya atake ya fad'i ya rasu, Abun ya bawa kowa mamaki soboda wannan jifan beci ace ya kashe shi ba amma da yake ajali ne ba yadda za'ayi, tana cikin hargowa ta k'arasa shiga cikin d'akin da yake, dama bakin k'ofa yake bayan ya fad'ine kamun ya mutu ya ida shiga d'akin, Hassan ba abunda yake in ba kuka ba... inda Hussain idon shi ya kad'a yayi jajur yana gefe bece komai ba.. ganin yadda mahaifiyar tasu ke jijjaga mahaifin su yasa hussan k'arasawa domin shiga d'akin... a lokacin k'arfe 11:20pm akwai wadatar haske saboda akwai wutar lantarki... Hussain ne yayi gaggawar tare mahaifin ku ya hanashi k'arasawa... kan kace mye wani irin iska mai kama da guguwa ya turnuk'e gidan .... ba'ayi wata wata ba wani Iska mai qarfi ya buga wanda shine yayi sanadiyar rushewar ginin dakin da surukaina suke wato mahaifin mahaifin ku kaka agurinku,
Inalillahii shine abunda mijina margayi babanku yake fad'a wanda atake Hussain kamar wanda aka tsikala kawai yayi wuuffff ya shige d'akin matar shi, binshi mahaifinku yayi wato Hassan... ganin ya finciko jaririya zahra yasa abbanku tare shi.. amma inaaa tuni ya ture mahaifinku ya bar gidan... tashi mahaifinku yayi Yabi bayanshi amma mye? Ba abunda ya gani... ba alamar su, bega ta inda suka bi ba, kuma baya tunanin ya isa ya billewa ganinshi tinda yana tureshi ya tashi ko secs ba'ayi ba..
Inalillahii wa'innah ilaihir raji'un😭 bamu ta6a ganin masifa irin ta wannan ranar ba, ga mutuwar mahaifan su ga 6atar dan uwanshi da yar shi... ga Furera duk ta shiga wani yanayi... bayan safiya ta waye ne aka zo aka kwashe ginin aka fito da gawarwakin iyayen su ya SUBHANALLAH!!!😭 ba kyan gani domin kuwa ginin yayi musu babbar illah... da k'yar aka d'an tattara su aka dan wanwanke domin ba'asan yanda za'ai musu wanka ba saboda yanayin su🤦🏿‍♀️ ahaka aka kaisu makwancin su. Allah ya gafartawa kakaninku😭😭..
A haka akayi zaman gaisuwa ana jiran tsammanin dawowar Hussain amma inaaa shiru kkji kamar an shuka dusaa...
Ana zaune jugum cikin jimami da taradudin abunda ya faru kwatsam se ga wasu mutane Inalillahii wa'innah ilaihir raji'un😭 se gasu da gawar Usman Hussain😭 ranar munga tashin hankali... sunce sun tsinci gawar ne acan bayan gari... munyi musu tambaya akan cewa basuga jaririya a tare dashi ba? Amma inaaa sukace ko alamar jariri babu agun... koda Furera taga gawar mijin nata da kuma tabbacin rashin ganin y'ar ta ai kuwa atake ta fad'i zuciyar ta ta buga akayi gawa biyu😭 Inalillahii wa'innah ilaihir raji'un😭.. a wannan ranar haukace wa kawai ne mahaifinku beyi ba....na tabbata da yanada k'ararrun kwana a wannan lokacin ba abunda ze hana zuciyar shi ta buga yabi mahaifanshi da d'an uwanshi.😭💔...
Wanka akayi musu aka kaisu makwancin su.. Allah ya jik'an su da rahama... mutane se sonjin abunda yafaru suke amma mahaifinku ya haneni akan kada na kuskura na gayawa kowa... haka akayi kuwa kowa yaja bakinshi yayi shiru.
Ya subhanallah tunda iyaye na suka haifeni ko a tarihu ban tab'a jin irin wannan k'addarar da ta afka mana ba. Cikin kwana d'aya mun rasa mutum biyar... Kakanin ku, k'anin mahaifin ku, matar sa, da kuma y'ar su zahrah wacce haryanzu babu labarin koda gawarta ne.. tin daga lokacin rayuwa tayiwa mahaifinku zafi... cikin k'ank'anin lokaci ya rasa gabaki d'aya danginsa.. dangin sa sune farin Cikin sa Abun Alfaharin sa domin kuwa nasha wahala kamun ya dawo dai dai, bayan lokaci ya jaa na haihu anan ya d'an samu sa'idah... inda ya tattara duka k'aunar da yake yiwa y'ar d'an uwanshi wacce ta 6ata ya d'orawa jaririyar... ranar suna aka rad'awa yarinya sunan yayar ta da ta 6ata wato y'ar k'anin mahaifinku Zahra.. so da k'aunar da yake yiwa d'an uwanshi yasa yakejin kamar Zahra y'ar Hussain ce ta dawo.. ahaka rayuwa ta cigaba da kasancewa har izuwa yanzu"

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now