Chapter 42

260 20 11
                                    




🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 42.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

"Ya zama dole nabar gurin coz banzo da any protection ba" dakatawa tayi tana kallan k'ofofin guda biyu, to ko wacce ma zata shiga? Ohow, ehh lallai akwai aiki gabanta, fararen doors in ta dinga kallah d'aya bayan d'aya, duka sunyi k'ura tamkar ba mutum a ciki, hmm lallai Dad in Captain akwai b'adda kama, to ko dai an d'auke shi anan? Noo!! Gaskiya I doubt!!
Juyawa tayi tare da komawa, bayan ta saka hular kanta ta goge handle in k'ofar both gurin shigowa da kuma fita.
A hankali ta cigaba da tafiya har ta bar gun ta koma side insu.
Tana komawa kawai wanka ta sake saboda y'ar k'urar da tashiga, bayan ta fito ta sake kaya ta kwanta tana y'an tunane tunane.

.
.
.
"Nan da two days ya kamata mu kammala komai, kinga a ranar ya kamata mu saka a d'auke ta, kinga zamu cusawa Haidar da y'an uwanmu duka cewa ai bata son auren shiyasa ta gudu, idan basu yarda da wannan ba kinga se muyi amfani da d'ayar hanyar yanda auren ze watse kawai"
Jimmmm Zeenatu tayi kamun tace; " ehh haka ya kamata, kuma inada wa'enda zan saka su d'auke ta cikin sauk'i ba tare da an samu mishkila ba, kawai the problem is that bana son suyi tunanin wai kidnapping inta akayi kingane? Nafison musamu wata hanya wacce zata cimma wa'enda zasu d'auketa da kanta, kinga idan akayi hakan, to lallai zasu iya amincewa"

"Ehhhto kusan hakannne maganar ki, but ya kike ganin zamuyi kenan? A naki tunanin tare dawa kike tunanin ya kamata sutafi? Abrar ta fad'a cikin zak'uwa.

"Ehh to nasan duk maccen da za'a kawowa lefe, ya kamata ace tabar gidan su at least ko neighbours ne tashiga har taron ya watse, kuma nasan a raranar zata kasance cikin friends inta wanda idan akayi yunk'urin kamata ta wannan hanyar to ba makawa na tare da ita zasu bada tabbacin cewa lallai sace ta akayi, which is a plan inmu na farko ba haka mukeso ba! Tana kawowa nan tayi shiru.

Abrar ce tace; "ya naji kinyi shiru? Ko ba mafita ne afasa lamarin?

"Ke banza ce wlh ana maganar kwarai kina harkan jakanci" shine abun da Zeenatu tace,.

"Kece babbar jaka da kika kasa gano mafita, look, nifa wannan abun ba dole ya zamar mun ba, though ke nake taimakawa ni bawani abu zanyi achieving ba kin gane? So idan naga dama I can simply quit the job, I'ope u get me? Allah se na barki da dabararki kina kallo masoyinki ya aure wata ba ke ba shashasha kawai" kitttttttt Abrar ta kashe wayaa.
(Nikam nace wannan drama tasu har Ina? Pretend after pretending? Lallai su Abrar manya, kamar dagaske kuwa Zeeno take taimakawa🤣bayan ko ita tanada nata k'udirin, hmmmm we'll se ai acikinku wanda zeyi succeeding. )

Immediately tana kashe wayar Zeenatu ta k'ara danno mata kira, se da ta katse still ta k'ara kira, d'auka Abrar tayi tare da fad'ar "lafia malama?

" da Allah saurara ke banza, mu cigaba da maganar iya masifa an, na samo mafita,!

"Okay inajinki" Abrar ta fad'a a k'age, domin kuwa ta matsu su sami mafita.

"Yawwa, kinga kinfini kusanci da ita, nd kinga mu zamu kawo lefen,so kawai zaku fita tare da ita, kice zata rakaki kinga idan yaso daga can gurin se a d'auke ta..."

"Ahhhh malama dakata!!!!!!

Shine abunda Abrar ta katse ta dashi, sannan ta d'ora da: "kamar ya na fita tare da ita? Ohoowww!! Kina son ni a zargeni kenan koh? A'a wallahi, gaskiya a canja plan.."

"Inalillahii Abrar, nikam kin fara bani hard time wallahi, abeg if u've something about it plzz just go straight to the point.... tell kawai nikam yanzu I've no idea gaskiya.... shine abunda Zeenatu ta fad'a cikin sanyin jiki.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now