Chapter 22

298 26 14
                                    



🧚🏻‍♀Abun Alfahari na🧚🏻‍♀
By
💐Teemahcutey 💐

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Page 22.

Sallama tayi tare da ida shigewa kai tsaye a gidan, da sauri Waleeda ta tashi daga wanke-wanken da take ta rungume k'awar tata.

Dagannan fah suka shige uwar d'aka.
( nace wanke-wanke ya tsaya 😅)

Se k'us k'us suke faman yi, ni banama jin abunda suke fadi.

Daga dayan 6angaren naji walida nacewa:
"Am nace ba, Meenah kinfa fara bani labari Abun da kika tuna game da hadadden tsadadden gayennan?"

"Tsaki Meenah taja.. mtswwww, ke fah Waleeda banza ce, son maza kamar me..,"

"Aafah Meenah bana san haka! Wallahi natsani kicemun mai son maza, haka kawai? Daga wasa, gaskia banaso, kada ki k'ara ban dauka, daga kawai na wani tambaye ki se cibi yazama k'ari? mtswwww"

Waleeda taja dogon tsaki tare da fita daga d'akin,.

Meenah ma ta6e baki tayi, tare da shige dakin Mama ramatu domin gaida ita.

Gaisawa sukayi tare da tambayar ya can gurinsu? Lpia qlw tace, daganan suka cigaba da firarsu.

Wayar haj. Ramatu tashiga ruri, dagawa tayi tare da sallama k'unshe a bakin ta.

Gaisawa sukayi a dayan bangaren.

Bayan ta kammala wayar ne ta kalli Meenah tare dace wa;
" Aminatou, tashi maza, da maman ki na gama waya tace kinyi bak'i,"

"Toh Meenah tace tare da mata sallama,"

cikin ikon Allah sega Ya haidar kawai yace tazo ya maita ita,
K'ememe Meenah tayi akan ita wallahi bazata bishi ba machine 🏍 zata hau,

Dagewa yayi akan dole shi ze kaita baxata hau machine bah, da kyar da sudin goshi mama tasa baki, sannan ta yarda.

Fita tayi batare da takalli gefen waleda bah, tabe baki Mama ramatu tayi domin tasan aikin nasu ne sukayi wato fada.

Waleeda kuwa ko k'ofarda tafita bata kalla ba.

Ya haidar ne yabi bayanta, tsaye ya cimmata ta rik'e k'ugu. Bude motar Tashi yayi ya shiga,
Without any second thought Meenah ta bude bayan motar ta shiga, ya Haidar kuwa Abun dariya ya bashi, da yaso yayi mata magana akan ta dawo gaba tinda ba drivern ta bane amma ya tsinci kanshi da kasawa dan yasan da gangan tayi dan yayi magana tunda an hanata hawa mashin, kawai sai ya fita batun ta ya tada motar suka wuce.

"Yo in mutum in ganin budurwar shi zeyi ai base ya la6a ta hanya taba, tunda idan yaje ba koro shi za'ayi ba"

Sarai Ya Haidar yaji abun da tace
"Mye kika ce?

Shiru Meenah tace domin tasan halinshi da ta maimaita ze dalle mata baki ne.

Ganin yayi wani dan k'aramin zagaye yasa taji hankalin ta t saboda tsiwarda t tun a gida.

Parker wa yayi a, D&D restaurant,

Washe baki Meenah tayi tare da cewa:

"Ayyaa Ya Haidar hala dai wani Abun zaka siya?

Banza yayi da ita yafita motar.
Dadine yakama Meenah domin tasan Abunda ze siya,

Tasan nanne ake sayar da Favourite meat pie na Miemie, to tasan dole asiyo da ita domin ba k'arya D&D kwararrine gurin iya meat pie, da yake mai gurin farar fata ne daga qasashen qetare. Mai gurin ne ya fito kazazaf Meenah tayi ,tafito ta gaisa da shi, domin yana da fara'a sossai dik da kasancewar shi bature, ya iya Faram faram da mutane, sun gwane gurin sarrafa shawarma da sauransu. Abincin su na da dadi musamman kayan snacks nasu.

Abun Alfahari Na✅Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon