Chapter 25

269 22 13
                                    

🧚🏻‍♀Abun Alfahari na🧚🏻‍♀
                  By
   💐Teemahcutey 💐

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Page 25.

Sun saka ido sossai har wannan mutumin ya k'araso, anan suka tabbatar da cewa Joseph ne d'aya daga cikin waenda train bai hau kansu ba.
Dama dashi da Captain ne suka b'ata,
Da gaggawa suka d'aukeshi aka sakashi a Ambulance domin duba tabbacin yana raye ko ya mutu.
Haka suka cigaba da zaga ruwan, suna k'ara zurfafa bincike domin basasan wanda ba d'an k'asarsu ba yazo da niyar taimakonsu amma ace ya salwanta, aganinsu wannan babban balae ne ze hassasa tsakaninsu da y'an k'asarsa.

Kamar ace su juya d'aya sashen gurin wasu y'an duwatsuna suka hango captain yashe anan,
Da sauri suka je agun domin tabbatar da Abunda idansu ke gane musu.
Da sauri naji d'aya yace;
"FREEEZ NUMBER THIRD!! FEEEED IT BACK! AUSTRIAN 322etas$! MISSION ACCOMPLISHED! WE THANK LORD!"

Atake gabaki d'ayan su suka k'ame suna fadi da yarensu..

"Twërsytîv sērÿįœm"

K'ame wa sukayi tareeda sarawa junansu atake aka saka taken k'asar nasu🎶🎵➿

Daganin Captain kam yasha ruwa, Domin kuwa kayanshi sharkaf suke da ruwa, ga kuma tarin rauninika a jikinshi abun ba sha'awar gani, he's in very in censorious condition, ya jimu sossai. Hakama yasamu very severe bleeding, most especially inda aka harbe shi a k'afa.

Daukan shi sukayi bisa wani d'an abu wanda aka fitar daga cikin ambulance, a 360 sukabar gun.
Basu suka dakata daga speed inda suka sakama car nasu ba seda suka gansu a DÖBLING PRIVATE HOSPITAL. Anan suka taka birki.
Atake manya manyan likitoci da nurses sukayiwa gurin tsinke domin kuwa kowa yana da update na abunda ya faru, so suna k'aunar k'asarsu dan haka dole su taimakawa wannan bawan Allah da ya taimaka musu.

Atake aka kaishi *Emergency* ana Bashi taimakon gaggawa,

Gabaki d'aya duniya ta d'auka Domin kuwaa kowa awannan lokacin yasan abunda yafaru ah Austria, musamman da k'addara ta afka ga d'an Nigeria.

Atake aka tattara dik wani details nashi da ya kamata akayi komai cikin sauqi, sunji dadi sossai Domin a iya bincikinsu sun gano cewa lallai d'an masu shi ne, bima'ana sananne ne sossai.

A bangaren dad in Captain tinda ya gama kallan news in kenan atake, xufa ke karyo mishi ta ko Ina, hankalin shi bai k'ara tashi ba seda yaga yana ta kiran wayar Ammie amma baya samu, sossai hankalinshi ya tashi domin yasan ko ma yane dole ne tabbas Ammie taji wannan ~*MUMMUNAN AL'AMARI*~ ( my next novel Insha Allah)
Sossai hankalin shi ya k'i kwanciya, atake yasaka aka mishi booking flight na tomorrow firsting in the morning, Domin alokacin da wuya asamu jirgi.

Sossai Ammie take kukan wannan Al'amari, har ga Allah bata san ta rasa tilon d'anta a daidai wannan lokacin,

Ganin kukan da take yayi yawa ne, yasa Meenah fara mata nasiha mai sanyaya jikin dik mai sauraro, Nima dai Galala nai Ina kallan Meenah, ashedai Meenah nada hankali? Lol.

Sossai nasihan Meenah yay tasiri aranta, atake ta share hawayen ta ja Meenah ajikinta tana mai mata Addu'ar ci gaba a rayuwa
" hak'ik'a ke 'yace ta gari, wacce dik uwar da Allah ya mallakama ita a matsayin 'ya dole ta godewa rabbani, madallah dake d'iyar kirki Ameenatu, Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki miji nagari, inamai godiya akan wannan tunatar suwa da kk mun, hak'ka kuka ko hargowa baya maganin masifa adik lokacin da ta kunno kai acikin Al'umma, Hak'uri da juriya shine maganin dik wata musiba anan duniya, A lokacin da muke cikin farinciki bada shawarar mu ya saka mana ba, amma ahakan zamuji dad'i kuma mu gode mishi , wata k'ila ma harda y'ar bushasha saboda farinciki, tinda hakane, bai kamata idan ya jarabce mu da d'an k'an k'anin abu ba mu butulce mishi ta hanyar kuka, bobowa, wayyoni nashiga ukku! Kamata yay mu gode mishi no matter how the situation is,. Allhamdulillah, Allah ka bama d'ana Lpia, Allah ya tayarda kafad'in Shi"

Dogon numfashi Meenah taja., Domin Alal hak'ak'a taji dad'in wa'innan kalamai da Ammie ta furta, tasan ko ba komai hankalinta ya d'an kwanta zatai mishi Adu'a da kyau da kyau batare da komai ba.

Da k'yar Ammie ta Tashi daga inda take. Hadda wani jirin Bala'i ke d'iban ta.
Sama ta haura domin gabatar da sallar magrib, adaidai nan Meenah ta Tashi da niyar bin bayan Ammie domin ko ita ta gabatar da sallah kawai se taji hargowa da bobowa ta Afra wai tana kuka, "wayyo ita Allah Captain yaya, Tashi ga ukku an kashe mata Captain"

Sororo!! Meenah tayi tana kallan ta.

"Ke dallah kin shawa mutane kai da hargowa kamar wata kafura dallah can kama mana baki, wayace miki ya mutu ne? Mtswww dallah malama jeki kiyi mishi addu'a yafi wannan shashancin da kike"

Chakk!! Ta tsayarda kukan munafur cin datake tayi tana kallan Meenah. Kalaman da Meenah ta gayamata yamata zafi, ya chakar mata zuciya, amma ahakan ta hak'ura ta juya tabar sight in. Duk da har ga Allah kukan har ruhinta yake saboda tana matuk'ar k'aunar Captain bazata so ta rasashi a dai dai wannan k'arnin ba.

Misalin k'arfe 9;30am ta mishi a babban filin jirgi Sultan Abubakar Maccid'o na |||.

Atake convoys na motocin gidan shi da sauran guard in captain suka cika farfajiyar Sansanin Airport in.

Sossai Ammie tayi mamakin jin mijinta ya sauko. Coz bata san da zuwanshi ba.

Bayan dawowan shine acikin gidan agurguje yaje sight in Ammie domin ko b'angaren hajja be kalla ba.

Sossai yayi mamakin ganinta kamar ba abunda yafaru, yaji dad'in ganinta ba cikin damuwa ba gaskiya.

Bayan sun kammala gaisawa ne suna maida zance abunda yafaru. Ananne ma yake shaidamata ai shugaban k'asan Austrian ya kirashi ya jajanta mishi akan abunda yafaru, kuma ya k'ara da cewa Captain Yana samun kyakyawar kulawa daga asibitin da aka kaishi saidai har yanzu bai farfad'o ba, amma kada su damu idan yasamu sauk'i zasu mayar dashi har gida Nigeria cikin k'oshin lpia.

Anan dad yanuna rashin amincewar shi. Shikam gaskiya hankalinshi baze kwanta ba har sai yaje yaga a wane hali boy inshi yake ciki.

Ammie girgiza kai tayi alamar gamsuwa da lamarin.
Suna cikin hakane se aka kira dad aka shaidamishi cewa flight in da yasa ayi booking zai tashi around 1:30pm.

Sossai Ammie tayi farinciki najin har yayi musu booking flight Wanda zai kaisu a Austrian.

Meenah Ammie tasa akai mata kira.

Dama suna zaune ne ah parlour ita kuma Meenah batama san da xuwan Dad in Captain ba.

Tin tana akan stairs na saukowa take kallan Dad in Captain har ta sakko idanta na kanshi, adaidai shikuma ya d'ago ya kalleta.

Rasss rasss yaji gabanshi ya fad'i haka kawai yaji yarinyar bata mishi ba.

K'araso wa tayi ta durk'usa ta gaidashi, amsawa yayi a tak'aice.

Dawowa tayi ta zauna gurin Ammie tace gani Ammie,
" Yawwa baby dama abban Captain ne yazo shine nace bara nakiraki ku gaisa, Nd ishaAllah by 1:30pm flight inmu zai tashi zuwa Austria, ban masan da maganar ba. Da abban naku baiyi saurin mana booking 2 tickets ba da naso namiki visa sai mutafi tare. Amma da yaddar Allah bayan muntafi ko yayane zan saka amiki visa sai kizo. Because ba na son ayanzun muyi nisa dake. Inshallah zanyi magana da Abbanki da kuma Umma ki kinji"

D'aga kai Meenah kawai tayi Domin takasa tantance awani hali take ciki na tsakainin farin ciki da akasin hakan.

Sorry for the late update please

Da Allah amana addu@ muna exams🙏🏻🙏🏻

Thank you so much for the love nd support 😇😇😇😇😇

See yeah soon💋💋💋💋💋💋💋💋💋

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now