THE LAST PAGE..!

2.6K 110 7
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *KA'RSHE*.... _END_😥👏🙌✌

            *Chapter 40*

     
""Azeema bata Rufe Shekara da Shiga mkranta ba,Ciki ya bulla ajikinta,lokacin sunyi jarabawar Karshen semister,sun tafi hutu suna Shirin zuwa aji biyu,Inda Allah ya taimaketa Su Afiya shekaransu daya lokacin da wata daya,tuni sun yi girma suna Tafiyansu ko"ina,in ka gansu bazakace Azeema ta haifesu ba,sakamakon basa kama da ita ko kadan,Sai da da Aliyu suke kama,kana ganinsu daga gashin kansu zaka zargi kodai sun hada jini da larabawa ko Buzaye cikin biyu za"ayi daya,balle yadda Su Afiya suka dauko bakin gashin babansu,suna kanana dasu,ammh in Azeema tamusu tsifa ta daure musu da band Abun sai masha Allahu kawai.

Da farko Azeema tayi bori game da cikin jikinta,ta dinga kawoma Aliyu uzirinta,ga yara basu bar shan nono ba ga Kuma karatunta ita yanzu ya zatayi,zama da ita yayi yayita lallashinta dayaga taki yarda sai ya dauketa sukaje wani privet hopital suka samu wata likita,yasanar da ita mtsalansu nan da nan ta Shiga yima Azeema Fadan,ya Allah zai bata kyauta kuma tayimai butulci,tasan Adadin mutanen da suka zauna a inda take,suna mata kuka Allah bai basu haihuwa ba,koko tasan Adadin mutanen dake zaryan awannan hospital din duk dan Allah ya basu haihuwa? Azeema ta girgiza kai Hawaye suna zubomata tacigaba da Fadin"Kuma Shine ke Allah yabaki Kike neman kiyi butulci toh ahir dinki domin sai Allah yabarki da dubaranki,ai yafi ki sanin kina da ya"ya kuma ya zabeki acikin dubu ya baki wannan kyautan,toh tun Wuri ki daga hannu sama ki godemai kada Allah yayi Fushi dake"

jin haka yasa Azeema ta daga hannu hawaye na zuba tana godiya ga Allah,nan likitan ta sausauta takaramata da shawarwarin yadda zata kula da kanta da ya"yanta,Tunda ma taji su Afiyan sukai shekara daya tace ta ciresu anono babu damuwa,Sai acigaba da basu abinci wanda zai cigaba da gina musu jikinsu,magungunar karin lafiya dana karin jini ta Rubuta musu sukayi mata sallama,sai da suka biya phamarcy suka siya magungunar kafin su Wuce gida,Ranar dai Azeema kuka ta Wuni yi,Aliyu na aikin lallashin Tunda aiki ya riga ya sameshi.

  Haka Azeema ta cigaba da kula da cikinta sukuma su Afiya Ta ciresu anono ta damkama Baba lami tana cigaba da kula dasu,itama kuma tana Renon Cikinta tana kuma cigaba da karatunta babu wani mtsala domin Aliyu na tsaye kanta ita da ya"yanta,Cikin ikon Allah sai ga Azeema ta haihu kusan lokaci daya da Zafira,Azeema ta haihu yau Zafira ta haihu washegari Kuma duka mata Ranar suna Yar wajen Azeema taci sunan Gimbiya Razeenah,,suna kiranta Sajida,sai yar wajen zafira taci sunan Mahaifiyar Jabir wato khadija suna kiranta Meenal,tsakaninsu da Safaratu kwana goma sha biyar ne ita ta sauka ta haifi danta Namiji wanda yaci sunan kawu Bala,suna kiransa da Sajjad.

 
*AFTER 5 YEARS*

""Ashekaru biyar da suka gabata Abubuwa dadama sun Faru na Farinciki da akasinsa,na bakinciki Shine Rasuwar Ummah mai babban daki,tare da Rasuwar Baba Ade wadanda suka rigamu gidan gaskiya,Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansu Da Gafara Ameen.

Ababen Farinciki kuwa Shine Shekaru biyu dasuka gabata Maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yayi murabus daga kan karagan mulki ya nada da'nsa Aliyu Abdulnaseer Tambari,wanda yayi Retire,a aikin Soja,suka tararra shida da duka iyalansa suka dawo Niger da zama lokacin Azeema ta kammallah karatunta sai tazo nan tayi bautar kasarta,Nadin sarauta da sai da aka jadaga kafin Ayishi domin Aliyu Tuburewa yayi Shifa baya bukatar Sarauta yafi bukatar Aikinsa Fiye da komai,ga Umar nan Adorashi shi yabarmai har Abada,Sai da yaga maimartaba yanuna bacin Ransa sosai,kuma su Kawu bala da Mallam lawal suka tayimai Nasiha kafin ya yarda,itako Azeema daga sama taji Abun kamar almara wai Aliyunta zai zama sarki,bata nuna Rashin goyon bayanta ba,saima kara karfafamai gwiwa dataitayi,lokacin ma tana da wani cikin ajikinta,Shi duk damuwarshi daya yasan baza"a barshi yazauna da Azeema ita kadai ba,dayayimata wannan complain kallonsa tayi tana dariya tace"To sai me Ehe,ai wlh bana da wani haufi akan Sadaukina ko yanzu wata ta Shigo na tabbata ni Azeema nayi mata zarrah har Abada,saboda haka karka Damu kanka ga Ni"ima,babu wacce ta dace ka aura sai ita,domin itama masoyiyarkace ta gaskiya nekamar muneera taji lbrim wacce ke Fadin kyawawan Halayyan Azeema domin tana bata girmanta amtsayinta na Matar wan mijinta,ita ma Azeema tana tafiyarta da ita yadda Yakamata.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 06, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now