ALIYU GADANGA..!

1.9K 101 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_Special Day..!Special person,..!Special birthday..🍢🍡🍧..! *1/1/2020* May dis Day be d begining of Anoder beutifull year 4u...May there be pleasant,suprises...Loads of joy And infinite happiness...Wish u a very Happy birthday *HEARTBEATDADDY*_😘💃💃❤💕💖

        *Chapter 39*

""Azeema sun sauka A abuja lafiya,ita da gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu kadai sukazo,sai wata baiwa mai Suna Lami,dattijuwace sosai wacce zata dinga taimakama Azeema da kula dasu Anwar,inna Ramatu kuma daga nan Abujan gombe zata wuce wajen mijinta.

    Gimbiya Razeenah ita takira gadanga awaya ta sanar dashi saukansu,bai dau lokaci ba sai gashi yazo Filin jirgin na Nnamdi Azikiwe international Airport,koda ya iso,wajen da Azeema yafara tozali ya kalleta ta kalleshi lokaci daya suka dauke kai,kowa naji da kansa,cewa shi aka batamawa saboda haka shiza"a bama hakuri,ko su Anwar hannu Baba lami ya karbesu kafin ya daukosu su rankayo zuwa cikin barikinsu dake Abuja,ko zaman motan baya ta Shige ta hade rai sosai,gimbiya Razeenah ne ta Shiga gidan gaba.

Suna isa suka tarar da kyau da tsari irin na gidajen wajen harsunfi na kaduna ma girma,domin na nan din 3bedroom ne,da kuma falo har guda biyu,bayan katon kichen mai hade da store,kuma ko"ina yaji kayan alfarma babu Abunda ake bukata dama sai kayan da mutum zai saka su kawai zai zo dashi koda suka iso Tuni Ummah tagama gyara ko"ina harta Abinci sai tayi musu,suna zuwa Sallah sukayi kafin su zauna suci Abinci ana hiran Duniya da tambayan Mutanen chan,itako Azeema tunda tayi wanka tashige dayan bedroom din ta kwanta ko kara lekewa batayi ba,su Afiya suna wajen Baba lami,suma sunyi barci Tunda sukaji Ruwan zafi,da kuma nono,shikenan aka daina jin motsinsu,shiko gadanga Tunda yakawo su ya fice bai kara waiwayan gidan ba,saboda bayaso su Raba hali Shida Azeema don yaga take takenta so take yau takureshi har yatankanta.

Basu samu tafiya ba sai washegari da safe Gimbiya Razeenah da Ummah sai inna Ramatu suka rankayo sai kaduna suka bar Azeema da Baba lami da kuma mijinta Aliyu gadanga,daga kaduna ko kwana inna Ramatu batayi ta matsa tana son komawa gombe aranar Shiyasa Kawu Bala yasaka Direba ya kaita dauke da sha tara na arziki data samo daga Masarauta,dakuma wanda Kawu yakara mata,Gimbiya Razeenah dai tanan nan sai ta kwana biyu inji Ummah.

Tunda Su Ummah suka Tafi Azeema tashige bedroom din data zaba amtsauyin nata,takarayin wanka ta Shirya cikin Riga da sikat na Atamfa,wanda suka dauketa sukamata cas dasu,Baba lami na Falo tana Fama dasu Anwar yan Rigima itako kichen tafada domin lokacin har 11 ta gota yakamata tadora musu lunch ko badon Shi ba,don cikinta dana Baba lami.

Farar Shinkafa tadafamusu,saboda babu cefane,dama tazo da Soyayyar miyarta wacce taji kaji aciki,daga Niger wanda goggo da kanta ta soya mata shi,sukaci da ita,suna gama ci ta kwashe Abunda suka bata ta kai kichen ta wanke ta kife ta tsabtace wajen kamar ma batayi girki ba,tadawo Falo ta amshi Afra dake kuka tana Shiga bata Nono,Tagama bata kenan Ta karbi Anwar tana bashi ita kuma Afra baba lami ta sabata,tana dan jijjigata nonon ya kwantamata kada tadawo da ita,sai ga Gadanga yashigo da sallama,Azeema na jin sallamansa ta hade rai,tayi kini kini dashi,Baba lami ce ta zube tana jeramai Sannu da zuwa ya amsa yana mika hannu ya karbi Afra dake hannunta yazauna kusa da Afiya wacce ke kwance tana wutsil wutsil da kafafunta,kumatunta ya latsa yana Fadin"Afi Afi yanmata,kina wasa ne..? yafada yana daga Afra dake hannusa,Baba Lami kuwa Tunda ya amshi Afra ta shige dayan bedroom din da Azeema ta sauketa aciiki

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now