ALIYU GADANGA..!

1.9K 91 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

         *Chapter...23*

*BAYAN WATA DAYA*

   ""Acikin wata daya da Tarewar Azeema Fadar irin cigaba tare da zaman lafiya,dakuma wata soyayyah dasuke nuna ma juna bata baki ne,Tsayawa Lura da yadda suke kaffa kaffa da juna sai ka dauka sun Shekara goma ne,suna Soyayyar,uwa uba ga wata shakuwa daya Shiga tsakaninsu,Azeema ta yarda takamu da Son yaya captain kamar yadda Shima yakamu da Sonta duk da bai Furtaba tana gani a aikace.

  Taje gidajensu Anty madina da Anty mardiya sau daya,sai gidan Kawu dasukaje Sau biyu,dukkansu sun samu kwanciyar Hankali sunyi kiba sunyi kyau kamar basu ba,Kowannensu Kokariin Farantama dan"uwansa rai yakeyi kowa bayason ganin bacin ran Dan"uwansa baza"ace basu taba samun sabani ba,A'a Suna samu buh baya wani Tasiri suke bama juna hakuri domin dukkansu babu wanda zai iya Rashin dan"uwansa,Tuni Azeema ta Manta  da wata Aba Azeeza da inna Ramatu mahaifinta dai take kira taji yaya lafiyarsa sai goggo wanda bata iya kwana bata kirata ba,Tarigaya tazama wata ginshiki agareta.

Lokacin Jarabawansu  ya kusa Aliyu sukayi mgana da goggo yace in lokacin yayi zaizo da kanshi yayimata Rigistration Allah barshi in lokacin Yin jarabawan yayi sai ya maidota ta Ta rubuta ahaka suka rabu,wanda ko Azeemar batasan kwanan zencen ba.

_________________

  Conole Sulaiman yana zaune cikin kayatattacen Falonshi na cikin Barikin,yana hutawa gefe daya kuma Sigarice Ahannunsa yana ta zuka yana Fidda hayaki,daga ganin yadda yake sarrafa zakasan ya kware, wayarsa dake gefensa tadau Tsuwa yana dagota ya zaro ido yana mamakin mai kiran da rawan jiki ya daga kiran yana fadin

  "Allah Taimaki Hajiya Muneera yar Mutan gombawa,yau kuma an Tuna dani ne, bayan tsawon lokaci An samu akwandon shara.."Wata dariyar kissa muneera tayi kafin tace"Har na isa?ka manta hausawa na cewa Da tsohuwar zuma ake mgaani,"Dariya ya saka yana Fadin"Hakane kuma ta wajena,Allah yasa wannan kiran an min ne,domin kashemin kishirruwan ki ko? Dariya ta sheke dashi kafin tace"Sha kuruminka Gani A main gate dinku an hanani Shigowa.."Yana jin haka ya mike yana washe baki yace"Karki wani damu bari nayi musu waya.."Yafada yana katse wayan,Chan main gate din ya kira yace Su barta ta Shigo bakuwarsa ne nan da nan ko suka wangale mata get,ta sulala ciki,haka sauran get din suma Tuni Umarni ya ishesu,Tana Shiga ciki dama Tuni tasan Apartment din na Conole Sulaiman,suna chan gaba Sai ansha tafiya akwai dan tazara tsakanin nasu dana su Captain Aliyu,Kuma kowanni gida yana da nombarsa da sunan Sojan dake zaune agidan,sai da tayi gaba kadan da Apartment din Aliyu kafin naga ta tsaya baya ta juya inda naji ta Furta.."Come out..."Tafada kai tsaye.

  Bayan motan naga Wani Saurayi ya Fito yana kara gyara wani bakin kyallen  dake Fuskarsa wanda yake sanye da Riga da wando black and white,Kallonsa tayi kafin tayi pointing din gidan Aliyu tana fadin"Ga gidan chan,Kayi maza kuma kayi komai da lura,and don't forget kada kabari akamaka ko aga Fuskarka saboda nan bariki ne,yana da tsaro sasai so u better Carefully kaji ko"gyada mata kai yayi yana fadin"Karki wani damu aikina ne fa,Glass din Fuskarta ta gyara kafin tace"Ok lokacinka yafara daga yanzu.."Tana fadar haka ya bude murfin mota ya Fito yana kalle kalle,lekowa tayi tana fadin"Daka tabbatar da ya ganka,kayi hanzarin Fitowa kabi nan hanyar Da zanbi zaka ga nayi parking din motata,zan barmaka abude sai ka bude ka shiga kana Fitowa kayi min text yadda zan Fito da hanzari, kayi kamar yadda muka Shigo kagane..? kai ya gyada mata kafin ta kada kai ta Figi motar da gudu,shiko sai da yadan tsaya yana kallon gefe ganin wasu sojoji zasu Wuce sai da suka wuce ya juya yaga Babu mai kallanshi kana ya Tunkari gidan Aliyu,Yana zuwa yaga Sunanshi Manne jikin kofar Wajen,ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Fito da key daga aljihunsa wanda aka kera da karfe,ya saka yana juyashi sai ga kofa ya bude hamdala yayi kafin ya waiga yaga bamai kallonsa salaf salaf,ya Shigo falon ya maida kofar yadan Tura yadda bazata Rufe ba.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now