ALIYU GADANGA..!

2.4K 133 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*I DASH D WHOLE PAGE 4 U INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION..😘Son So Fisabillahi*👄😍💞

      *Chapter 31*

     ""Koda Sarkin gida ya isa Fada ya sanar da waziri sakon maimartaba da hanzari ya mike ya isa zuwa ga Sarki,inda maimartaba yake Shaida masa ashiryamsa jirgin masaurata shida duka iyalansa Tafiyan ta mussaman ne,shiyasa zai Tafi da Sarkin gida,Da shamaki,shi waziri zai zauna ya maye gurbin sarki saboda adokar Gidan Sarauta ba"a barin Fada babu wani Shugaba,Sarki baiyi wani Nauyi baki yafara warwarema waziri kadan daga cikin lbrin Abunda zai kaishi Nageria,Mamaki yakama Waziri Kiran Sunan Allah kawai yake yana Fadin"Ammh Allah yasakama ka Ranka yadade,domin sun cutar dakai babu Shakka Sihirin dasukayimaka babba ne mai daukan Lokaci mai Tswao bai saki mutum ba..".
 

Mirmishi maimartaba yayi kafin yace!"Koma miye sun ma kansu waziri,yanzu bagashi Allah ya warware komai,ka hanzarta so nakeyi ayi komai da hanzari,gobe Tun safe mu kama hanya.."Gyada kai Waziri yayi kafin ya mike yana Fadin"Angama Ranka ya dade.."Ya fice yana gyara zaman Rawanin kanshi,daganan Maimartaba cikin gida yakoma,Ummah yafara gayama cewa Ta Shirya gobe zasu Tafi Nageria,koda yagama Matan nasa Gimbiya Razeenah ce kadai Da ya'yanta suka Nuna murnansu Afili itako Gimbiya Fasilatu Ranta baiso ba bata da yadda zatayi kawai tayi Shuru ammh datana da iko datace bazata ba,Gimbiya Razeenah ita ta umarci Jakadiya data sanya bayin barayin Ummah mai babban daki dasu Shiryamata kayanta,sai takoma shashen ya"yan nata ta umarcin Shugaban bayin nasu data Zabi wadanda zasu Shirya musu kayansu dakuma bayi guda uku dazasu Tafi dasu,jiki na rawa shugabam bayi Uwani ta shiga Shashen bayi tana bawa kowa umarnin kowa yatafi barayin da zata turashi yin aiki,ita dai gimbiya Fasilatu sai da taga Fada ta rude da Shirye Shiryen Tafiyar maimartaba Nageria agobe ne yasa Ta Umarcin bayinta da suhada mata kayanta,kuma ta zabi bayi har biyu wadanda zata Tafi dasu,kaji hadama😜Tun adaren Sarkin gida yayi waya zuwa Fadar Shugaban kasan Nageria ya da sakon maimartaba,kana yayi waya zuwa Fadar maimartaba Sarkin gombe ya Shaidamusu zuwan maimartaba agoben,Jirgin Masaurata aka Shirya za"a tafi dashi,domin ababbar Masarautar ta Tambari buzu akwai jirage kama da Aeroplane da Helicopter,Kowane An Rubutamai *TAMBARI BUZU PALACE* Toh daga daya daga ciki aka Shirya tafiyan Kuma duka matuka Jiragen suna da kwalinsu na kammallah babbar mkranta amtsayin pilot,wato dai Sun karancin Abun kenan.

   _________________

Kawu da wannan lbrin ya isa gida yadda Ummah ta ganshi yana Fara"a tasan akwai Abunda yafaru,bai tsayama amsa sannu da zuwan datakemai ba yashiga kwararamata lbrin Abunda ya faru,tagumi Ummah ta saka tana kallon Kawu bala,tana jin Abun kamar al"amara,lokacin dayake Fadamata Mahaifin gadangan yanzu Sarki ne,garin Agadez,mikewa Ummah tayi ta saka hannu bisa hanci tana Sakin guda harda rawa da juya tana Fadin"Allahu akabar Suwaiba Matar sarki dole mu kiraki gimbiya,Shikuma gadanga yazama yarima Allah yakaimu wannan Masarauta muma mu nuna tamu Rawar..."Tafada tana dariya kawu kallonta kawai yake yana girgiza kai,bai Fadamata zuwan Maimartaba din sai da yaga ta natsu kana ya sanar da ita gobe Maimartaban zai iso gombe,so dukkansu zasu Tafi gombe,ta kira Ya"yanta awaya ta Fadamusu,yanzu Shima zai kira Haisam hardashi ataho,Nan yake Fadamata Goggo batasan Abunda ke Faruwa ta gargadi ya"yanta kada ta kirasu ta Fadamusu su kira goggo taji mganar daga sama,ai Saboda murna goggo ko Sauraransa batayi ba,ta Runtuma daki tan laluban Madina awaya,ita tafara Fesamawa Ihu tasaka tana Fadin"goggo a palace wow..."Take Fada kafin tace"Yaya captain kuma yarima,and kuma Azeema She is now a princesss..."Take Fada tana dariya,Ummah ta Shaida mata sakon Mahaifinsu na Tafiya gombe gobe,tsalle ta saka tana Hango gobe taga yadda za"ayi Rumgumar yaushe gamo Tsakanin goggo da Maimartaba Sarkin Agadez,kafin su yanke sai da ta kwabe kan karta kira goggo,suna gama waya ta kira Mardiya itama ta Shaida mata,Guda mardiya ta saki tana Fadin"Ummah Ashe muma munada jibi da jinin Sarauta no wonder yaya captain keda wasu dabi"un jinin Sarauta ashe itace ke yawo ajikinsa Allah mun gode maka.."Itama din sakon Kawu bala ta sanar da ita,kafin kuma ta kwabe akan kartakira goggo don batasan meke Faruwa ba Tukun,Sun rabu akan yanzu zata kira maigidanta gobe da Safiya ita da yara zasu tanan sai su wuce,tunda ummah ta Shaida musu Mahaifinsu yace suzo gidane,don ajirgi zasu je gomben.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now