ALIYU GADANGA..!

2.1K 115 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 38*

   "Koda suka isa Masarautan, ta dinke babu masaka tsinke,haka aka yayyabe Aliyu da Azeema kamar za"a cinyesu saboda murna da Farinciki,Triple ko sunsha dauka sai da Gimbiya Razeenah ta daukesu ita da Azeema kwacokam zuwa shashenta,inda ta sanya Jakadiya ta saka wata baiwa ta saka mata katuwar gawar da Ruwan zafi ta shiga da Azeema tiolet ta gasata dakyau sosai ita kuma Baba Ade ta wanke yaran tas,aka Shiryasu cikin kayan sanyi masu kyau,aka kaima maimartaba su,shida kawu suka daukesu suka sanya musu albarka,shiko Aliyu bayan gaishe gaishe shashensa ya wuce,shida amininnasa,yasamu yayi wanka yaci abinci ya kwanta domin Hutu,suko Su Zafira da Safaru,suna dawowa goggo ta damkama Anty madina su tace  amanar gyarasu na hannunta nan da nan ko tashige dasu Shashen goggo chan kurya domin cika Umarnin goggo,Ummah ko ita dasu gimbiya Fasilatu suna Shashen Azeema suna zaune suna hira cike da Farinciki da Annushuwa,Azeema kuwa tana gama cin abinci suka kulleta cikin daki wai ta kwanta ta huta,tana kwanciya kuma sai barci.

Tako'ina masarauta ta dinke da jama"a daga mabambanta wajeje a kasar Niger,dama kewayanta harda mutanen wasu yanki,domin samun damar amsa gayyatan Da maigirma Sarkin Agadez yayima jama"a na Murna haihuwar jokokinsa har guda uku,tare da Daura Aure tilon ya"yan nasa guda biyu,dole Abun ya Wuce hasashenmu,domin fa ashirya taro ne na azo agani,Hatta da Mallam lawal da Inna Ramatu sai da maimartaba yasaka akayi visa suka taho,domin yace har abada inna Ramatu tana mtsayin mahaifiya ne ga Azeema,sai ga Inna Ramatu zaune cikin masaraurar Tambari buzu rike da ya'yan Azeema,lalle duniya Abun tsoroce kuma hausawa na Fadin Abunda yabaka Dariya watarana Shizai sanya ka kuka,Sai kuma alokacin Aliyu ke jin lbrin Rasuwar Azeeza yaji ba dadi,ammh baiwani nuna damuwarsa ba,kawai yayi jim ne,saboda kada Azeema tace yana murna da Rasuwar yar"uwanta,ammh harga Allah ya manta da wata hallita Azeeza,Fatan dacewa wajen Allah yayimata,ammh akasan Ransa Yana fadin an rage mugun iri.

  Daga Nageria Aliyu ya samu waya dadama,ciki harda waya daga Babban headquater su na Abuja,sukayimai ya jiki,bayan nan ya samu waya daga abokan aikinsa dadama,cikin wayar data tsayamai arai itace wayar da Ni"ima tayimai tana kuka,tace tayita nemansa so ba adadi bata sameshi ba sai yanzu,tadamu sosai Allah yasa ya warke babu Abunda ke damunsa,Mirmishi kawai yayi mata kafin ya sanar da ita ya warke yanzu hakama yana Masarauta nan yake sanar da ita haihuwan Azeema,da kuma Aurensu Jabir,Ni"ima taji hawaye sun taho mata tayi Saurin dannewa tana fadin!"Allah ya raya su bisa sunnah Congratulation,"Lokacin datake Fadin haka yana jinta kuka takeyi,sai ya basar yana tambayanta yakamata su Fito da miji ita da muneera Suyi Aure saboda Shine mutumcinsu,Dariyan kuka Ni"ima tayi kafin tace"Muneera zatayi Aure in Allah ya bata miji na gari,mgana na kuma bata don bazan taba yarda na auri wani namiji ba sai mutum daya,in ban sameshi ba,sai da nakoma ga Allah banyi Aure ba.."Saurin katse kiran tayi tana Fashewa da kuka,Aliyu Tunda sukayi waya da Ni'ima ya koma wani Sukuku ranar,saboda kalaman Ni"ima,hakika in yace bayason Ni"ima yayi karya,kuma in yace baya tsausayinta tabbas yasan karya yakeyi,kawai Shi ra"ayin Aurenta ne bayayi,saboda Shi mutum ne,mai zuciya da tsayawa kan Ra"ayinsa tunda yarasa Ni'ima da Farko komai na plan din Aurenta ya Rushe,sai gashi Azeema dabaitaba tsara Rayuwa da ita tazo tazama kaddaransa,gashi yau an wayi gari bayan goggo bai da wata sanyin idaniya daya Wuce Azeema yanamata Sonda baisan iyakarsa ba,saboda kirkinta da sadaukarwanta gareshi,hakadai yayita tunane Tunane har ya kareta baisamu mafita ba.

Ranar Da Azeema ta cika Sati biyu da haihuwa da misalin karfe 10:00am na safiyar Ranar jumma"a Duban mutane da sarakai,suka Shaida auren Haisam da Safaratu sai Jabir da Zafira kan sadaki mafi daraja, afarfajiyar Fadar maimartaba Sarkin Agadez Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,Daurin Auren daya amsa sunansa,wanda ba"a tabayi ba masarauta tacika makil da yan gida da yan waje,busan algaita kadai kakeji da kade kade da raye raye na Masarauta,abinci ko tako"ina kawai afitowa dashi ake,daga cikin masarauta kuma Yau din ne ake Sunan Triples,wadanda suka ci Sunaye masu daraja Daya taci Sunan goggo SUWAIBA ,Dayan kuma FATIMA,Sai Namijin yaci Sunan Maimartaba wato ABDULNASEER,Wanda ada sunan kawu akaso yace,kawun da kanshi yace maimartaba yafishi chanchantan samun takwara da farko,shima inda rai da rabo,mai sunanshi na zuwa,sunsha wanka cikin kayan alfarma,suda Mahaifiyarsu Azeema,wacce ke sanye cikin wani leshi,mai tsada da yarari,kunnuwanta da hannuwanta gabadaya Sanye da zinarai suna daukan ido,Hakama ango karni sanye da shadda fara riga da wondo harda babban Riga Shida aminan nasa,guda biyu duka shiga iri daya sukayi harda cikon Umar na Hudunsu,Ana gama Daura auren suka nufa shashen Aliyu suka gudanar da wata yar kwakwaryan walima,bayan la"asar nayi aka Fito akayi wata kayatattacan kilasa,mai ban Sha"awa Da dadin kallo,haka duka zaratan maza su hudu ke bama doki wuta sunajan limzami,kowa da kowa yafito kallo,harda maimartaba,Amare ma suna gefe,kowacce ita tarike ma mijinta limzaminsa kafin afara kilasan,Hakama Azeema tayima Aliyu gadangan kusar yaki,daga karshe maimartaba da tawagansa suka Rufe kilasa,yau hatta da kawu Bala Da mallam lawal da sun hau dokuna,Atawagan Sarki,itako inna Ramatu Tunda sukazo take Shashen Azeema ta karbi su Ummah ita ke kula da ita da Triple,Tayi nadama sosai in kuka ganta kamar ba ita ba,Abun jin dadinta ma babu wanda ya riketa da Abunda ta aikata kowa amasarautar yana bata girma amatsayinta na Uwa ga Azeema,Gadanga ne dai haryanzu bai saki da ita sosai ba,don shi mutum ne mai Ra"ayin bala'in in baya Ra"ayinka Tun Farko Abu ne mai Wahala yayi Ra"ayinka daga baya,kawai mazayewa yake saboda Uwar mata Azeema,don ya lura Tunda ta haihu takoma masifaffa,mgana kadan sai ta hau Fushi,shiko yanzu Aduniya in akwai Abunda ya tsana to yaga Fushi Afukar pretty yanzu nan zai Rasa natsuwarsa,shiyasa in gaya su Jabir na Rawan kafa kan su Zafira mamaki suke bashi,dariya kawai yake Aransa yana Fadin"Yarinta haryanzu na damun su Jabir,Allah ya kaunda Fitina,tunda daga su Jabir din har Su zafira shegen Rawan kan tsiya😂

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now