ALIYU GADANGA..

2.1K 114 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*Dedicated to UMAIMA ALIYU...Tanque dear for ur Wonderful Comments*

        *Chapter 17*

   """Washegari da duku duku goggo tagama Shiryama Azeema duka kayanta ta sakata tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai Ruwan Kasa da zanen fulawan brown ajikinsa sai Farin hijabinta data sanya wanda ya wuce gwiwanta da kadan,goggo na cikin Shiryamata Sauran kayan nata cikin babban akwatinta wacce ta siyamata gadanga ya tarar dasu cikin daki Shima cikin Shirinsa na Riga da wando,rigar light blue ne,sai wandon baki ne,kafarsa sanye cikin wani takalmi mai Rufi baki kansa kuwa sanye da hula p-cap sai wata katuwar jakar bayansa,wacce take rataye abayansa kallo daya zakamai ka fahimci ya mallaki dukkan zati da jarumta goggo na ganinshi tace"Badai wai har ka Fito ba gadanga..? rausayar dakai yayi kafin ya tsugguna yana gaisheta amsawa tayi tana fadin"Kwa tsaya ku karya ko gadanga,kuma sai ka biya da ita tayima kakarta sallama,tunda tafiyace ba yau za"a dawo ba,kuma ba gobe,ko saboda halin Rayuwa.

  Mikewa gadanga yayi kafin yace"Goggo na yanke wata shawara,kawai kema ki Shirya naki kayan mutafi tare dake da Baba Aden da ita Azeemar,yanzu nagama ma Baba bayanin Allah barshi in zamu tafi tashiga tayimai sallama koya kika gani? Dan jim goggo tayi tana kallon Azeema wacce ke zaune gefen gado tayi Rau rau dab ido kada kai tayi kafin tace,,"Eh kuma kaima kace wani Abu bai kamata Azeemar takai kanta ita kadai ba,bari na Shirya sai mu biya mu dauki Baba Aden nasan ba mtsala me ko kawunka zaiji dadin ganina kullum mukayi waya sun dingamin dan kida kenan Shida Umaimah.."Mirmishi Gadanga yayi kafin yace",Kema goggo kin nacema gombe nan kamar wani ya kafeki ciki kodai kodai.."Keyarsa ta maka da Rigar dake hannunta tana fadin"Kodai me,Ja"iri Fita falo kajiramu gamunan zuwa Dan kawai.."Dariya yayi yana fadin"Allah baki hakuri goggon Gadanga,ai ni babban burina shine mutafi bariki tare muyi zamanmu mu uku na tabbata Azeemar taki zata fi jin dadin zama sosai.."Kallon Azeema Goggo tayi sukayi mirmishi atare kada kai goggo tayi tana fadin"Allah ya shiryamin kai gadanga.."Take fada tana mirmishi ita kadai.

Cikin lokaci goggo tagama hada nata kayan dama tayi wanka karyawa kadai sukayi suka kulle ko"ina suka Fito Aliyu shiya kwashi akwatun yasaka amota bayan ya Fito da motar daga gareji,goggo da kanta ta tasa Azeema zuwa cikin gidansu,domin tayi bankwana da mahaifinta koda suka Shiga cikin gidan suna sallama,ba wanda ya leko sai mallam lawal,din nan fa yatasa Azeema yana ta mata Nasiha sosai tare da horar da ita hakuri da kuma yin biyayyah ga mijinta daga karshe ya dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka Azeema yakuma albarkaci Aurenku keda Aliyu ya kareku da dukkan sharri,Allah ya kade Dukkan Fitina atsakaninku yakuma baku zuru"a dayyaba tashi kuje Allah ya tsare hanya yakuma kaiku lafiya.."Da Amin take amsawa tana kuka sosai hawayenta na shatata wanda ita kanta goggo sai da tayi kwallah Sun mike zasu Fita Azeema ta waiga kofar dakin Inna Ramatu wacce ke tsaye ta Fito ganin Abunda ke faruwa,ganin ta waigo sai tayi Saurin sakar labule ta koma,kada kai tayi sai kuma idonta karaf kan dakin dasuke kwana ida da Azeeza nan ta hango jikin window dakin tana hawaye,Kallon ido cikin ido sukema juna kowacce da Abunda take sakawa Aranta kafin Azeema tajuya tana share kwallah tabi bayan goggo suka fice tana ma gidan wani kallo mai kama dana karshe.

Suna Fitowa ko ganin Azeema tana kuka baisa gadanga ya tambayi ba"asi ba,suka Shiga mota suka nufi gidan Baba Ade,ko da suka shiga cikin gida Goggo ta koramata jawabi,baba Ade guda ta saki tana korama gadanga Albarka tare da Fatan Nasara bata ta bata wani lokaci ba tashiga ciki ta gyara jikinta ta dauko yan kayanta kala biyu ta rufo dakinta tama matar datasa haya agidan makulli suka fito suka Shiga mota,Dakyar Azeema ta yarda ta shiga gaba sai da goggo tamata ta jan ido kana,Shiko Aliyu kalloma Azeemar bata isheshi ba,don mganar gaskiya haushinta haryanzu bai gama sakinsa ba,sakamakon goggo na motar gadanga bai samu damar shararan gudu kamar yadda ya saba basu iso kaduna ba sai after 3:00pm na Rana,kai tsaye anguwan Rimi ya isa dasu wato gidan kawu bala kenan,wani makeken gida mai kama da aljanar Duniya ga security nan tako"ina agidan yadda kukasan gidan wani gwamna ko mataimaki,motoci kuwa baka iya kirga iyakarsu aharabar gidan,bazata ka taba kallon goggo da gadanga kayi Tunanin suna da dan"uwa mai tarin dukiya da mtsayin irin haka ba,duba da inda ita kanta goggo ke rayuwa ammh ko ajikinta donta Fi son gombe Fiye da shigowarta kaduna,don ko banza tanajin kamshi zaria in ta shigota Shiyasa bata kaunar nesa da gombe don koba komai goggo tace garin Shiya Rufamata asirin lokaci da garin na zaria suka nemi su tona mata.

ALIYU GADANGAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant