ALIYU GADANGA..!

2.3K 112 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_* Oh ni Jikar Fati😿Gabadaya yau ba"a barni nayi barcin Safe ba,gabadaya Anki barina nayi Sukuni ko"ina naje GADANGA..GADANGA...Toh gashinan Dai kada asamu masu cinyeni danya ban gasu ba😂 Nasan in ban sakoshiba,Akwai masu zuwa har zaria sucini Tara,irinsu TEAM AZEEMAR GADANGA😘Happy Lahadi day😂😜Asha karatu lafiya Masoyan kwarai*_💞💖

   *Chapter 30..*

    ""Gimbiya Fasilatu ta kira likitan mai martaba Tasanar dashi ko mintigoma  baiyi ba, ya iso masauratar,kai tsaye akayi mishi iso shashen maimartaba,koda ya isa ya iske maimartaba nata sambatu yana kiran Sunan Suwaiba,bai bata lokaci ba ya nemi da su Ummah su bashi wajen don yasamu damar gudanar da aikinshi,suna Fita ya karisa gamai maimartaba wanda ke zaune yayi Tagumi yana Ta so kwalkwalwarsa Ta tunamai Sauran Abubuwa ammh Abu yaci Tura,Likitan baiyi mgana ba,illah bude akwatin kayan aikinsa ya Fito da allurai ya harda harda ya juye a Siriji yayi mai martaba ita,wanda ko minti biyar bai karaba ya sulale yana barci,koda likitan ya Fito baice masu Ummah komai ba,illah sanar dasu dayayi"Da zaran ya Farka zai Dawo daidai Ranki Shi dade.."Sallama sukayi yatafi wanda dama Likitan Shima zuru"ar Mairtaba tsohon sarki ne,da yake ga Sarki Abdulnasser din.

Har garin Allah yawaye maimartaba Bai Farka ba,yana ta barcinsa Hankalinsa kwance,Tuni lbrin ya ishi kunnen sauran iyalansa da kuma Shamaki tare da waziri da galadima,su suka sanar da Fada  cewa sarki bazai samu zama ba yau sakamakon baitashi da jin dadin jikinsa,Fatan samun sauki akayimai sai Waziri ya Karbi sarki Aranar aka cigaba da gudanar da Mulkin.

   *********************

Suna Shiga cikin gidan Aliyu,suka zazzauna,Aliyu bakinsa yaki Rufuwa saboda murna wayarsa yazaro yana Fadin"Dude ni nama Rasa wazan Fara kira goggo ko kawu? yafada yana Danna wayar dariya Jabir yayi kafin yace"kira kawu first shine ke kusa goggo kuma,in son samu ne ayimata Big Suprise kawai..."Dariya sukayi gabadaya.

Umar yace"Nikuma sai komai ya kammallah zan kira video call na hadaka da maimartaba nagani ko yaya zaiyi..? Shuru Aliyu yayi yana mirmishi daidai lokacin da Kawu ya daga kiransa yana Fadin"Aliyu Gadanga ya"akayi ne? Bakinsa duka abude yace"Kawu yau Allah ya gwadamin dan"uwa na,kawu yau  naji lbrin dangina,Ashe nima Da"ne kamar kowa ina da uba da yan"uwa da kanne da yayye.."Yafada idonsa na cikowa Da kwallah.

Kawu Bala dake zaune a office yayi Saurin mikewa yana Fadin"Aliyu are u Serious....? Da hanzari yace"Wlh kuwa kawu kazo barrak dinmu yanzu kaga wani Abun mamaki.."Kawu bai jira cewarsa ba ya datse kiran,alokacin yana da tattaunawa da yan jaridu,ammh ya tsallake Shida tawaganshi Suka Shisshiga mota sai bariki,tun amota yake addu"a Allah yasa Abunda Aliyu yafadamai da gaskene.

Aliyu najin karar Jiniyar motocin Kawu ya Fito da gudu,baima jira yakai ga Fitowa ba ya bude mota ya Riko hannunsa yana fadin",Taho kawu kaga wani abu.."Yafada yana Jansa zuwa cikin gidan,da hanzari ya Bishi yana kara saba babbar rigarsa Suna shiga cikin Falon kawu yaci karo da Umar zaune yana mai mirmishi Zaro ido kawu yayi yana bin Umar din da kallo,Kafin kuma yakoma yana bin Aliyun da kallo,Kawu yayi tsaye kafin ya Durkushe kasa kawai yana Fadin"Sarki ya tabbata ga Allah Shugaban kowa da kowa.."Yafada yana kai goshinshi kasa yadade kafin ya dago,koda yadago hawaye ne sharkaf bisa Fuskarsa,Aliyu ne yadagosa yana Fadin"Kaima kayi kuka ko kawu,wlh nima nayi,banta zaton zan yi Farinciki irin na yau ba,kawu kaga kamana dashi ko,kuma muna using da Surname iri daya His Name is Umar Abdulnaseer Tambari buzu..."Hannunsa Kawu ya riko ya karisa ga Umar yariko hannunsa ya hada dana gadanga yana Fadin"Ka sanar dani wani Abu game da mahaifinku Shin Abdulnaseer na raye acikin Duniyar nan"?Mikewa Umar yayi yana Fadin"Tabbas Maimartaba na Raye,ammh kuma yana rayuwa da mafarkin dakuma damuwarku,koda da darana daya Abbah bai taba Fidda rai da Allah zai bayyanamai Sirrin boye ba.."Ido Kawu ya zaro yana Fadin"Naji kace maimartaba kuma? dariya Umar yayi kafin yace"Eh Shine Sarkin dake mulkan *MASARAUTAR TAMBARI BUZU DAKE YANKIN AGADEZ..* Baya kawu yaja yana Fadin"Allah mai hikima da kari,babu wanda ke tsarawa kuma ya zartar lokaci daya sai Ubangiji.."Ya fada yana jinjina kai,kafin ya zauna sukoma suka sakashi atsakiya Kawu ya kalli Umar yace"Kabani wani lbri game da Abdulnaseer...'Nan Fa Umar ya basu lbrin Abunda ya sani game da mafarkin da maimartaba keyi,dakuma fadamai dayayi yayi Rayuwa A nageria ammh bazai iya Tuna awani gari bane,ako awani yanki bane,Shidai lokacin da Hankalinsa ya dawo ya Tsinci kansa ne awani gari,ammh kuma har mutumin daya taimakamai ya kawoshi har masarautarsu bai fadamai awani gari bane alokacin,ammh kullum cikin mafarkin wata mata da Danta yake,suna ahalin neman Taimakonsa..."

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now