ALIYU GADANGA..

1.9K 100 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *Chapter 36*

  "Washegari Sojojin suka yima Dajin Sambisa tsinke,wannan karon harda manyansu atare, dasu bayan su Umar da Jabir da Sauran wasu jajiratattun Sojojin,Ta jirage ne wadanda ke da Na"irorin Daukan Hoto ta kasa,ma"aikatan dake cikin Helecopter din suna ganin duk wasu kananan Abubuwan dake cikin dajin,ta Na"urorinsu,cikin ikon Allah suka tarar da wani sansani na yan boko haram din acikin chan kuryan Daji,Umarnin yin kasa akabama Jiragen bayan kowani Soja ya saka rigar iska,sun Fara sulalo wa kasa,Mamaya suka yi musu ba Shiri kawai sai dai sukaji tashin harbi kokafin su Fito da Makamansu sunyi musu kwanya harbi kota ko"ina domin Sojojin suna dayawa Suma,nan Fa akaita bata kashi har na tsawon Mintina Talatim kafin sojojin su samu Nasarar kashe wasu ammh duk da haka akwai wadanda suka kara Nausawa dajin,suma acikin Sojojin an samu Wadanda suka Raunata,ammh ba!a samu rasuwar rai ba,nan da nan suka kafa sansani bayan an Fitar da masu Rauninka likitocin cikinsu na basu Taimakon gaggawa.

Cikin katon sansaninsu da Sojoji sukayi watsawatsa dashi aka gano Sauran Sojoji 8 daga cikin wadanda suka bace,suna  daure dukkansu da kacha,duk sun rame sun lalace,dukkansu babu riga ajikinsu,ko"ina tabon bulalane da sara alamar dai Suna cikin wata rayuwa,cikin azama aka kwance su aka daukesu zuwa sansanin sojojin domin basu Taimakon gaggawa Major Sadeeq Amfani ne ke Fadin!where iz Captain Aliyu Naseer..'?yake Fada Ahankalinshi take,sai alokacin Sauran Sojojin suka Fahimci babu Aliyu aciki,nan fa hankalu suka Tashi nan da nan akace su Jabir su sake bazama cikin dajin domin sake dubawa kila a dace su ganshi.

Aikuwa hakane ta Faru basuyi nisa ba,suka iske wani sansanin ammh babu kowa aciki,koda suka Farma wajen sai suka tarar da wani mutum Daure daga saman hannayensa da kasa ma an Dauremai kafafu,Shibai kai tsakiya ba,shikuma bai sauko kasa ba,kansa na sunkuye ne jina na zuba ta hanci ta baki,bayan Kafarsa ta dama daure da wani kyalle,ammh haka jini ke zuba awajen,gashi ta kumbura,Tsaye sukayi cak suna bin Mutumin da kallo,Abu daya yasa su ka gane wannan nasu ne,wandon Sojan Nagerian dake jikinsa,wanda yachanza kala saboda jini,Jabir daje tsaye yayi kukan kura yana Fadin"Dude...."Yafada da duka muryansa bude,wanda harsaida Dajin ya amsa,hatta sauran Sojojin dake baya da suka ji suka Biyosu aguje dauke da makamai.

Umar najin haka ya karisa garesa suka rikosa baya Numfashi alamar ma Asume yake,wasu daga cikin Sojojin suka fara Zagaya wajen suna dube dube,wasu kuma suka isa wajen suna kokarin kwance Aliyu,awurin kwancensa ne suka Fahimci yana da karaya biyu Akafadansa ta
dama,bayan kafarsa ta dama ta Dauke da harbin bindiga,ammh an cire harsashinsa,sai kafarsa ta hagu itama tana Dauke da karaya,sai wasu kananun gocewar kashi,kuka reras Su Umar keyi na tsausayin Halin da Aliyu ke ciki,haka suka Daukosa ko"ina na jikinsa ya saki kamar gawa,suna Fito dashi manya sojojin suka karisa garesu da hanzari Jabir ne yake sanar dasu irin Rauninka dake jikinshi,nan da nan Major Sadeeq  Amfani yasa su Jabir da Sauran Sojojin su cikon 8 din da kuma wadanda suka jiggata su shiga jirgi tare da Likitocin cikinsu su koma chan Asbitin Federal Ta Abuja,domin basu Taimakon gaggawa,su in sungama tararra komai zasu zo daga baya.

Cikin kankani lokaci aka sakasu cikin jirgin suka lula sararin samaniya,tun acikin jirgin Likitocin sojojin ke bama Aliyu taimakom gaggawa,ammh har zuwa lokacin bai farfado ba,sun dai samu daman warware kafar data keda harbi sukayimata dressing kafin su isa Abuja,shiko Chaif Amry of Staff tun suna chan lbrin ya sameshi cewa an ganosu,nan da nan suka sanar da kafafen yada labarai na Gano wadandan Sojojin dasuka bata ayayin kwantar da tarzoma agarin na maisuguri.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now