ALIYU GADANGA..!

1.9K 114 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*O Allah, You are the only supreme being worthy of worship, We associate no partners with You and only from You alone we seek for Guidance, Protection and Forgiveness for our sins. Ya Allah save us from the Darkness and Loneliness of the Grave, from the Torments of Hell Fire and finally make Jannatul Firdaus our final abode, Amin. Juma'at Mubarak!*

      *Chapter 35*

   "Koda Su Aliyu suka isa barrak,sun tararda angama dukkan Training din da za"ayi har anfara Tura sojoji zuwa yanki da ake tashin hankali domin kwantar da tarzoma,suma din sai da suka nemi izini,kafin abarsu su Tafi suna dawowa babu wani tsaiko aka Turasu kowane da bacth dinshi Captain Aliyu An hadashi da wasu sojojin Cameron ne zuwa Maiduguri  ayayinda Jabir aka Hadasu da sojojin Chadi,zuwa yobe,shikuma Umar da Sojojin Nageria aka hadasa zuwa Kaduna adajin nan na birnin gwari ma"ana dogon dawa,babu wanda aka hadashi da wanda yasani Tafiya ce ta taimakon kasa da kasa saboda haka babu gudu babu ja da baya,kwana daya sukayi kafin suyi sallama da junasu kowannesu yabi tawagarsu suKa dauki hanya,Dukkansu kowani yatafi da niyar Taimakon kasarsane,dakuma Matakinsa na soja da kuma alqawarin da suka dauka na kare kasa da al'ummah dake cikinta,barikin gabadaya tayi rakwa rakwa gabadaya Rabi da kwatanta duk basu sai wadanda ba"a rasa ba sudin kuma sun kasance suna kasa ne,sosai basu gama sanin wasu dabarun yakin ba.

Ko kafin kace me,Kafafen yada lbrai sun watsa wannan lbrin na Tafiyan wadanan sojojin tare da rokon yan Nageria da su mika godiyarsu ga Kasar Niger da cameron hade da chadi bisa kokarin kawo musu zaman lafiya da tsaro akasarmu ta nageria,haka Aka dinga nuna hotunansu tare da tawagar kowanne,ciki ne da kuma rokon barar addu"ansu garesu na Allah ya basu Nasara suje lafiya su dawo lafiya,Ni"ima taga gwarzonta harda kuka sai da tayi tana mai Addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya nan tayi alkawarin duk sallarta sai ta sanyashi ciki,dukkansu sojojin babu wanda yatafi da wata waya ahannunsa sai dai wayar tsaro,wanda zasu dinga mgana da junansu in wani abu yafaru,ko kuma su kira bariki in suna bukatar wani Taimako.

***************

Inna Ramatu da Mallam lawal sun tattara sun koma gidan goggo da zama Duniya sabuwa mai tattare da Farinciki,Inna Ramatu in ta tuna Abunda tayi ta aikatawa ga goggo da Aliyu sai taji kunyan gashi yau tana raban Arzikinsu,Azeeza kuwa bata kowa take ba,sai ta kanta domin Jikinta gabadaya ya rikice shiyasa iyayan nata suka kwasheta suka kaita general hopital inda nan take aka bata gado,tare da wasu gwagwaje,sai gashi gwajin farko angano Azeeza ta dauke da hawan jini,kuma jininta yayi mugun hawa sakamakon ta sakama kanta damuwa,toh tayama Azeeza bazata damu ba,tabiyema Sharrin Shedan da Duniya gabadaya,Sai daga baya take ta Nadama da Danasani,da"ace tayi yaki da zuciyarta bata biyema Rudin Duniya ba da yanzu bata cikin wannan Halin koda Allah bai yayemata soyayyar Yaya captain ba,toh zai yayemata kaso mafi yawa acikinta,kila ma harta samu miji gangariya tayi aurenta bayan tana zaune lafiya da yar"uwarta mai Sonta Adda Azeema,gashi yanzu komai ya lalace duk Burinta babu wanda ya tabbata,Tun Aduniya tafara ganin ishararta inga Randa muka tashi gaban ubangijinmu,ayanzu haka Azeeza tafi kaunar Mutuwa fiye dakomai domin Tasan kotarayu babu amfani ga Rayuwarta domin hatta mahaifinta ya tsaneta,kuma da wani ido zata cigaba da kallon mutane bayan Duniya tagama sanin Duk Abunda ta aikata.

Ammh duka wannan halin data Shiga batabama kowa laifi ba,sai Mahaifiyarta Inna Ramatu,don Tun tasowarta inna bata taba kwabanta ba akan tayi ba daidai ba,kullum goyon bayanta take,koda Abun nan kuwa bamai kyau bane,Inna zata mara mata baya,bata taba koda zaginta domin gyaran Tarbiyanta ba,duk halin data Shiga ayau inna ce Sila domin Baba yana iya bakin kokarinshi wajen basu tarbiya,ammh sakamakon Inna ramatu ya isa gabadaya bata ganin Baba da mutumci,duba Adda Azeema bata da uwa,ammh kalli irin kyawawan dabi"unta da kuma hakurinta da sanyin Halin ta,ammh ita datake uwa ammh bata mori kowanni hali ba sai na mugunta,lalle Rashin Tarbiyama ma wani babban ginshikine sosai ga rayuwa yayanmu na yau da kullum.

ALIYU GADANGANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ