ALIYU GADANGA..!

2.3K 131 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*NOT EDITED*💥

        *Chapter 11*

  """Goggo na cikin kichen taji Sallaman Azeema,da hanzari ta fito tana fadin"Ah Azeema,kice kamar daga sama da daddaren nan? Tafada tana kallonta,Sunkuyar dakai Azeema tayi tana kokarin dukawa ta gaida goggon saurin Rikota tayi tana fadin"A"a tashi kada muyi haka dake,bama wannan ba,miye naga kina wani zare ido,gabadaya kamar atsorace kike,gayamin badai wani lalatattace bane ya biyoki yanzu na fita naci ubanshi,kokuma na hadashi da gadanga wlh yaci uwarshi yanzu nan fadamin waye ya biyoki naga kin Shigo  a Tsorace"Dan waro ido Azeema tayi kafin tace"Ba kowa bane fa inna Dama yaya captain ya daki Azeeza saboda tamin Rashin kunya,shine na shigo nan kada na koma gida inna ta huce akaina.."Galala Goggo ta kalleta kan tace"Ai yamin daidai wlh,kema dai Azeema wlh ki kamma jikinki,in dai kina wannan sokanci wlh bazaku Shirya da gadanga ba,shi mutum ne dabayason wargi balle shashanci yo in ma kinaso sace zuciyarsa ne,na baki satan amsa ki zama mace Tukunnah bayan kinkam jikin ki Atoh.."Tafada tana Riko hannunta,Baki Azeema takama tana yar dariya,Mangare mata kai goggo tayi tana fadin"Au dariya na baki ko?yo ai gaskiya ne,ammh wani lokacin in kina wani Abun sai ki dinga Tunamin da Mahaifiyarki Fatima,wlh Azeema yadda kike da hakuri da kawaichi to Fatima ta fiki.."Tafada cikin sanyi,nan da nan idon Azeema ya ciko da hawaye,dafa kanta goggo tayi tana fadin"Karki damu Azeema wlh Tamkar Aliyu haka nake kallonki da izinin lahi sai kin zama Abun alfahari,da kin Tuna da mahaifiyarki karkiyimata kuka kiyi mata addu"a da Fatan tana kyakyawan mtsayi kinji ko? dakai Azeema ta amsa tana share,kwallah hijabin jikinta goggo ta ciremata bayan ta amshi al"qur'anin tana fadin"Maza shiga shiga ciki ki dauro alwala kizo muyi sallah sai muci abinci yanzu na gamashi da zafinsa,ai ni nagodema ja"irin nan gadanga daya bugemin Mara kunyar yarinyarnan gashi sanadin haka yata tazo wajena,duk da yanzu wasan buya ake dani Tunda Megida yadawo.."Tafada tana kyabe baki,Tura baki Azeema tayi tana fadin"kai goggo ba ina zuwa ba,kuma ni yaushe nace haka.."Goggo tayi yar dariya tana fadin"Au hakane fa,to naji baki ce ba,maza shiga kiyo ki fito an kusa sallame salla daga masallaci.."Tafada tana Ficewa daga Falon,itako Azeema dan mirmishi tayi kafin tafada bedroom din na inna wanda in ka gansa ko na wata amarya albarka saboda yadda yasha wani ubansu royal bed mai kyau da tsari gashi yana malale da capet mai kyau da tsari,da makeken wardrope dinta sai madubinta dake shake da kayan shafa na mata,wanda goggo banda kwalli bata shafa komai,ammh kullum taramata Ali gadanga yake,Tunda kawu ya daukemata Nauyin komai.

Tare sukayi jam"i da goggo suna gamawa goggo ta zubomusu abinci Shinkafa da miya sai slat datayi musu goggo fa,ba baya ba,akwai iya girki sosai kamar ka tsinke hannu,nan suka zauna Dole tasa Azeema sakin jiki don goggo dai kun santa dole ma mutum ya saki jiki da ita,da farko Azeemar kin ci tayi,aiko goggo tayimata barazana da zata kira Aliyu yanzu yazo yayimata dure,kila taci jin haka yasa taba goggo hakuri ta hau cin abinci dama yunwa takeji sosai domin tun karin safe rabonta da Abinci,Ammh tanayi tana waige da sauraran waje kada Yaya captain yazo ya Ritsata.

  Itako Azeeza tana shiga gida da ihu Ta iske mallam lawal atsakar gida shida Inna Ramatu,jin ta shigo da ihu yasa Inna mikewa tana fadin"Ke lafiyanki kuwa keda wane.."gabansu Azeeza ta zube tana fadin"Inna wlh In baki dauki mataki kan Adda Azeema ba,ni zan dauka dakaina.."Tafada tana hawaye,wanda bana zafin marin da yaya captain yayimata bane,a"a takaichi yadda taga kamar yana tsausayin Azeemar ne,wanda ita ba burinta kenan ba,burinta kafin yafara son Azeemar ita ta riga ta mallake zuciyarsa Allah barshi ya dankarama Azeemar sakinta ta kara gaba.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now