ALIYU GADANGA..!

2.3K 112 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

     *Chapter 27*

    Jabir na bin gayen da Aliyu yace yabi, hankalinsa na wajen Tuki yace"wai Dude waye wanan mutumin daka sa nabi bayansa..?Aliyu bai kallesa ba yace"Zakaji ammh sai ya Shiga hannu,kadai kacigaba da binsa kawai.."Ba wanda ya sake mgana,Jabir na biye dashi daidai wajen iyali hospital Yasha kwana baiyi nisa da Tafiya ba,ya tsaya bakin wani karamin gida mai get,yafaka ya sauka bayan ya sagale Hular kwanon bisa mashin din,ya tsallaka yana kokarin Ture wani karamin get dake kofar gidan,motarsu Aliyu takawo wajen ko gama parking Jabir bai yi ba Gadanga ya balle murfin motan,ya dirko ko kafin Jabir yayi mgana Tuni ya tsalle ya dira gaban gayen nan,bai yi wata wata ba ya Shako wuyansa ko kafin ma ya waigo Aliyu yafara sakarmai marika tako"ina Kafin ya saka kafa yayi Shuru dashi yatafi ya Fadi kanshi ya bugi da get,harsaida keyarsa ya fashe yana jini Shafa jinin yayi yana bin gadanga da kallo,Razana yayi,da hanzari yayi kokarin mikewa zai gudu,ammh sai gadanga ya yi hanzari ya Rikosa yana kara zubamai maruka kamar Allah ya aikosa.

Jabir yana gyara parking hankalinsa tashe ganin Abunda gadanga keyi,wayarsa dake cikin aljihunsa ta dauki Tsuwa bai Cirota ba,sai da ya Fito,kana ya dauko wayar yaga bakuwar Nombace kekira,bai dagaba ya maida aljihu ya karisa wajen Aliyu yana fadin!"Dude wai lafiyanka zaka Fa kasheshi,kana Dukanshi ta inda jininsa zai biyone fa.."Yafada yana Riko Aliyu dayake ta Taushin gayen Afuska Tuni har ya hadamai jini da majina,Rikesa yayi dakyau shiko yana Kokarin kwace kansa yana fadin"ka kyaleni Jabir wlh yau sai nayi ajalinsa..",Da hanzari gayen ya ja baya yana zubar da jini ta baki ta hanci a galabaice yake Furta.."kayi..Kayi..Ha..kuri,Turoni akayi...Ma...Matarka bata da sani a kan komai.."Yafada yana Numfashi walala.

  Cak Aliyu yadakata daga son Finzge kansa daga hannun Jabir dayake kokarin yi,da kallo yabi gayen kafin ya durkushe gabansa yana Fadin"Karya kake Makaryaci,in Turoka akayi waya Turoka..? Jabir dake tsaye cike da mamaki harzai yi mgana sai yaji Gayen ya Furta awahale"Ha..Hajiya muneera..."Muneera..? Jabir da Aliyu suka maimata atare kafin su kalli juna,suna mamakin Sunan da sukaji ya ambata,gyada kai yayi kafin ya sanya hannu a aljihu a wahalce ya ciro waya yana danna dannawa kafin ya mikama Aliyu wayar yana fadin"Eh Muneera sunanta,ga hotonta nan,ita tabani aikin,kuma kamar ma itama aikota akayi,don tana waya da wata tana Fadamata yadda akayi,su bukatarsu kawai ka ganni cikin dakin,ammh wlh yadda ka ganni,haka matarka taganni bata da akala da zuwana aiko ni akayi.."Yafada yana dafe hancinsa dake malalan jini.

Matukar Razana Aliyu ya Razana da ganin Hoton Muneera baro baro,Amtsayin wacce ta aiko da kwarto har gidansa na bariki,Jabir ma dake tsaye mamakin ne ya kasheshi,duk da bai wani Fahimci meke Faruwa ba,zai yi mgana kenan,wayarsa takara daukan Tsuwa tsaki yaja yadaga ganin bakuwar nombar dazu bai kai ga yin mgana ba,yaji ance"Don Allah Jabir ka tsaya ka Sauraremu sako zamu baka kafahimtar da Captain don Allah.."Aka Fada murya na Rawa Cikin mamaki yace!"Waye..? tace"Muneera ce ga Ni"ima zatayi mgana dakai,munta kiran wayan captain bai daga ba.."Tafada tana mikama Ni'ima waya Wacce ta amsa tana Fadin"Hello Jabir,..."Tafada tana Hawaye muryanta cikin kuka.

     Jin Muryan Ni"ima yasa Jabir Saurin sanya wayar A speaker, dai dai lokacin da Ni"ima take Raftafama Jabir lbrin duk Abunda yafaru Tundaga zuwansu gombe har haduwarsu da Azeeza da Abun da suka aikata duka sai da tafadama Jabir,Aliyu da Tunda yaga Hoton muneera yashiga wani yanayi,bai Fita ba yaji muryan Ni"ima na koro bayanai,bai tsorata ba sai da Ni"ima tace"Jabir ka sanar da my captain don Allah ya yafemana,wlh bani da niyyar cutar da matarshi Sharrin Shedan ne,da Sharrin Kanwar matarsa Azeeza,kuma ka sanar dashi yayi gagaggawan Daukan mataki akan Azeeza domin tace yanzu Aikinta na gaba Shine ta kashe Azeema.."Afirgice Aliyu ya mike ya warce wayar hannun Jabir yana Fadin"are u Sure Azeeza tace zata kashe Pretty...? yafada da kakkausan murya.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now