ALIYU GADANGA..

2.3K 144 4
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

     *Chapter..32...*

  ""Gabadayansu sukayi kan goggo wacce ta sulale bisa jikin maimartaba,dagota yayi yana jijjigata yana kiran Sunanta"Suwaiba..Suwaiba.."Ammh ina ko motsi batayi,gadanga ne ya Runtuma daki aguje ya dauko ruwa yana zuwa ya duka,maimartaba ya mikasa Tafin hannunsa yana kallonsa kai Tsaye ya tsiyayamai Ruwan ahannunsa yayarfe kafin ya Shiga Shafe fuskar goggo  dashi,lokaci daya ta saki ajiyar zuciya kafin tafara kokarin bude ido,tana budewa taci karo da Gadanga,sai kawu sai Umaimah da Haisam,sai Jabir dake gefe,chan ga Mardiya da madina,sai Umar dake durkushe gefe,jin ta ahannun wani ne,yasa ta dago ido Fes ta saukesu kan Maimartaba wanda ke kallonta yana kara godema Allah...

Zabura goggo tayi daga jikin maimartaba tana Raba ido don ita azatonta mafarki take,Nunashi Tahauyi tana Fadin"Yaya kaga Abunda nake gani kuwa.."Da hanzari kawu bala ya karisa gareta ya rikota yana Fadin"Nagani Suwaiba ki Natsu kikuma godema Allah dayasan zaku kara ganin juna dukkanku kuna raye.."Fashewa da kuka goggo tayi tana lafewa jikin kawu,tamaki kara dagowa ta kalli maimartaba.

Aliyu ne ya Shiga daki ya Fito da wani kafet,babba da wasu manyan Tabarmu yazo su Haisam suka kamamasa ya Shimfida atsakar gidan,saman kafet din nan maimartaba yazauna da iyalansa sai Tabarmu su Kawu bala suka zazzauna wanda ke rike da goggo yana lallashinta,Da hannu Maimartaba ya yafito Aliyu,Jikinsa na rawa ya mike ya isa ga mahaifinsa Yana kokarin zama,Maimartaba ya rikosa yana Fadin"Aliyu..."Yafada yana shafa sumar kanshi,Ummah mai babban daki ta riko hannu Aliyu tana Fadin",Sannu sabon megida.."Mirmishi ya saki yana binta da kallo,Kusa da maimartaba ya zauna yana kallon Su Zafira,wadanda ke dagamai hannu suna dariya,shima  dagamusun yayi yana mirmishi gimbiya Razeenah ta Dafa kan Aliyu tana mirmishi tace"Sannu magajin Sarki.."Tafada tana kallon gefen gimbiya Fasilatu wacce ta cika ta batse kamar ta fashe

Goggo ce ta dago tana kallon Aliyu,wani harara ta zabgamai kafin tace"Yana raye,ammh Shine yabarmu baitaba waiwayanmu ba tsawon wannan lokacin? Tafada tana Tsiyayan hawaye sai wajen ya dauki Shuru kukan goggo kadai akeji,Ana cikin hakane sai ga mallam lawal Shida inna Ramatu Sun fado gidan,domin inna ramatu na ganin Abunda ke Faruwa takoma gida ta sako mayafi tatafi kasuwa ta fesama mallam lawal,tatasoshi kuma agaba saboda in ba dashi ba,bazata samu damar Shiga gidan goggo ba balle hartaji mai ke Faruwa,kawu na ganinshi yatashi ya rikosa yana Fadin"Alhamdulillah barka da zuwa mallam lawal kazo akan gaba don kaima kana da jibi da wannan Ahalin..",Yafada yana kariso dashi gaban maimartaba yana Fadin"Ranka yadade,wannan mallam lawal kenan uba yake ga matar da Aliyu yake aure,kuma uwa uba shi na damkama amanar Suwaiba tun bayan dana kawota garin nan,su sukayi hidima da ita har zuwa haihuwar Aliyu,mallam lawal kai kuma wannan dake gabanka Mahaifin Aliyu ne,kuma Sarki ne na Kasar Niger"Ba mallam lawal da"ake ma bayani ba inna Ramatu ce,wacce ke tsaye ta zabura tana dafe kirji da karfi ta Furta"Mahaifinsa? kuma sarkin Niger to ya akayi haka? Tafada cikin Rudewa..

Kowa kallonta yake,yana mamakin kalamata,su Maimartaba ma sun zata mahaukaciyane,ganin yadda ake kallonta ne,yasa Tayi Saurin dukar dakai tana Raba ido,Fadawa ne suka dakamata tsawa suna Fadin"Hattara dai Diyar talakawa ba"a mgana indai sarki bai bada izini ba hattara Dai..."Inna Ramatu da jikinta ke rawa ta duke ta kyarma ganinsu da bulalai,kawu ne yasa baki yace"Ku kyaleta maidakin mallam lawal ce"Shiko yana gaban Sarki durkushe kamar ya kwantamai,idanunsa sun cika da kwallah,Mikasa hannu maimartaba yayi yana Fadin"Mu gaisa Tukunnah..."Kasa mikamai hannu Mallam lawal nokewa yakeyi yana Fadin",A"a Ranka ya dade,Talaka kamata baidace na yi hannun dakai ba,Allah yakarama yawan Rai.."Mirmishi kadai sarki yayi yana Fadin"Ina Surukata take.."Yafada yana kallon goggo,wacce kanta ke duke tana Sharan kwallah.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now