ALIYU GADANGA..!

2.1K 127 0
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

         *Chapter 16*

  _Am srry For d typing errors ban samu na editashiba_✌

      "Aliyu yasha barci domin sai wajen karfe daya na Rana ya farka wanka kawai yayi agurguje ya sanya Shadda fara Dinki Muhammed riga da wando,da hula yatafi masallaci saboda ya samu jam"i,,koda aka idar da sallar bai Shigo gida ba,kofar gida yazauna yana waya da Haisam bayan sungama kiran Jabir ya Shigo wayarsa nan fa yazauna Sunata Fira,sun dau tsawon lokaci suna mgana kafin suyi sallama Akan sai sun hadu akaduna don kowannensu jibi yake san Ran komawa bakin aiki.

    Sun yanke kiran kenan sai ga KekenNapep din dayake Kai Azeema mkranta ya iso Faka keken yayi ya fito ya nufo Gadanga wanda yake binsa da kallon mamaki karisowa yayi yana mai sallama lokaci daya ya bashi hannu sukayi musabaha,bayansa Aliyu ke kallo yaga kota ina Azeema zata bullo ammh shuru,da kallon Tambayan Aliyu yake kallonsa kafin yace"Ah Ko Azeemar bataje mkrantar bane yau..?

  Sani mai KekenNapep yace"Shine Abunda yadauremin kai yallabai,ni dakaina na kaita mkranta yau da safe,ina kallo ta shige cikin haraban mkrantar,ammh Abun mamaki bayan antashesu naje daukota,ammh har duka Yan mkranta suka gama watsewa banganta ba,shine nazo nagani kodai tadawo gida da kanta ne.."Sororo Aliyu yayi kafin yace"How comes anya Azeema tadawo kuwa?bandai sani ba,buh bari na shiga na tambayi goggo naji wait for me.."Yafada da sauri yana fadawa gida,Tundaga nan yake kwalama goggo kira wacce ke daki ta zabga tagumi har lokacin dawowan Azeema yayi ammh shuru,da hanzari Ta fito,zaninta ahannun yana neman Faduwa tana fadin"Gani gadanga lafiya irin wannan kira haka? tafada cikin tashin Hankali

Gabanta yaci burki yana fadin"Goggo ina Azeema.."? Fuskar damuwa ta bayyana ga goggo tace"Nima yanzu nake Shirin kiranka awaya Tundazu lokacin dawowarta yawuce ammh haryanzu shuru bata dawo ba,bakana da nombar mai Keken ba kirashi muji kowani aiki ne ya tsaidashi baije ya daukota ba."Kansa ya dafe yana fadin"Kash..Wayyo To ai goggo ga Sanin chan,yace shima yaje mkrantar su Azeemar ammh har kowa ya watse bai ganta ba.."Salati goggo ta fara tana fadin"Na shiga uku ni Suwaiba.,To yanzu ina yarinyar tashiga kuma ba dabi"arta bane biye biye,toh ina ma ta sani balle taje.."

  kallon goggo yayi kafin yace"Goggo kishiga gidansu kigani kila ta biyo yar"uwarta sun dawo tare.."Da hanzari goggo tace"Eh kila ta yuyu haka din ne,bari naje na gani.."Tafada Tana Fadawa daki,Hijabi ta sanyo ta fice da Sauri ta bar Aliyu na Dafe kansa baisan dalili ba yaji hankalinsa yatashi,goggo na fita taci karo da Dan adaidaita,yana ganinta yahau Fadin"Ah Hajiya an ganta ne..? ko kallonsa Goggo batayi ta fada gidansu Azeema tana zabga sallama ko izini ba"a bata ba,ta sakai cikin Filin tsakar gidan,nan ta iske Azeeza da Inna Ramatu suna zaune kan Tabarma suna cin dankali,suka ga goggo ta fado kai tsaye inna Ramatu ne takalli goggo tana cewa"A"a suwaiba lafiya naga kin fadomana gida,  tamkar wani ya biyoki daga waje.."

  hararanta goggo tayi kafin tace"Azeeza ina Azeema.."?Tun dazu bata dawo gida ba,ko kin ganta yau amkaranta.."?Tafada tana maida kallonta kan Azeeza,Jin haka yasa Ran Azeeza yayi fes Tsarinta yana tafiya kan tsari,Mikewa tayi tana fadin"wlh tallahi goggo yau kaf ban saka Adda Azeema a idona ba,dana ga banganta ba bayan antashi break,naje ajinsu ammh ban ganta ba,na tambayi yan ajinsu sukace batazo ba yau,dama taje mkranta ne yau..? Azeeza ta fada cike da makirci,baya goggo taja tana fadin"Armmm.,Bakomai.."Tana fadin haka tafice da sauri Inna Ramatu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan Azeeza wacce ke mirmishi mai Fitar da amon Sauti Tabota inna tayi tana fadin"Ke nifa nashiga rudu mai wannan uwar sojan mara mutumci,take son Fada.."

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now