ALIYU GADANGA..!

2.5K 126 1
                                    

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 10*

     ""Jikinsu na rawa suka fara takowa zuwa gabansa,kowacce tanaji kamar ta saki Fitsari awando saboda tsoro da Razana,Kafin su kariso ya sunkuya akasa ya sanya hannu ya dauko wata sanda baya yakoma daga chan wajen inda ya faka motarsa ya shiga jan Dogon layi,yana gama ja,cikin wani Fusata yazo ya wucesu kamar kiftawa da bismillah ya isa chan nesa da bohol din ma nan yaja wani dogon layi,Ko kallonsu bai yi ba,daga chan bangaren ya nunasu da hannu yana fadin"Ku yan iska ko? marasa mutumci,dama kune marasa tarbiyan anguwan ko? ok To iskancinku yazo karshe daga yau oya all of u ku fara frog jump daga inda layin chan yafara zuwa inda ya kare,kuma 50 zakuyi each zuwa da dawowa to be counting one ne..."Yafada cikin gadara da isa.

  Gabadayansu suka kalli juna ganin zasu batamai lokaci yasa ya fara taku zuwa garesa ai da gudu suka isa ga layin kowacce ta duka tafara,daga nesa yace"duk wacce batayi da kyau ba,ko ta gama sai ta sake so is better da ki zage kiyi yadda nace..."Yafada yana harde hannuwansa akirji Sulaiman dake gefe yana kunshe dariya yace"Yallabai zanyi musu couting.",Da kai ya amsamai yana cije lebe kafin yace"ka sa ido akansu..Duk wacce bata yi dakyau ba juz ka waremin ita yau zasu ci ubansu ne..",Yar dariya Sulaiman yayi yana fadin"Baka da mtsala yallabai,ya fada yana kallonsu yana fadin"Toh maza kuyi da jiki...one,two...three,wlh kika bari aka barki abaya zan tsayar dake.."Yafada yana dariya jin haka yasa suka zage sai yi suke kafin kace kwabo sun Fita hayyacinsu ko goma basuyi ba,ammh haka suke kuka da majina,Tuni layin ya cika da mutane anata dariya wasu kuma na murnan Abunda ke faruwa don daman kowa yasansu Azeeza alayin basu da kunya ko kadan,wasu sai fadi suke gwara hakan,kila daga yanzu sayi hankali.

  Azeema na gefe tana barin jiki Tana kallonsu Azeeza yadda suke kuka harda majina,Dasun bude baki zasu yi mgana sai captain yace +anoder 50 din,dole sukayi Shuru da bakinsu domin Wannan wahala tayi kama da wahalan gidan yari ne,Shiko yana gefe ya harde hannuwa bisa kirji yana kallonsu yana dan murmusawa,Da kallo yabi Azeema yadda tayi wani kalan Tsausayi nufota yayi sai ta hau ja da baya,tana ganin ya kariso sai ta duka ta kama kunni tana fadin"Don Allah kayi hakuri nima zanyi..Zanyi.."Take fada tana kokarin Fara tsallan kwado tsawa ya dakamata yana fadin"Stand..."mikewa tayi jikinta na bari,Tsaki yaja kafin ya juya yana fadin"Ina abubuwan dakika zo dasu diban Ruwa.."Bakinta na rawa ta nunamai botikan guda biyu,don dayan kam ya fashe,bai kara kallonta ba ya isa garesu,da hanzari ya isa ga bohol din yasa hannu ya ture layin dake kai ya aza botikinta Yasa dayan laullausan hannunsa yafara buga bohol din,Jikin Azeema na rawa take binshi da kallo yana zubamata ruwa bai dauke hannunsa ba,sai da ya cika duka botikan guda biyu,da hannu biyu ya daukesu atare,ya nufota cike da mamaki mutane ke binsa da kallo yanayin komai cikin Jarumta da takama,sai da yazo gabda da ita kafin yace"Wuce muje bush girl kawai..."Yafada yana huci jikinta na rawa ta mika hannu tana fadin"ba..Bari na dauka.."Wani dirty look ya watsamata kafin yace"Leave dis place now..."Yafada a tsawace,da hanzari tashiga gaba tana bin su Azeeza da kallo wadanda sukayi chanza kammanin saboda wahala ga Sulaiman Shiko ba mutumci da gayyah sai yace basuyi daidai ba,sunyi yafi ashirin ammh yace biyar ne,mai kyau sauran sai sun sake,Bayanta yake bi dauke da ruwa,Ransa na masa kuna banda An raina masa wayau wai wanna ce matar da"aka Aura masa,kullum gantali alayi kamar wata karya,Saboda cin mutumci harda Debo Ruwa saboda Rainin wayau,Kallonta yake tana tafiya wani takaici ya makarosa ji yake kamar ya shakota ya kifkifamata mari saboda haushi,Suna zuwa kofar gidansu taja ta tsaya tana so ta kalleshi ammh tsoro yahanata,Kanta na kasa tace'Don..Allah ka..kayi hakuri ka..."Bata gama Rufe baki taga ya wuceta ya shige gidan dauke da Ruwan baki ta rike tana bin bayansa da kallo,kafin jikinta asanyaye tabi bayansa.

ALIYU GADANGAWhere stories live. Discover now