Fahad ya katseshi ta hanyar fad'ar " come on buddy ai wasa ce take ya fad'a yana dariya domin duk da haka ta bashi dariya"

"Wallahi nikam ai ya baby ba raina shi nayi ba ai, kaima abun ai ya baka dariya ko?

"Kauda kanshi yayi yace oya get lost yanuna mata hanyar stairs"

"Chabbbb Yaseen ba inda zani... haka kawai ina kallo na a kore ni ? Yo ai mutum ba nan ne side inshi ba aii, kuma wollah mutum ya koran ta k'arfi Ammie ta dawo gidanan hmmmmmm base na fad'aba"

Shikam mamaki ya cika shi domin a yanda yake hasashen sauran halayen ta tsaffff zata iya aikata dik abunda ta fad'a

Be ce mata komai ba kawai ya zauna.

Dawo wa tayi safff safff ta zauna inda ta tashi.
D'aukar hular ta tayi ta saka tare da k'ara Volume.

Afrah data kammala k'ure wanka tayi makeup tayi kyau matuk'a. Sashen su Ammie ta nufa tana wata tafiya kamar wata shu'uma.

Shigowa tayi a parlour ba tare da tayi sallama ba, Meenah da ta riga ta hango ta tana tunkaro gurin su, d'aga murya tayi tace;
"Malama ya zaki shigo mana haka zak'au ba sallama?

Su Captain da basu kai da ganin shigowar ta ba hankalin su ya koma inda Meenah ke kallo.

Shikam Captain ya d'auka ma Ammie ce domin yanzu tsoron ta yake akan komai zata iya🤣 ( nace anya kuwa zata iya yiwa Ammie haka?)

Ganin irin kallan da Captain ya tsareta dashi yasa ta koma domin yin sallama.

Sallamar tayi suka amsa tare da k'araso wa gunsu.
Ita kam Meenah anyi abunda takeso. D'auke kanta tayi daga gare su ta cigaba da kallon ta.

Ta kujerar su Captain tabi tare da lankwasa murya ta gaida shi.
Amsawa yayi tare da kallan ta, 4eyes sukayi a take gaban shi ya fad'i.. be d'auke idanun shi daga gare ta ba hakan yasa tayi wani shu'umin murmushi.
Zagaya wa tayi ta zauna a d'ayar kujera..

Dumm dumm!! shine sautin da gaban Meenah ya bayar alamun fad'uwar gaba, juyowa tayi ta kalle Captain da ya tsare Afrah da kallo, haka ma ta juya ta kalle Afrah da take wani mugun murmushi.
tashi tayi zumut taje gun Captain, kusa dashi ta zaune ta rik'o hanun shi, launin idanun ta ya kallah sun sauya kala sosai.

"Baby me same ka? Gaskia akwai abunda.... difff taji ta kasa fad'ar abunda take son fad'a.... kuka ta aza tana rik'e mishi hannu.... babyyy please...... waii!!! Shin mye ma zance??????? Dariya tayi tare da fad'ar bakomai.... tana hawaye😭tana dariaa😅...." wani abu take son fad'a Amma ji take kamar an aza mata wani dutse a zuciya ......Abun gwanin tausayi 😢
"Ke bana san shashanci"

Besan lokacin da bakin shi ya kufce yace haka ba.
Ya na son ya rarrshe ta but abunda ya ke ji yafi k'arfin zuciyan shi... haka ya dinga binta da ido kamar zautacce.

Keee!! Shine abunda Afra ta fad'a a tsawace.

"Mye kike wani tatta6a shi? Jarababba! Jarabar taki har takai ki dinga kai kan ki da kanki? Anyi asarar haihuwa anan.

"Keeeeeee...!!!!! Dan ubanki wa kike cewa jarababbe? Wallahi kishiga hankalinki dani, uban wa yace miki kowa irinki ne har kike wani ik'irari akan jaraba? Ko kin d'auka ban san abunda kike ba? Ki kama kanki saboda baki sanni ba tukunnah...." Meenah ce take wannan maganar gabaki d'aya se tsuma jikinta yake, gumi se tsatsafo mata yake, inda idanun ta har wani yalalo sukayi saboda masifa... da ganin kalar idanun nata kasan da kamar akwai wa'enda ke taimaka mata gurin masifa wato mutanen ta.
Duk iya kalar iskancin Afrah har ga Allah tana tsoron Meenah matuk'a domin kuwa hadda ita taso ta had'a duka har Ammien ta magan ce su, amma bokan nata ya shaida mata da cewa koshi karan kanshi tsoron Meenah da Ammien yakai kawai abar maganar su, yace mata kuma ko Shi Captain in ba wani mugun kamu irin yadda takeso maganin ze mishi ba, kawai dai tayi a sannu.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now