A kwana a tashi har kasuwancin yayi albarka Allah ya albarkaci kasuwancin sossai  gashi kuma saurayine mai qwazo saboda ana bashi kwangiloli..

Nan danan yazama yong billionaire...
So adaidai wannan lokaci ne Alhaji Shehu yace yakamata yayi aure....

Usman yace "to baba inshllh xan fidda wacce nakeso nan bada jimawa ba "

Batare da 6ata lokaci ba usman ya fidda wata diyar maqwabcin su mai suna Fareedah.

An daura auren Usman da Fareedah inda aka kaita Bado quarters suna zaman Lpia.

Anan ne Allah ya hada Hajia Fareedah  mak'wabtaka  da Hajia Rahmatu.

Hajia Ramatu tana da y'a'ya  biyu Aisha ce ta farko se Haidar.

Allah ya azurta Hajia Fareedah da Alaji usman haihuwar farko inda suka samu Maryam wacce ake kira da Miemie.

Sunyi matuqar farinciki sosai bayan shekara biyu Allah ya qara azurta Hajia Fareedah da mak'wabciyar ta  Hajia Ramatu da samun ciki... cikin ikon Allah suka haihu rana daya Hajia Fareedah ta haifi Ameenah wacce ake kira Meenah, Hajia  Ramatu  ta haiho Waleedah...

Bayan zagayowar shekara hajiya faredah taqara haihuwar Maneer

Agurguje...

Hajia Fareedah  da Alhaji  Usmab suna da y'ay'a 3  Miemie, Meenah and Maneer

Hajia Ramatu  kuwa tana da y'ay'a 3. Aisha, Haidar da Waleedah.

Tsakanin haidar dasu walida akwai taxarar shekara 13 tsakani.

An saka su duka a  makaranta Miemie da Meenah da Waleedah.

Meenah da Waleedah dsame class suke while Miemie ta wucesu da aji biyu.

Ana cikin haka se Allah ya qarama Alhaji Usman yalwar arziqi ya qara sa gina musu sabon mansion a bafarawa estate.
Ba bata lokaci suka tashi daga bado.

Watam su daya da tashi suma su hajia Ramatu suka 6a66aka suka koma  sabon gidan su na kaduna road.

Zumunci tsakanin su ba'a magana
Domin kuwa sun zama kamar yan uwa.
Suna ziyartar juna.

Tun a quruciyar yaran guda biyu wato Waleedah da Meenah suke tafka rashin arziqi domin basu Jin magana ko kad'an ga d'an banzan rashin mutunci ga jan fada amma se tsoro.

Akan tsananin surutunsu yasa aka bama Meenah class rep Waleedah ass. Acewar malamai tunda an basu shugaban ci ba batun surutu.
Wannan kenan.

                          ()()()()()()()()

                        Cigaban labari.
Dama Waleedah taje hutu ne gidan Anty Aisha dake aure ah Zamfara  state.

Yaya Haidar yace yaushe zaku rubuta jlc ku ne? Tace da ankoma da sati biyu zasu fara yace tam Allah ya taimaka tace Ameen tana wasan hauru...

Bata jima ba se ga Hajia Ramatu ta shigo "ahhh yau menah ce ah gdan? Kodai batan hanya kkyi domin nasan baki zuwa se in Waleedah nanan"

"Laaa Mama bahaka bane mommah ce ta aikoni"
Ta fad'a tana sosa qeya.

"ohh anyi haka kuwa domin d'azu takirani tacemin ai zata aiko a  kar6an  mata saqo"

bayan gaishe gaishe aka gabatar mata da abinci tace ta qoshi

Mama tabata saqon tace takaima mama. Takarba tace to.

Amaimakin ta tashi ta wuce se ta gyara zama, Mamah ta kalle ta amma se ta qyaleta ta d'auka ta gaji ne.

Bayan 1hour Mamah tace "Meenah kije ki Kaimata tun marece beyi bah"
tace "tau " se ta tashi tace to Mamah se anjima.. ok bye.. Allah ya tsare ....

Kamar barauniya haka take tafiya tana sand'a har takawo bakin gate.

Tana sand'a ta leqa aikuwa taga har yanxu mazannan nanan basu tashi ba..

Ai kuwa ai hanzarce ta koma ciki...
Mama tace "lpia baki wuce bah meenah? Ko mantuwa kikayine??

"Ehmmmm ahmmm ehnnn" take fad'a tana y'an soshe soshe, "Mama dama Anty Aisha nake son ki kiramin taba Waleedah zanyi magana da ita...

"Ok to jeka daki ki dakkomin wayana... taje ta dakko se tabata ta kira mata ita....

Aiko kamar wacce za tayi waya da saurayi ta shige dakin walida suka gaisa
Anan meenah zufah na keromata ta gayamata abunda ya faru tana neman mafitah agun walida...

Acan bangaren bana jin abunda walida take cewa meenah kawai se naga meenah ta saki murmushi se suka katse wayar..

Ahankali tafito tana sanda... kitchen tanufah a hankali, ba wanda  yangan ta  kawai senaga ta d'auki  knife🔪 tasaka a  jakanta gurin fitowane ta hadu da mama
Mama tace kingama wayar tace ehh se tabata wayar ta tafice ah gidan...

🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na 🧚🏻‍♀️
    Na
💕Teemahcutey💕
Truncated by watsapp #wattpad

Abun Alfahari Na✅Место, где живут истории. Откройте их для себя