Mowar miji (Borar Danginsa) 36

2.1K 156 45
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

36

Har kusan asuba suna zaune jigum a k'ofar room din don Doctor na investigation kan Mamah, ganin zasu kwana a gurin yasa Ameer deciding su tafi hotel kawai.a hotel bayan sunyi wanka sunyi shirin kwanciya Ameer ya matso kusada Seemby a hankali yayi wrapping hands d'insa a bayanta yace "Dreamboat kiyi hak'uri da abinda Mamah ta miki kinsan..." Saurin toshe masa baki tayi tace "It's late sweetheart let's sleep as we're going out tomorrow early in the morning, and ba bukatar ka bani hak'uri remember your mum is mine" duk jikinsa yayi sanyi Seemby bata taba nuna taji haushi ba duk me Mamah ta mata,koda kuwa Taji haushin ta Boye masa yaji dadi at least ta masa kara,but shi da kansa yasan Maamah bata kyautawa Seemby, a hankali ya fara rubbing hands nasa all over her body while thanking and blessing her. Washe gari as Early as 6;40am Seemby is done with all her morning things including bathing and dressing twins, Ameer ta kalla dayake gyara link tace "DaDa baka ganin tunda Mamah bata gama warkewa ba, we need to rent a house and settle  so that I'll be cooking a light and health food for her?" Ya sauki numfashi kafin yace "That's a good idea, I'll see, but yanzu dai we're getting late mu wuce don Doctor yace Amaal zata iya farkawa a kowa ni lokaci, remember?" Yeah ta answer shi kafin ta dauki Inteesar shi Kuma ya dauki Al~ameen as usual suka fice.
Mamah tana zaune gefen bed while Nurse tana zaune kan visitor's chair tana feeding nata, a dakile ta answer gaisuwar Seemby ba tareda ta kalleta ba, Ameer ya k'araso yana kallon Nurse din suka gaisa kafin ta mik'a masa bowl din ta fice, zama Ameer yayi gefen Mamah ya cigaba da feeding nata,zuwa can hankalinsa ya kai kan bed din da Amaal take the other days da mamaki ya kalli Mamah yace "Mamah where's my kid sis?" A hankali saboda fracture dayake wuyanta tace "Ta farka dazu so an tafi other room da ita for investigation, Sighing yayi kafin ya ajiye empty bowl din hannunsa daya gama feeding Mamah, yace " Lemmi check her out " daga kan ya fice da sauri, "he cares so much about his love one's most especially his family" Seemby said to her self, kanta a kasa yake but she can feel  Mamahs eyes on her, ta dinga juya gold ring dake hannunta tana tuna Ammi, ita ta sai mata a Saudi, "Ke dai Gaskiya Allah ya jarraveki da naci kamar tso huwar Mayya,Wannan inke Mayya ce kika kama mutum har lahira zaki kaishi" taji Mamah tace Wannan yasata dagowa a razane, tayi tunanin Wannan lokacin daya kasance  Mamah tana cikin halin rashin Lafiya zata samu sassauci Ashe ba haka abun yake ba, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, a ranta tace "Gaskiya na cuci Kaina dana auri Ameer tun farko" ta zubawa Inteesar dake wasa da hijab d'inta ido,tace  a ranta "Zan cigaba da hak'uri saboda Ku yarana",kasa dena hawaye tayi har sanda taji an taba k'ofa, tayi saurin sa hannu tana wiping tears, akan idon Ameer kuwa,kusada ita ya zauna ya rik'o hannunta da sauri ta kwace ganin yadda Mamah ta Kura musu ido,karamin tsaki Mamah tayi kafin a hankali tace "Ameer zoka zauna a nan" ta karashe tana pointing masa kusada ita, yake yayi yace "am okay here Maa" tayi shiru kawai tana hararar Seemby, ganin haka kawai sai Seemby ta mik'e ta fita da sauri shima Ameer ya bita kafin Mamah ta hana sa,rik'o hannunta yayi da sauri bayan ya dora murmushi kan angry face nasa yace "Ina zaki?" Yake tayi kafin tace "Zan zauna a resting chairs din can nasan kaida Mamah needs privacy, naga tunda muka zo Bakuyi wata magana ba" "come on kema ae family member ba babu wani sirri da zamuyi da Ba zamu so kiji ba, zo mu koma pls" bata son tace masa bazata koma ba amma lallai bata son komawa sai ta tsaya kawai bata kara motsawa ba, shikam ido ya zuba mata yana examining face nata,she look very fail kamar wadda tayi cuta haka ta wani fada,sai yayi clearing throat kafin yace "Bari na dauko Al~ameen kije kiga Amaal sai na maidaku gida,ganin batayi musu ba yasashi komawa room din Mamah, Ba tareda yace komai ba ya dauko boy dake wasa a floor, a tare suka shiga room din da Amal take,tana zaune tana facing k'ofa, kuka ta fashe da ganinsu Wanda ya karyawa Seemby ma zuciya sai kawai ta durk'usa a inda take ta fashe da kukan itama,Ameer ganin haka yasashi saurin dago Seemby yajata suka fita a room din. Tasha mamaki dataga taxi ta sauke su k'ofar wani bungalow me kyau bata San time da Ameer ya musu renting gidan ba tunda suna tare, yasan mamaki take don haka ya daga mata gira yana dariya yace " a waya nayi komai Mamie" bata ce komai ba har saida suka shiga gidan ta fara rava kyaun gidan.sai dare Ameer yace zai koma hospital, ya dinga mamaki jin Seemby batace zata bishi ba, shi da kansa yasan yau Mamah ta kai Seemby bango don tunda suka dawo batace dashi komai ba sai in ya mata magana ta answer shi sanda ranta yaso.

Hospital

Ameer ya kalli Mamah shima ransa a matukar bace yake duk yau saboda Bacin ran Seemby, yace "Maamah gaskiya kin fara kaini bango haba, Seemby tana matukar k'ok'arin zama damu duk da irin abubuwan da ke da Afaf Kuke Mata bata taba bata ranta ba, Yanzu bakida lafiya ina ganin ma kamar ta Fini damuwa ta biyo ni amma saiki dinga zaginta?" "Haka ta fada maka na zageta?" Mamah ta katse shi, yayi shiru sai huci yake zuciyarsa tana masa zafi, ta cigaba "Ban taba ji ina sonta ba Kuma bazan taba ba, ban Kuma taba cewa ta damu Dani ba, biyo ka datayi Kuma ai saboda Allah ya Dora Mata jarava da naci ne kamar mayya" maganganun sun masa zafi yasan idan ya cigaba da bata answer zuciya zata kaisa ya aikata ba dai-dai ba sai kawai ya mike ya fice ya mata banging k'ofar.
Da murna Seemby ta taresa bayan ta rungume shi tace "Ya jikin Mamah? Allah yasa taci abinci" yaja hannunta gefen bed,bayan sun zauna yace "Bansan wace irin zuciya ce dake ba amma na tabbatar ba irin wadda Mamah take miki tunani da gori bace, nasan sona kike da yawa shiyasa kike jure duk abinda Mamah take miki amma nikam gaskiya I can't withstand it anymore dole na maidake gida Seemby I can't cope with abinda take miki ,I just can't" ya k'arasa yana hawaye, itama Seemby hawaye take itada kanta tasan hak'urinta ya kusa yin yawa,abinda Mamah take mata ba kowace mace zata iya dauka ba tunda dai ba Dan gold bane Ameer bare mace ta tsaya a dinga takata a kansa amma Kuma tana so ta faranta ran Ameer Dana Ammi don bazata manta ba kullum fadan Ammi vai wuce mutum ya zama mai hak'uri da juriya a duk halin daya tsinci kansa saboda Allah baya taba mantawa da Dan Adam saidai yana bukatar mutum yaci jajjaravar yadaya masa, batasan tace "Na yarda Wannan auren shine jajjaravawa ta Kuma shine kaddara ta,ina Fatah na cinye Wannan jajjaravawar ya Allah" kawai sai taji Ameer yace "Zakici Wannan jaravawar,I promise you indai aljannarki gurina take to na baki, no word in this world is enough to describe your kindness, only God can reward you for who you're, ke mace ta gari ce Seemby wadda a Wannan zamanin irin ki basuda yawa Sam,may God bless you for being with me, for your durability... I love you more and more than they way uwa take son Danta" kasa answer shi tayi but sincerely his words gives her strength taji zata iya doubling hak'uri da durability d'inta just for him, she know for sure Almighty is with her He's just waiting for a time to made her most happiest person in the world, saita kwanta a jikin Ameer tana wiping tears, duka jikinsu a sanyaye yake saboda haka Basu kara komai ba sai kwanciya da sukayi har bacci yayi gaba dasu.
Washe gari tun da Seemby tayi subh prayer bata koma ba kitchen ta shige ta fara preparing light food for Mamah, Ameer yayi tsaye k'ofar kitchen din yana kallon yadda take shivering, tun tsakar dare dama yaji zafi jikinta kamar me fever, ya k'araso ya rik'o ta jikinsa yana feeling temperature d'inta da hannunsa a hankali yace "Bakida lafiya ki hak'ura da abincin nn sai mu siya a restaurant in mun fita" ta noke hadeda cewa "A'a nikam I want to cook for Mamah, mu sai mu siya" daga haka ta kwace a jikinsa ta koma position d'inta na da,ko hour batayi ba ta kammala, wanka tayi tana ji duk zazzavi ya dameta amma bata nuna ba suka tafi,da sallama suka shiga room din a tare,Nurse ta answer tana gaida su, tana fita Seemby ta durk'usa har kasa tace "Mamah kin tashi Lafiya? Ya jikin ki?" As usual Mamah shiru ta mata Ameer kamar dole aka masa ya gaidata can ciki,sannan ya fara k'ok'arin bud'e food flask da suka zo da,a plate ya zuba mata chips da plantain rings, a hankali ya kai mata baki ta karba tana ci bayan tayi swallowing yana kallon Seemby yace "Mamah is it yummy?" Tayi nodding kanta tana murmushi ya cigaba "Maamah Simbiat ce ta miki Wannan da kanta saboda...." Wani yunkurin amai da tayi ne Wanda Seemby bazata taba mantawa ba a rayuwar ta ne yasashi saurin dakatawa yana binta da kallo, ta hade fuska irin Wanda Ba su taba gani tayi ba tace "Ameer ka cuceni daka bani abincin Wannan bakar kadarar,wa yasan abinda ta saka min a ciki?Ashe za'a iya had'a baki dakai a cutar Dani? Ban yafe ba idan ka kara bani abincin ta Ameer",  A fusace Seemby ta mik'e tace " ko wadda ta haifi makiyina bazan bata guva ba bare wadda ta haifi Oban yarana,kisa a ranki banida niyyar cutar dake a iya zamana daku Kuma ko wani be fadamin ba ni nasan zuciya ta me kyau ce" tana kaiwa nan ta fice a room din da sauri, kallon cikin ido Mamah da Ameer ke yiwa jiunan su kowa da abinda yake sakawa a ransa......

_Anzo dai-dai gurin wallahi.. Lallai Mamah takai Seemby bango tunda ta tanka Mata? Ta Burge ki\ka? Nidai wallahi tamin dai-dai naso ma ta fadi Wanda yafi haka🤣🤣🤣💃🏻💃🏻_

Cute💖

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now