Mowar miji (Borar Danginsa) 24

1.2K 81 20
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

Show me the love *comment*, *Like*& *share* please
  _You know how I love reading your reactions,and how they encourage me to write faster....ta-ta and type your comments please fans_

*wattpad* @Zainab Yakasai

24

Da gudu Seemby ta shigo parlour, ta wuce upstairs direct, Ammi da Daddy dake parlour sukayi saurin mik'ewa suna kallon-kallo, Ammi ce tayi k'arfin halin bin bayanta jiki a sanyaye. Rahienert dake toilet tayi saurin fitowa jin faduwar mutum tsakiyar bed, dai-dai nan kuma Ammi ta shigo,jikinta har rawa yake ta k'arasa bed din, tayi azamar dago Simbiat tace "Ke lafiyar ki kuwa kika shigo mana gida da gudu,kikazo nan kika zube kina kuka?" Seemby ta rungume Ammi tana cigaba da kukan, Ammi duk hankalinta yaki kwanciya gashi Simbiat is not ready to stop crying, Ammi ta girgizata da karfi a tsawace tace "Ke dan ubanki kinada hankali kuwa? Kinaji ina miki magana shine kika min shiru kina cigaba da kukan? Wani Abu ya hadaku da Ameer din?" Kara kankameta Seemby tayi a hankali take rage sautin kukanta, Rahienert dake tsaye har a lokacin ta k'araso a sanyaye ta dafa bayan Seemby tace "Aunty ki daure ki fada mana abinda yake faruwa,kinga Hankalin Ammi ya tashi" a hankali Seemby ta dago tana goge hawayenta tace "Cewa yayi in tafi gida" Ammi ta mik'e da sauri tana zaro ido tace "Shi Ameer din? Me kikayi masa da zafi haka?" Shiru Simbiat tayi not ready to talk, ta maida kanta kasa tana wasa da yatsunta, maganar duniya Ammi tayi amma Seemby ko dagowa batayi ba bare Ammi tasa ran Answer, a hankali Ammi taja kafarta ta fice daga room din, room din Daddy ta wuce yana tsaye daga gani k'arfin hali yake amma deeply ya damu yaji me ya faru Seemby ta dawo gida at this instance, Jin Ammi ta rufe kofa yasa shi saurin juyowa har yana banging table ya k'araso wajenta,riko hannunta yayi yace "Ameenatou me ya faru Seemby tazo gida yanzu?" Ammi ta kalleshi ya bata tausayi sosai, ta kararo murmushi trying to assures him everything is okay, tace "Banajin wata babbar matsala ce fa Daddyn Seemby, kasan halin Simbiat tanada rauni sosai (Just like me, my mum always use to say Zainab rauni ne da ita sosai, and I like it),Daddy can't believe her, yasan issa very serious case, Seemby tanada rauni amma kuma tanada zurfin ciki, is hardly ta fadawa wani damuwarta sai in abun yayi zafi sosai,ya dinga safa da marwa cikin room din, Ammi ma duk zuciyarta zafi take Mata, tace "Nasan Halin 'yata batada matsala, na kasa gane me tayiwa Ameer da zafi yace yaje gida" Daddy ya juyo a razane yace "What? Kikace yace taje gida?" Ammi tayi nodding kanta, Daddy ya dinga Sauke numfashi lallai yaron nan, su ze yiwa haka? Wayarsa ya dauko da sauri ya shiga dialing number Ameer amma har ta katse Ameer beyi picking ba, Daddy ya kira yafi sau 10 ba'ayi picking ba, a hankali ya sauke wayar, ya koma gefen bed ya zauna hadeda dafe kansa,Ammi ma tabi bayansa.
*******************
A hospital kuwa tunda Seemby ta fice Mahmoud ya dawo da kallonsa kan Ameer yana masa kallon tuhuma, ganin haka yasa Ameer ya juya kansa da sauri yana facing wall, Mahmoud ya juyo dashi da sauri yace ",Hey! What's happening between you guys? Me tayi da zafi haka? Wait.... Did you really know what you just do? Do you know what you're causing yourself ? Remember its your Simbiat a mother to your soon coming babe, Simbiat doesn't deserves this,no matter what she have done to you, you remember her kindness Ameer" Ameer da maganganun Mahmoud ke neman karya masa zuciyarta yayi saurin sa hannunsa ya janyo pillow ya rufe fuskarsa, tabbas Seemby didn't deserves what he did to her, amma she offended him and he have to punish her, to let her know that what she did is absolutely wrong, Mahmoud yaji haushi sosai yasa hannu ya fisge pillow yayi throwing, yace "Baka jina ne Ameer? Me Simbiat tayi maka da zafi nace?" Ameer ya mik'e a zafafe yace "You count yourself out of this case, issa personal case, don haka mute your mouth in zaka iya, if not ..then get out of this room immediately" ya k'arasa yana nuna masa k'ofa, Ran Mahmoud ya baci sosai shima ya mike yana bin Ameer da mugun kallo yace "Haka kace ko Ameer? Lallai! To daga yau kar matsalarka ta kara tashi ka nemeni , ka rik'e duk wata damuwarka, nima zan rik'e nawa kaji?" Daga nan ya fice daga room din ya masa banging k'ofar, sulalewa Ameer yayi kan bed ya kife kansa jikin side rail wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a idanunsa, meyasa Simbiat zata masa haka, tanada gudun zuciya fa, meyasa zata kwashe masa kudin account d'insa? Kansa ya dinga jerowa wadannan tambayoyin, ganin bashida answer yasa ya cigaba da hawayensa har a lokacin be dago kansa daga jikin side rail ba, a haka Doctor Haiydar ya shigo ya samesa, ya dago da sauri jin mutum a kusa dashi ya shiga goge hawaye, Haiydar yace "Are you okay Ameer?" Ameer ya kakaro murmushi yace "Absolutely okay Doctor" daga nan ya mik'e ya sauko daga kan bed din ya shige toilet da sauri.

**************
A bangaren Afaf ma ganin Su Ameer sun fita cikin wani hali ba karamin farin ciki yasata, jiki na rawa ta kira Jimoh ta fada mata duk yadda komai ya faru, Jimoh ta dinga dariyar  mugunta tace "You see! Ai na fada miki sai sun kwashi kashin su a hannu, this is just the beginning" Afaf ma dariya ta dinga yi tace "Nasan ba abinda bazaki iya ba tawan, a cigaba da gashi" a tare sukayi dariya sukace "Suya sai ranar sallah" daga nan sukayi hanging, Afaf ta shige room din Simbiat idonta yakai kan wayoyinsu dake kan bedside drawer ta k'arasa da sauri ta dauko, fashewa tayi da dariya ganin messages dake kan screen din wayoyin ta dinga dariyar harda rik'e ciki, ta Dade a tsaye kafin ta ajiye musu wayoyin cikin side drawer ya fice a room din, tana shiga room d'inta tayi tsalle ta fada kan bed ta hugging pillow tightly wani sanyi takeji cikin ranta, tasan ta Simbiat ta k'are yau din nan.
Zumbur kuma ta mike tace a fili "Nasan bakin nacin Ameer sai yaki sakinta fa, tunda yana sonta sosai" ta fara zagaye a room din, Maamah! Maamah ta fado mata, ta k'arasa kan mirror ta dauko wayarta da sauri ta fara dialing number mamah, ai Maamah kamar jira take tayi picking tace "Lafiya Zainab" Afaf ta gyara tsayuwa tace "Inafa lafiya Wannan shegiyar Simbiat din ta sacewa d'anki duk kudin dake cikin account d'insa" Maamah ta mike zumbur ta dafe kirji tana zaro ido kamar Afaf tana gabanta tace "Kice Allah? To yanzu me Dan banzan yayi akai?" Afaf tace "Uhmm ai inaga Sumewa yayi, don be taba tunanin ita barauniya bace sai yanzu data gwada masa, ni yanzu shawara zan baki ki kirasa kisa ya saketa tun wuri tun bata k'arasa yashe muba, tunda ni dama na Dade ina ganin ana min 'yan d'auke -d'auke shiru kawai nake don nasan Ameer cewa zeyi na fiya son fitina" Maamah ta rik'e habarta tace "Lumbu-lumbu wutar k'aik'ayi, wato yashe min d'a tayi ko? To karshenta yazo a gidan D'ana wallahi" Tana kaiwa nan tayi hanging, Afaf ya fada bed ta dinga kyalkyala dariya, da alama hak'anta ya cimma ruwa.
Maamah tana sauke waya ta fara Neman number Ameer, tanata ringing amma Ameer ko kallon wayar beyi ba, kuma bashida niyya, ya tsani kansa, ya tsani  komai a duniya, ji yake inama yasan inda mutuwa take ya kaimata kansa. Maamah ganin ta kira yafi 20times yasata rubuta masa text kamar haka : Dama nasan bazakayi picking ba don kar in fada maka gaskiya, to ina me tabbatar maka cewa ko zaku mutu gaba daya sai ka saki barauniyar yarinyar nan wallahi, kuma kazo gida ina Neman ka yanzu.....
Ameer besan meyasa ba duk da yana jin haushin Seemby amma ransa ya sosu da Maamah ta kirata barauniya, waye ma ya fad'a mata abinda ke faruwa to? Afaf ce, which means tana sane da abinda yake faruwa kenan.tsaki yaja ya wulla wayar kan bed ya hau kan praying mat daya shimfida ya tada sallah.....

*Comment please*

Cute💖

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now