mowar miji (Borar Danginsa)

1.5K 77 4
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

12

After a month...
  Ameer ne ya shigo room d'in Afaf a fusace yana mata mugun kallo itako ko a jikinta don mayarda hankalinta tayi kan wayarta bata ko kalleshi ba, abun ya bashi haushi ya fizge wayar sai anan ta dago a tsawace tace "Bani wayata" ya doka wayar da kasa yace "ke  ya kamata ki kama kanki  a gidan nan, Simbiat baiwarki ce  da kullum zata dinga dafa min abinci ke kuma kina kwance kina danne-danne banza a waya?" Afaf ta watsa masa harara tace "May be haka din ne, wait kaga nifa ban maka kala da wadda zata shiga kitchen ta dafa maka abinci ba, idan da gaske ka gaji da girkin da take maka you get her a maid sai tana muku girki, kuma wallahi tunda ka fasa min wayana sai ka biyani" ta karashe tana d'auko wayarta a kasa, sakin baki Ameer kawai yayi ya kasa fahimtar kalar rainin da girl din tayi masa, amma shi da kansa yasan ba lefin ta bane Maamah ne ta bata kofa, ya fisgota yace "Bazaki shiga hankalinki bako?" Bata damuba tace "Eh din, kuma ka sakeni kafin nakira Maamah yanzu wallahi" sai ya kara matse hannunta har saida tayi kara yayi sa'ar fisge wayarta yace "Ba dai wannan wayarce hanyar da kike bi kina hadani da Maamah ba? To daga yau bake ba ita" daga haka ya cillarda ita a gurin ya fice.
  Ko a jikinta ta mik'e ta bud'e bedside drawer ta Ciro dayar wayarta tayi plugging charge tayi kwanciyarta, wato yaga kwana biyu tayi sanyi shine yake son Tayar Mata da borinta ko? Zatayi maganinsu yanzu, jira kawai take yasa kafa yba.fita itama ta fice gidansu Jimoh.
Ai kam ko hour be karaba a gidan ya fice, tayi saurin saukowa a gado ta shirya cikin sauri, a parlour suka kusa cin karo da Simbiat, Simbiat ta matsa da sauri tace "Yi hak'uri ya Afaf ban kula dake bane" tsaki Afaf taja batace komai ba ta wuce , Simbiat abun sai ya bata mamaki don da ace dane da tuni ta fara zaginta, sai gurin 4:49pm ta dawo gidan, tun a gate take jiyo hayaniya a gidan abun ya daure Mata kai, ta k'arasa cikin sauri parlour... Turus tayi ganin Simbiat da kawayenta sun cika parlour ga abinci kala-kala agurin ta hade fuska ta nuna Simbiat da hannu tace "Kee! Wadannan tarkacen fa daga ina?" Ta nuna bak'in tana kallonsu a wulak'ance, Simbiat jikinta har rawa yake tasan friends d'inta zasu iya kula Afaf ayi masifa tace " Friends dina ne" "uhm..to kuma shine kika Tara mana su suka cika mana gida da surutu, kuma wannan abinci waye yasa ki basu, oh.... Ave understand abinci sukazo ci kenan ko? To sunci rabonsu ki fitar min dasu anan kafin nasa afitar dasu yanzu" Kharimat daya daga cikin kawayen Simbiat tace "Kan uba mune ma mukazo cin abinci?" Simbiat tayi saurin rufe mata baki tace "Dan Allah kiyi hak'uri, kuje kawai zamuyi waya" Duk se suka zaro ido suna kallonta da mamaki, ta marairaice ta riko hannun iyami tace "iyami kuje gida zanzo daga baya" iyami ta fisge hannunta tace "Amma wallahi kin bada mata Simbiat, wai kirasa Wanda zakiji tsoro sai kishiya..chaii Allah ya sawwake" taja handbag d'inta azuciye ta fice, sauran ma suka rufa mata baya suna masifa. Zata wuce daki Afaf dake tsaye har a lokacin ta daka mata tsawa tace "To uban wa kike jira ya gyara miki gurin kuma? And lemmi tell you something daga yau har rana me kamar ta yau karki kara ajiyemin kazaman friends dinki a parlour in sunzo ki kaisu room dinki kin gane?" "To" kawai Simbiat tace ta k'araso jiki a sabule ta fara gyara wajen.
Koda Ameer ya dawo Simbiat bata gaya masa komai kan abinda ya faru ba, amma duk da haka ya fahimci tana cikin damuwa yayi nacin da fada masa kuma ta kafe wai babu komai.
Washe gari suna breakfast Simbiat ta kalli Ameer tace "Dreamboat inason inje in gaida Maamah" yaji dadi sosai kuma sai yaji wani tausayinta ya rufe shi tanason ta dinga zuwa gurin Maamah, amma ita Maamah Sam bata sonta , ya kakalo murmushi yace "To idan mun gama sai ki shirya na kaiki ko?" Murmushin itama tayi tace "to sai muje tareda ya Afaf ko?" Ya b'ata rai bece komai ba don yasan in yace baza'a je da itaba Simbiat zatayi fushi ko tace itama bazata ba.
Sanda suka fito zasu wuce Ameer ya daure ya leka room d'in Afaf yace "ki taso zamu tafi gidan Maamah" bata ko dago ta kalleshi ba tace "Sai naga kamar nasan hanya ko?" Abun ya kona mishi rai Amma kawai ya dake yajuyo, Simbiat tace "Tana ina" yace "Zata biyo mu anjima" bata kara cewa komai ba, har suka bar parlour.
Sanda suka k'araso gidan Maamah Daddy baya nan Sai Maamah kawai da Amaal a parlour , Amaal ta juyo da sauri jin sallamarsu, ai da gudu ta taso ta rungume Simbiat tana mata oyoyo, Maamah kam kallo daya tayi musu ta d'auke kai, duk Sai sukaji ba dadi suka k'araso gabanta suka durk'usa suna gaidata "Tafi 40sc batace komai ba kafin can ciki ta answer musu da " lafiya " Ameer ya tashi ya koma kan 2sitter kusada Amaal, yayinda Simbiat takasa motsawa daga durkuson da tayi kanta a kasa tana ta wasa da wayar hannunta. Zuwa can Maamah ta juyo tana harararta a tsawace tace ",keee! Lafiya kika sakani agaba ne haka? Kina wani kasa da kai munafika kawai" Simbiat ta tsorata sosai da Maamah sai ta mik'e da sauri ta fice a parlour jikinta har rawa yake, me tayiwa Maamah da zafi haka? Ta tambayi kanta, ran Ameer ya baci sosai kawai shima ya mike a fusace ya fice, tana tsaye jikin kofa yaja hannunta gurin mota ba tareda yace mata komai ba, a cikin mota Simbiat kasa cigaba da rikon kukan dake cinta tayi, kawai sai ta fashe masa da kukan, Ameer bazai iya hana kukan ba yafiso tayi ma ko zata samu relief cikin zuciyarta haka duk da yanajin kukan da take a ransa Amma ya rabu da ita taitayi har suka je gida.





Cute❤

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now