Mowar miji ( Borar Danginsa)

1.5K 82 0
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

16

Washe gari Afaf ta shirya zata gurin Maamah, amma ga mamakinta gate man yace "Yallabai yace kar abar kowa ya fita" ranta ya baci sosai, tace lallai Ameer har ya isa ya mata kulle? Komawa tayi direct room d'insa ta shiga suna tare da Simbiat yana feeding d'inta, ta dinga harararsu tana tabe baki, Ameer yayi k'arfin halin cewa "ke lafiya kika zo kika tsaya mana aka?", ta murguda masa baki tace " So nake kasa gate man ya bud'e min zanje unguwa" ya dinga mamakin irin k'arfin halinta yace "To da izini wa zaki fita?" Afaf ta fara dariya tana kallonsa tace "Kana expecting zanyi seeking permission a gurinka idan zan fita? Who do you think you're to me? A husband right? To nikam banga husband a nan ba,kaga Nifa na aureka ne kawai don in bakanta ranku duka, amma kafin auren na dade da cireka araina saboda naga kaima ba sona kake, kuma naga ba zaman mata da miji muke a gidan ba, bare na tambayeka in zan fita, lemmi just remind you, constitution ya bamu right to freedom of movement, so ba yadda za'ayi ka hanani fita" batasan time din da Ameer ya k'araso gurin ba kawai ji tayi yasa hannu ya danna shoulders d'inta har saida takai kasa, yace "Ke you have to watch your words, ni ba sa'an ki bane da zaki dinga fadamin yadda kikeso, lemmi tell you ke baki isa inji tsoron kiba, mutuncin Maamah na nake gani yasa nake saurara miki, amma daga yau zan fara wulakantaki San raina, sai na nuna miki ke karamar yar iska ce,kince zaki bakanta ta mana right? To I'll never beg you to change your mind, you can go ahead amma wallahi saina lahira yafiki jin dadi a gidan nan, kuma ba constitution ba ko uban meye ya baki right din gantali daga yau baki kara fita a gidan nan sai idan naso useless" daga haka ya fisgota ya fitar da ita daga room d'in, Simbiat dai tagumi tayi tana kallonsu duka,lamarin yafi k'arfin kanta,batada abin cewa,sai ta cigaba da cin abincinta, Ameer kam yaji dad'i da Simbiat bata masa magana ba,sai ya dawo ya fara massaging mata kafarta, har ta gama cin abincinta, sai a sannan ta masa magana tace "Ameer inason zuwa gurin Ammina" ya matse hannunta har tayi kara yace "meyasa kika cemin Ameer?dama ana fadar sunan babba gatsal?" sai ta rufe idonta tana dariya a shagwabe tace "Kuma shine zaka matse min hannu, dana karye fa?" Yace "Sai na kaiki a Dora ki" tayi murmushi kawai tace "To kayi hak'uri bazan kuma fadar sunanka haka ba" yana murmushi yace "Nidai bazan hak'ura ba Gaskiya, sai kinyi kissing dina 50 times" Simbiat bata San sanda ta mike ba tana zare ido tace "Dan Allah kayi hak'uri, bazan iyaba,inajin kunyarka" kunya?wai kunya? Ameer yace a ransa, sai kuma ya bata rai ya sake mata hannu yace "Shikenan" ya mik'e wai shi dole yayi fushi,Simbiat bataji dadi ba, tayi saurin riko hannunsa, ko ba komai Ameer yana k'ok'arin faranta mata meyasa itama bazata yimasa yadda yakeso ba, tayi tunani. Dawowa yayi ya zauna kusa da ita, ta rufe idonta tayi kissing forehead d'insa, ya dagota yace "Ba anan ba,anan" ya k'arasa yana nuna lips d'insa,kamar zata tsaga kasa ta shige don kunya, haka dai ta daure ta masa sau 30 ta koma zata kwanta ya rikota yace "Saura 20" ta marairaice tace "Ni na gaji bacci zanyi" sai ya kwantar da ita yace "To Shikenan, ina binki bashi, you'll pay" tayi murmushi kawai idonta a rufe tace "I'll, may be to night" daga nan taja blanket ta rufe duk jikinta harda fuskarta, Ameer mik'ewa yayi ya koma parlour ya kwanta yana dialing wata number, bugu biyu akayi picking yace "Hello Imran, kana jina so nake ayiwa wife dina passport cikin week dinnan zamu fita" Sai yayi shiru, can kuma yace "Okay,okay please you come over, and collect all the requirements" ya sake yin shiru kafin yayi hanging.
  Bayan kwana 2 passport din Simbiat ya zama ready, Ameer so yake yayi surprising d'inta, dan haka bece mata komai ba yaje ya musu visa zasu wuce Florida, sai da komai ya dai-daita ana gobe zasu wuce ya sameta a kitchen, time din taji sauki,rungumeta yayi ta baya,yana hura mata iska a kunnenta a hankali yace "sweetheart inkin gama ki shirya na kaiki gurin Ammi" , da sauri Simbiat ta kashe gas tace "Babe am ready, let's get going" yaja hancinta yana murmushi yace "Kin fiya zumudi,baza kici abincin naki ba zamu wuce?" Har ta kusa kaiwa k'ofar kitchen tace "Dama d'anwake nake sha'awa buh innaje gida Rahienert tayi min wani,sai dai in kai zakaci" ya biyota yana tabe baki yace "Ni ban iya cin wannan abun ba, muje kawai".
A mota Simbiat sai murna take,ji take kamar ta karbi driving din don gani take kamar baya sauri,tayi missing Ammi over, sai cewa take ya kara Speed yana biye mata, Sam basu kula da wata mota dake tawowa ba saiji sukayi ta daki tasu motar, motarsu ta koma gefe, Simbiat ta buge kanta da glass jikinta sai rawa yake, da kyar Ameer ya samu ya lallabata tabar tsorata, sai da suka cigaba da tafiya yace " Ai duk ke kika janyo da kika dinga sawa ina kara speed, da kinmin asarar babe fa?, Simbiat dai ba baki sai nishi take sama-Sama, suna isa gida tayi saurin ficewa ta barshi,yayi dariya yabi bayan ta,A parlour suka tararda Ammi, ya durk'usa yana gaisheta,ta answer da fara'a , yace "Maamah dama kawota nayi ta miki sallama gobe zamu wuce Florida" Simbiat ta zaro ido tana kallonsa tace "Baka gaya minba" yayi murmushi yace "Just wanted to surprise you" Ai tsalle Simbiat tayi ta rungume Ammi tana murna , Ameer ya mik'e da sauri yace "Babe Meye haka kinason bawa babyna wahala ne" Ammi ta cireta a jikinta tana dariya tana kallon Ameer, sai yaji kunya Sam besan ma yayi maganar ba,ya fice da sauri yana murmushi...


Cute

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now