mowar miji (Borar Danginsa)

1.8K 97 0
                                    

Mowar miji(Borar Danginsa)

By Zainab shukrah

10

Hade rai Maamah tayi tana masa mugun kallo, shikam marairaicewa yayi ya durk'usa akan kafarsa shi da kansa yasan bashida yadda zeyi ya kare kansa, ya Riga yayi lefi... Maamah ganin ya saduda yasa ta zauna kan chair tace "Ameer bakada mutunci wallahi.. Amma ni yanzu nayi deciding kawai Afaf zata dawo nan gidan gaba daya naga kamar kafisoñ zaman nan din? A razane yake kallonta ya za" ayi Simbiat ta iya zama da Afaf? Take jikinsa ya fara rawa ya bud'e baki zeyi magana Maamah tace "Don't dare say I single word here.. Ave already made up my mind and dole ayi yadda nake so, kamar Ameer zeyi kuka yake ji... Maamah bata kara cewa komai ba ta mik'e ta fice.. Tana fita Simbiat ta juyo rai a bace tace " Ameer meyasa ka kwana gidan nan, kaga irin abinda nake gudu ya faru ko?, me zesa familynka bazasu tsaneni ba? Tabbas zasuyi tunanin ni na zugaka kazo, jiya fa aka Kai Afaf gidanka amatsayin amarya Ameer, meyasa zakamin haka?meyasa?" Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e ta shige room d'inta tayi banging k'ofar, Ameer kwatanta halin tashin hankalin da ya shiga ma bata baki don har wani jiri yaji yana dibansa , ya kasa ko motsi yayi zaman sa a gurin, har ya rasa tunanin da zeyi, yafi k'arfin awa daya a zaune gashi Simbiat bata fito ba, yana nan zaune kawai sai ganin Maamah ta k'ara shigowa yayi, yaga tashin hankali kuwa don tare suke da Afaf da Ummi dukansu ransu a hade yake kamar basu taba dariya, Maamah ta bud'e wani room Wanda bana kowa bane tace "Afaf this most be your room, ki shiga ki zauna za'a kwaso miki kayanki daga can gidan daga baya" Afaf tayi murmushi kawai ta shige, Maamah da Ummi ko kallon Ameer basuyi ba suka fice, Ameer gathering courage yayi ya mik'e yaje k'ofar Simbiat ya dinga knocking amma bata bud'e ba banda kuka ba abinda take, a zuciye ya wuce k'ofar Afaf, duk itacen silan komai. Zan gyara mata zama, yace a ransa, murda handle yayi cikin sa'a ko k'ofar a bud'e take, be bata lokaci ba ya shige ciki ya fisgota daga kan bed din da take kwance dare-dare, ya mugun shak'eta yace "ke wace irin shed'aniya ce Zainab? Meyasa kika hadani da Maamah? Kinaso na kasheki ne? Nasan bakida niyyar alheri a wannan zaman naki da Simbiat , bazan baki hak'uri ba rather I'll beg you pls ki bata mata rai kinji?" Daga haka ya wullata bed, Afaf ta fasa k'ara tana murza wuyanta dayasha hannun maza, tace "Mugu, azzalumi kawai wallahi bazan yafe m ..." Tass ya mari bakin  fitsara yace "Bazaki saduda ba Zainab? Inaji yau zan gyara miki zama a gidan nan, and where's your phone, miko min yanzu kan na saba miki" Duk da Afaf arude take hakan be hanata fashewa da dariya ba tace "Malam you're deceiving yourself if you think zan maka biyayya ne? Aww..you better wakeup from your slumber and ita wadda kake cewa kar a bata mata ran wallahi Allah I promise you wannan gidan sai ya fiye mata kabarin kafiri kunci, sai na wahalar da zuciyarta" Ameer kawai zaro Ab wire dake jikin plasma yayi ya fara zubawa Afaf, so yake ya dai-,daita mata zama, dan ya tabbatar zata iya abinda tace, shedaniya ce. Ihu kawai Afaf take tana fada masa maganganu yadda ranta yaso shi kuma so yake sai bakinta ya mutu ze kyaleta, Simbiat bataza iya jurewa ba, Mace ce fa yar uwarta, ai da gudu ta fito ta banko dakin ta shigo, da gudu ta k'arasa ta rungume  Ameer ta baya tace "Honey bun please stop beaten her, ko bakasan babu kyau dukan matar aure ba, and ko babu komai yar uwarka ce kanason lalata muku zumunci ne?" Maganarta tayi tasiri a gurinsa amma sai ya dake ya cireta a jikinsa yace "Kije room d'inki zanzo yanzu" ta turje tace "Wallahi bazan tafi ba , in kuma kasan haka zaka dinga mata a gidan nan ka fadamin wallahi tafiya zanyi Dan bazan so in zama silan bacin zumuncin kuba" Afaf ta watsa Mata harara tace "Munafika wallahi sai nayi maganinki nan kusa, ai duk kece silan komai"  Simbiat ta cigaba da kuka tace "Trust me Afaf wallahi banice sila ba, bansan komai ba don Allah kiyi hak'uri" Ameer Jan hannun Simbiat yayi suka fice.
Suna fita Afaf ta janyo wayarta tayi dialing number Jimoh, tana picking ta fashe mata da kuka tace "Jimoh zan miki sending address din gidan Ameer na bawo road kizo Dan Allah" daga nan ta kashe wayar ta fara Mata text na address din
  A bangaren su Simbiat kuwa tunda suka shiga room Simbiat take rikici, gaba daya rasa yadda zata sa kanta tayi, kiyayyar dangin miji babu dadi Sam gashi yanzu Ameer ya janyo Mata, Ameer kam harya rasa me zece Mata hankalinta ya kwanta sai kawai ya tsaya yana kallonta



Cute

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now