mowar miji (Borar Danginsa) 34

1.2K 86 6
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍


Don't forget to take a second and vote....comments are really appreciated....

34

Mamah bata bar gidan ba sai da ta tabbatar tayiwa Ameer wankin Babban vargo, shiru ya mata har ta gama kafin yace "Allah ya huci zuciyarki" ko kallonsa bata k'ara ba ta mik'e ta fice, haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ameer zaman sa da Afaf babu yabo ba fallasa, though gaisuwa kadai ke tsakaninsu, wata Ranar ya kwana a gidanta wata ran gidan Seemby buh she never cares, tafi danganta rashin kwanansa a gida da tight schedules na gurin aiki, Ana cikin haka kuma Afaf tayi noticing tanada ciki, sai da taje hospital tayi test da scanning ta tabbatar akwai cikin kafin ta shirya ta tafi gidan Maamah, tana sanar mata da maganar cikin Maamah ta mik'e da sauri ta dawo inda take tace "Are you serious dear?" Afaf tayi murmushi kafin ta fitoda takardan test ta bawa mamah, murna kamar zata kashe Mamah tace "Alhmdlh yanzu nasan nayi grandchild, kina ji yaushe kike da time muje China mu fara siyañ kayan baby, kinsan fa Wannan shine jika na farko a gurina gurin Alhj.Kuma na biyu so dole inji dashi" Afaf tace "Maamah ina ji dake nima Kuma ko yau kikeso sai mu wuce" Mamah tace "A'a ki fara tambayar mijin ki tukiun,ko har yanzu Baku shirya ba" da har Afaf za tace a'a sai ta tuna yanzu fa Ameer ya kusa dawowa na ta tunda tana d'auke da cikin sa,sai kawai tace "Maamah kinsan fa ban sanar da Ameer ba, nafi so ki masa alvishir da kanki shiyasa ma daga hospital ko gurin Ummi banje ba na tawo nn" mamah baki har kunne tace "Angama Zainab barima kiga" daga nn ta dauko wayarsa ta doka masa kira, time din suna tare da Seemby be iya ya d'auko wayar ba saboda yadda jikinsa yake a mace,sai Seemby ce tayi k'arfin hali ta miko masa duk kuwa da yadda gabanta ya fadi ganin sunan Mamah da tayi a ,a hankali yayi placing wayar a kunne yace " Mamah ina wuni" bata answer tace "Kana ina?ya naji voice d'inka ya canja?" Yayi saurin clearing throat d'insa yace "Ina office Maa wani Abu ne?" Da murna tace "Abun alheri ma kuwa kaidai maza ka tawo yanzu" da sauri ya mik'e ya wuce toilet, bayan ya shirya yace "Dreamboat tashi ki samarwa twins abinci, zanje naga Mamah" har a time din gabanta be bar faduwa ba, tunanin ta daya kar Mamah ta gane suna tare take Neman sa,da kyar tayi gathering courage tace "Ka gaida ta" daga nan yazo yayi pecking forehead nata ya shafa kan twins yayi gaba.Da sallama ya shigo parlour Afaf ta dinga masa wani murmushi shikam sai harara yake watsa mata yana wondering abinda ya kawota, Mamah ta washe masa baki tace "Sannu Dan alvarka,dole ma ka bani goron albishir Wallahi" yayi murmushi he's eager to hear from her yace "Ki fadi duk me kikeso after naji abinda zaki fadamin I promise to give you" tace "To rufe idonka" yayi yadda tace kafin tayi placing paper din test a hannunsa tana dariya, dariya yayi kafin ya bud'e idonsa, bata fuska yayi daya gama karantawa yace "What's my business with this?" Maamah ta masa dakuwa tana harararsa tace "Ban gane ba, matarka tanada juna biyu kace min haka" sai da ya mike yana gyara link yace "Allah ya raba lafiya I though it's something important kika kirani ina aiki na Bari na tawo" both Mamah and Afaf feel very disappointed, suka dinga harararsa,da sauri ya fice kafin Mamah ta tsaida shi,koda yaje gida ya gayawa Seemby farin ciki yaga tanayi yayita mata mugun kallo yace "Ke wai Meyasa bakida kishi ne?" Tayi murmushi tace "Duk Macen da Allah ya halitta ya saka mata kishi ae,is just that one has to control him self,idan mutum yace ze viyewa kishi Wallahi sai yayi kisa,but ina kishinka beyond your expectations, saboda ina Sonka" ya rungumeta sosai yace "And I love you more than you love me sweetheart".
After a week
Ameer yana zaune a bedroom d'insa na gidan Afaf ta shigo tana yatsina fuska, yayi mata kallo daya Kawai ya d'auke kai, a shagwabe tace " Ya Ameer am feeling hungry" ya mata banza ta daure ta kara cewa "Kuma ni wainar flour nake son ci" yace "To kici mana" duk kansa na kasa yayi maganar, ta harare shi tace "To ai kasan dai bana jin dadi bazan iya girki ba ko?" Yace "To ki cinye ni mana" a zuciye tace "Is that the way you're suppose to respond me?" A takaice yace "Fita" tsaye tayi tana karkada kafa kafin kuma ta fara dialing number Mamah da wayarta dake hannunta, sakin baki yayi jin tace,Hello Mama bake kika ce duk me nakeso in gaya wa Ameer Ba? Tayi Shiru kafin ta dora ,"to Dana gaya masa cewa yayi ko Zan mutu da yunwa vazai fita nema min abinci ba " a fusace ya mike tako fasa kara kafin tayi hanging wayar ta fice da sauri, Mamah ta kira yafi ten times buh batayi picking ba tafiso ta daga hankalin Mamah, da sauri Maamah ta zari veil d'inta ta fito sukayi kacivis da Daddy a parlour ta had'e rai zata wuce yace "Maryam ina zaki?" A takaice tace "Gidan Ameer" yace "You're going no where kin gane? So you better get back to your room" daga nan ya wuce room d'insa, tabe baki tayi ta fice da sauri kafin ya sake fitowa.ko sallama batayi ba ta fado gidan,Ameer ya mik'e da sauri yana Mata Sannu da zuwa,bata answer ba tace "Ashe so kake ka kashe min jika ko?" Yayi shiru ta Dora "Ameer ka kiyaye ni Wallahi" yace "Mamah kinsan ai ban iya girki ba ko?" Tace "to ba saika samo mata Wanda zata dinga mata girki ba, yawwa best solution kawai kaje ka dawo da matarka sai ta dinga mata abinci" yayi murmushi yace "Maa kiyi hak'uri Amma Matata ba me Aikin ta bace ko ta dawo bazata dinga mata girki ba sai dai Ku samo mata maid" baki ta saki kafin tace "Ai Shikenan Ameer baka isa kaga iyaka ta ba me aiki Zan nema mata ko 10 take so" shiru yayi kafin ya mik'e yace "Zan wuce company Maa Allah ya tsare hanya" sai da Mamah tayita bawa Afaf baki har ta hak'ura kafin ta tafi,washe gari ko maid tazo.
  

9months later.....

Ranar Saturday da daddare Afaf ta fara labour gashi Ameer yana gidan Seemby dakyar ta iya laluvo wayarta tayi dialing number Ummi, bayan tayi picking tace mata tazo,abun ya bata mamaki, Ameer is supposed to be at home by now, bayan Mamah ta tabbatar mata everything is okay between Ameer and Afaf amma yanzu 1;00am Ace baya gida,Abbah ne ya kaita gidan Ameer ta shiga da sauri ganin Afaf ta galavaita yasata saurin rungumota gurin mota, suna zuwa hospital aka karveta , Ummi gefe ta koma tayi dialing number Mamah ,tana picking Ummi tace "Gaskiya Maryam am really disappointed in you kika nuna min Ameer yana kula da Seemby Ashe karya ne? Yanzu gashi yarinya tana labour amma shi baya gida at this very hour" Mamah kunya da mamaki ya kamata tace "Yanzu Kuna ina inzo?" Ummi ta mata bayanin  hospital din kafin tayi hanging,tare da Daddy sukaje hospital din, fadi in fada suka dinga yi da Ummi har Doctor ta fito ta shaida musu Afaf ta Haihu, sai da aka kaita resting room da babe suka shiga, yarinya Masha Allah Kamar ameer Sam,Mamah a fusace tayi dialing number Ameer yana tsaka da bacci yaji ringing kamar bazai dauka ba sai yayi saurin dauka don kar Seemby ta farka,Mamah tace "To tabbatacce Mara mutunci ka same ni a Annur clinic Yanzu Afaf ta sauka" besan sanda ya wartsake ba though baya ra"ayin Afaf amma yaji dadi yayi babe, yana shirin tafiya Seemby ta farka,da mamaki ta dinga kallonsa tace "Sai ina?" Yace "Afaf ce ta Haihu Yanzu Zan tafi" taji wani mugun kishi Ashe Ameer yayi tarayya da Afaf sai ta kawar da Wannan tunanin ta mike ta wuce wardrobe ta Ciro hijab d'inta tana kallonsa tace "Muje" Sam ta Manta Mamah bata San suna tare ba sai a mota tayi recalling, tana kallonsa tace "Maamah fa bata San  muna tare ba" yace "Ba komai" yana shan corner din hospital d'in, A tare suka shiga room d'in bakinsu d'auke da sallama, Mamah da Ummi suna ganin Seemby a bayansa suka mik'e a razane, Mamah ta nuna ta da yatsa tace "na shiga uku ni maryam Yanzu Ameer Wannan tabbatacciyar yarinyar kazo min da ita?iyakata zaka nuna min? Oh yanzu na gane abinda yasa baka kwana a gida ba Ashe tare kake da ita ko?" Ummi ta karve zancen tace "To bakar kadara,annamimiya, sarakan bin voka, fice kar in figo ki in miki dukan kawo wuka" da sauri ta juya ya bita Mamah tace da sauri "Allow Allah ya isa idan ka bita" cak ya tsaya a gurin yace "Dan Allah ki Bari na bata ko kudin napep ne" tace "bakar zuciyarta ta me shegen naci ta maida ta" ita kam tana fita ta fara tafiya a kasa, horn din mota ne aka dinga Mata sauri ta kara mutumin motar ya fito yavi bayanta, kiris ya rage tayi ihu ganin ya taddata , yace "Seemby Lafiya na ganki a nan da tsakar Daren nan?" Ajiyar zuciya ta sauke ganin Ashe Sadeeq ne course mate d'inta a buk,da sauri ta shige motar suka var wajen a hanyar ta masa bayanin abinda ya kawota ta kara da cewa "shine zanje na tawo mata da kaya tunda Haihuwar ba'a shirya mata ba" dai-dai gidan ya sauke ta ta masa godiya ta shige.
A hospital kuwa Mamah da Ummi ba abinda basu ce masa ba kan Seemby zagi ko Seemby ba irin Wanda bata sha ba, shi kam ko hak'uri be basu Ba saboda sun bata masa rai, Babban tashin hankalinsa be wuce yadda Seemby ta fita da tsakar Dare ba, huduva yayiwa babe da suna  Maryam wato sunan Mamah kenan (wai Aunty masifa...yarinya ta taso da tsiwa).
Washe gari Mamah hana Ameer tafiya tayi don kar yaje gurin Seemby tunda ta fahimci auren su bame karewa bane, a takaice dai Seemby har bayan kwana 5 bataga Ameer ba sai dai time to time idan ya samu privacy yana mata message.
Ranar suna ba karamin shagali akayi ba,Munci uwar Oban savada, ga remgem ma mukayi Hani"an da ita....

*Kai Alhmdlh ansha suna*🤣🤣


Cute❤🔥

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now