Mowar miji (Borar Danginsa)

1.5K 87 2
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

Hey! Wattpadians please show me some love by voting and commenting💖
  Wattpad @ Zainab Yakasai

18

Number Ameer Maamah ta fara dialing sai taji a kashe, ta dinga Safah da marwa cikin dakinta, ita Ameer yake son tozartawa? Lallai zatayi maganinsa kuwa.... Ganin zama ba nata bane kawai sai ta dauki veil ta fito da sauri, a k'ofar parlour suka hadu da Amaal tana shigowa daga school, tace "Wuce muje ki saukeni gidan Hajiya Fateema" Amal da mamaki take kallonta tayi gaba abinta, sai da suka shiga mota suka hau titi Amaal ta kalleta tace ",Maamah lafiya kuwa" a takaice Maamah tace "Ba lafiya" Amaal ta rude sai tayi parking a gefen titi tace "Wani Abu ne ya faru Maamah?", shiru Maamah tayi mata da farko, ganin taki Jan motar kuma ta tsaya tana kallonta yasa tace "Ameer ne ya dauki shegiyar matarsa suka tafi honeymoon suka bar Afaf a gida, ko sallama basuyi mata ba" Amaal har cikin ranta taji dadin hakan, at least Simbiat zata samu peace of mind, gashi dama yanzu ba ita kad'ai bace, tana bukatar Hutu da kwanciyar hankali sosai, sai ta dake tace "To yanzu Maamah binsu zamuyi ko yaya?" Maamah ta kai Mata duka tace "Ah ubanki zamuyi, an taba tafiya U.S a mota ne" dariya Amaal ta dinga yi kafin taja motar sukayi gaba, har suka isa gidansu Mahmoud ba Wanda ya kara cewa kowa komai, Amaal na gama parking Maamah ta fice da sauri ta fada parlour, Hajiya Fateema ta mik'e a razane tana kallonta tace "Maryam lafiya kuwa?" ",Maamah sai huci take taki ko zama tace " Mahmoud yana nan kuwa?", Hjy. Tace "Yana side d'insa, bari Humairah ta kirasa" daga nan ta kira humairah tace ta kira Mahmoud, har a nan Maamah a tsaye take itada Hajiya, Amaal ce kadai a zaune, bayan kamar 2mnts humairah da Mahmoud suka shigo, har kasa Mahmoud ya durk'usa ya gaida Maamah, bata answer ba sai tambaya data watso masa "Ina Ameer yace maka zashi?" Ya dago da sauri yana kallonta yace "Ameer kuma? Baki gansa bane? Nikam rabona dashi kusan 4days fa, tunda yazo yamin handing over wani contract" harararsa Maamah ta dinga yi kafin tace "Ni zaku rainawa hankali Mahmoud? Wato yace karka gayamin shine zaka min karya?" Kan !Mahmoud ya kulle, yama rasa me zaice, shidai yasan iya gaskiyarsa kenan, bayan Wannan duk wani abu da ze fada mata karya ne, yayi shiru yana kallon Hajiyarsa data hade rai tana kallonsa, kafin yayi magana Hajiya tace "kai Mahmoud kasan duk nan ba sa'an ka ko? To ka fada mana inda yake" kamar zeyi kuka yace "Hajiya wallahi ban saniba, na fada muku 4days kenan rabona dashi", Hajiya ta kalli Maamah da tayi nisa a dream land tace " Nifa na kasa gane muku, wai Ameer din b'ata yayi kome?" Sai a nan Maamah ta zauna, ta fada Mata duk abinda Afaf tace ta kara da cewa "Fateema ni Ameer yakeson tozartawa? Afaf fa yar kanwata safiyya ne, Fateema inason safiyya sama da kowa da komai aduniya, ta zama gatana a lokacin dana rasa gata, duk kuwa da cewa nice yayarta" Maamah ta gyara zama tana kallon Amaal tace "Koda yake ba lefin Ameer bane, nice da ban taba nuna masa muhimmancin Safiyya ba, amma ko ba komai ai yasan darajarta a matsayinta na yar uwata ko?" Hajiya tace "haka ne" ,Maamah ta cigaba ...."1970 muka samu wani mummnan accident a garin gombe, mun dawo daga ganin Safiyya alokacin tana boarding school, Hajiya da Alhaji ko shurawa basuyi ba Allah ya musu rasuwa, sai ni kadai nayi ragowa da driver , inda na samu two fractures da dislocation a same leg, sai kuma muguwar buguwa da nayi a kaina, Wanda hakan yasani dogon suman da mutane sukayi zaton ko na mutu ne, da taimakon Allah da taimakon driver, na samu kaina a hospital, nasa wahala sosai don saida nayi jinyar wata shida, kuma duk wata shidan nan tare mukayi da Safiyya wadda Uncle dinmu ya d'auko a school, lokacin da akayi discharging dina, gidanmu muka koma daga mu sai maids da gate man muka dinga rayuwa, daga baya maids suka dinga tafiya ganin ba biyansu muke ba, lokacin ina level one a B.U.K, ni da kaina naje gidan Uncle Sadeeq na fada masa halin da muke ciki, na nemi ya bada wani Abu cikin kudin Alhajin mu mu nemi wasu maids din, Amma budan bakinsa sai cewa yayi ai dukiya bata Alhaji bace tasa ce ya bashi ya dinga business har karshen rayuwarsa, abun ya bani mamaki Uncle Sadeeq yamin karya, amma banida gut na karyata shi, sai kuma na nemi da mu koma gidansu mu zauna tunda zefi mana security, nan ya amince muka koma, amma ko wata bamuyi a gidanba, muka fara fuskanta banbanci ko dama can matarsa Aunty sa'adah ba sonmu da Hajiyarmu take ba, saboda Alhajinmu yafi mijinta kudi, ko abinci bata bamu isashshe, ga kyara da tsangwama, ganin har yanzu ban gama warkewa ba yasa Safiyya ta nemi Aikin da N.G.O, dakyar da taimakon Allah da taimakon wani El-mustapha course mate dina ta samu, ita ta dinga kula damu har na samu sauki nima ta bani kudi na fara business, Saida Safiyya tayi asarar shekara daya na makaranta, kafin ta shiga wani school din ta k'arasa SS3 d'inta, duk da ina samun kudi amma Safiyya bata bar kula dani ba,ganin cewa ta fini samu sosai, zaman gidan Uncle saida ya gagaremu muka koma dangin Hajiya a yola, bamu kara dawowa kano ba saida mukayi aure tukun, kuma har yau uncle Sadeeq be kara ce mana komai kan dukiyar Alhaji ba"
Daga nan Maamah tayi shiru tana wiping hot tears, Amaal da Hajiya ba karamin tausayi labarin ya basu ba suka dinga bawa Maamah hak'uri, sai bayan magrib suka koma gida.
   Mahmoud ko bayan ya koma side d'insa wayarsa ya d'auko ya fara Neman number Ameer ta Jordan amma bata tafiya, haka ma na Turkey dana San Francisco, yayi ta tunani to ina Ameer zashi? Florida! Florida ta fado masa yasan Ameer yana yawan zuwa Florida may be can ya tafi, amma kuma ai bazeje honeymoon can ba tunda aiki ke kaisa can, komawa yayi ya kwanta yana cewa Allah yasa ya nemeni koma ina yaje.

  The other day
    *Florida*

Ameer yana zaune yana aiki a system while Simbiat tana bayanshi a kwance, tunani kala-kala take,haka kawai sai ta dinga yi gabanta yana faduwa, tasan zuwa yanzu Maamah tasan basa nan, tunanin abinda zai biyo baya idan sun koma kawai take, batasan Ameer ya hauro kan bed din ba, sai ji tayi ya hura mata iska a face d'inta, ta mike zumbur har saida ta rik'e bayanta, da sauri shima yasa hannu inda tasa nata yace "Meyasa kike tunani haka? Kinga kinsa na tsorata ki ko?" Ta turo bakinta tace "Wai yaushe zamu tafi ne?" Ameer ya zaro ido yace "Madam yau fa kwananmu 2 kawai har kin fara zancen tafiya? Kin gaji ne? Oh I guess kinason yawo ne Ni kuma ban fita da ke ba, amma ki kwantar da hankalinki gobe as early as 7:00am zamu fita, I promise to take you different places, you'll learn that Florida yafi ko ina kyau a U.S" ta kwanta a jikinsa tace "Ni tsoro nake ji nasan Maamah tayi fushi damu yanzu, and gaskiya abinda muke Sam be dace ba, Afaf ma matarka ce Ameer, tanada irin hakkin danake dashi a gurin ka, amma Sam baka kula, na taba fadamaka kaji haushi, buh gaskiya ce dole na dinga fada maka as long as we're together I'll never stop from setting on a right path Ameer saboda in sonka banason ka shiga fushin ubangiji bayan na Maamah kuma, you've yo think, bakya kyautawa Sam" maganar Simbiat ta daki zuciyarsa sosai yasan Gaskiya take fada masa amma ya zeyi, ba yason Afaf bayajin ze iya kasancewa tare da ita amatsayin ma'aurata amma dai he'll try his possible best yaga ya fara kyautata mata in sun koma gida, zare Simbiat yayi a jikinsa ya fice reception ya zauna, he just need privacy, he wants to think..think .and think about abinda Simbiat tace,lallai yasan zuwa yanzu yana cikin fushin ubangiji....astagfirillah! Yace yana jingina da resting chair da yake kai, hade da lumshe idonsa ......


Cute💞

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now