mowar miji(Borar Danginsa) 28

1.2K 91 10
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

_Hey! Are you enjoying this novel?  Okay then... Take a second and vote, comments are really appreciated.... you can also follow me @Zainab Yakasai_

28

Rayuwa me dadi Ameer da Seemby suka dinga yi a daya gidan nasu, basuda sauran matsala saboda har Yanzu Mamah da Afaf basu gano inda Seemby take ba, a tunanin su ma Ameer ya maidata gidansu ne, shiyasa suka kwantar da hankali su,Ranar Afaf tana zaune a parlour shi kuma Ameer yana dining area, kullum yana zuwa gidan wata rana ya kwana wata rana kuma baya kwana, Amma har yanzu yaki sakar mata fuska tsakaninsu gaisawa kawai and nothing else, ta rasa yadda zatayi, wayarta ce tayi ringing, ta dauko da saurin ganin sunan Maamahn Ameer yasata murmushi, Ameer ya zuba mata ido, bata damuba tayi picking hadeda sallama, a daya bangaren Mamah tace "Ya ake ciki Afaf? Yarinyar nan ta dawo ko a"a?" Afaf ta saci kallon Ameer shima ita yake kallo, a hankali tace "shiru dai har yanzu ba labari" Mamah taji dad'i tace "Shi kuma fa, yana zuwa?" Ta sake kallonsa tace "Eh yanzu ma yana nan, ai kince ya fad'a miki a office yake kwana ko?" Mamah tace "Eh wai contract d'in Aikin flyover suka samu so they have to work over" Afaf ta gaji da idon Ameer, sai ta mik'e ta wuce room d'inta, Zumbur shima ya mik'e yavi bayanta, Fisge wayarta yayi yace "Gulmar Oban wa kike?" Afaf tayi kifikifi da ido tace "wai ina ruwan ka da ni? Ko tunda kazo ka kulani?" Ameer yaja kunnenta yace "ke wace irin yarinya ce? Kwata kwata bakida ladabi wallahi, a haka kike cewa kina sona bakya ganin girma na?" Sai Afaf ta marairaice, Anzo dai-dai wajen, tace "Wallahi ina son ka, I love you, I love you More than expectations, please give me a chance to show you the real love" Ameer ya saketa yana harararta yace "Bana bukatar hakan" daga nan ya fice a room din, Afaf ta fad'a kan bed tana tunani, bata San kuma ta yadda zata vullowa Ameer ba, ta nunawa Ameer soyayya amma ya kasa fahimta, wayarta ta dauko tayi dialing number Jimoh, ringing biyu  picking, tace "Hello babe ya?" Afaf taja tsaki tace "Ke dalla wace babe, Ameer yaki fahimta na, ,na rasa ta yadda Zan vullo mishi Dan Allah ki taimaka" Jimoh tayi wata shegiyar dariya, tace "Idan Jimoh tana nan Afaf bazata taba kuka ba, sai dai ayi mata, ganin zuwa" daga nan sukayi hanging.
30mts later, Ameer yana shirin tafiya wajen Seemby yaji tsayiwar mota, window ya koma,yana kallon Jimoh ta fito a motar yayi wani murmushi ya samu guri ya zauna, Turus Jimoh tayi da taga Ameer she never think zasu hadu, ta k'araro murmushi tace "Sannu da gida Ya Ameer" shiru yayi yana nazarinta kafin yace "me ya kawo ki gidan nan?" Ta fara kame kame "umm dama nazo gurin Afaf ne" "Sure?" Ameer yace, ta gyada kai tana murmushi, yace "When did you two become friends?, I never know, Ashe kina zuwa gidan nan" ta kara gyada kai tace "It has been long, nazo sau ba adadi ae, hadu wa ne bamu taba yiba" Ameer ya mik'e ya rik'e hannunta har bakin k'ofa, yace "Ashe tare kuke kullawa Seemby Kullalliya?" Shiru tayi sai dai Ameer ya karanci rashin gaskiya a fuskarta, yace "Wuce ki fita, kuma wallahi kar in kara ganin ki a gidan nan tunda Ke munafika ce, kuma Zan samu lokaci inje in samu Ammah na mata Bayaniñ komai" daga nan ya turata waje, yana juyawa sukayi four eyes da Afaf, tayi saurin komawa room d'inta tayi banging k'ofar, yaja tsaki kawai ya dau wayarsa ya fice a gidan.
Farm center ya wuce direct, be samu Seemby a parlour ba so also bedroom and this means tana kitchen tunda veji motsin ta a toilet ba, ta k'ofar bayan kitchen yaje yana lekawa ta glass tana tsaye tana Aikin ta, da alama bata San wani ya shigo gidan ba, Sai da ya vari  ta juya sannan ya bud'e k'ofar a hankali cikin sand"a ya shigo, caraf! Ya rungumeta ta baya, ta saki k'ara har saida ya tsorata ya koma baya da sauri, ta dade a tsaye ta runtse idonta, ganin haka yasa Ameer zagayowa gabanta ya rik'e hannunta yace "Am sorry bansan zakiji tsoro ba, ta fisge hannun tace " Dan Allah ka Dena min irin Wannan wasañ kasan fa inada matsalar Bp, Dan Allah ka Bari " ya kara kamo hannunta yace "Bazan kuma ba, ya kike, ya unborn twins d'ina?" Ta kwanta a jikinsa ta rungume shi tace "We're all fine and we missed you much" yaji dad'i yace "I know for sure, mezan samu?" Ta kara matse shi tace "Me kake so?" Yace "you! I just need you babe" sai da ta kashe gas tazo taja hannunsa zuwa room d'inta, suka zauna a bakin bed  tana korafi wai duk kayanta sun Mata yawa sai dogayen riguna take sawa kuma wasu ma sun d"age, Ameer ya zira hannunsa a cikin rigarta ya fara shafa cikinta, muryarsa har ta fara sarkewa yace "To meye a ciki tunda ba fita kike ba",Lumshe ido Seemby tayi tana enjoying duk abinda Ameer yake mata, a hankali ta fara maida masa martañi, har dai Ameer ya samu yadda yakeso.

A month later

"Dreamboat mana! Inaso inje bikin nan Wallahi, please ka vari naje Allah Zan nitsu", cewar Seemby tana Jan Ameer dake kwance ya rufe idonsa, be bud'e idon ba yace " Dan Allah kiyi hak'uri babu inda zaki Allah Wannan month din EDD din ki ne fa dole bazaki dinga bawa kanki wahala ba " Seemby ta bata fuska kamar zatayi kuka ta dora kanta a kirjinsa tace "Inji waye yace an fiso a zauna guri daya, mace me ciki ai anfi sonta da exercise, most especially wadda ta kusa haihuwa" yana wasa da gashin kanta yace "To naji amma nafi son kiyi exercise a gida, ni Zan kira wata Nurse Shukrah Dana sani a gurin Dr.haiydar sai ta dinga guiding dinki kina exercise d'in" Seemby ta tashi ta fara kawo masa duka "Ni Allah bazan yarda ba, kar Kuma ka kiramin ko wace mace Allah", Ameer yaja hancinta yace "Sarkin kishi kawai", rik'e hannunsa tayi ta Kai bakinta ta fara tsotsa, Ameer ya lumshe ido, unexpectedly ta kasa masa cizo, ya fisge hannun yace " Ah babe you Hurts me " tayi rolling eye balls d'inta tace "This should be your punishment duk sanda ka kara kawo min maganar mace", " Allah ya baki hak'uri " yace, kafin ya mik'e ya dauko nail cutter yazo ya fara cutting mata grown nails d'inta.

2 months later

Yau ne Expected date of delivery na Seemby ya fara, Ameer har yaje office ya tuna, ya mik'e da sauri ana tsakiyar meeting,Duk aka zuba masa ido, be damu Ba ya fice a office din da sauri, yana zuwa gida yaga Seemby a tsaye tana yatsina face, ya rikota yace "Sannu babe gaba daya na manta yau EDD dinki ya fara, ya kamata muje hospital" tayi murmushi tace "Kalau nake ai, vasai mun je ba" ya shige room yana cewa "Yarinya ko kalau kike dole muje hospital ko ba yau zakiyi delivering ba, zasu baki bed rest", already dama Seemby ta had'a duk kayan da zasu bukata a akwati don haka box din ya janyo ya dauko mata hijab ya wuce da kayan mota kafin yazo ya dagota a time din Wannan ruwan ya fara fita a jikinta don haka da sauri ya sakata a mota, suka kama hanyar AKTH,tun kafin suyi nisa Seemby ta fara kuka tana kiran Ammi, Ameer duk ya rude sai ya karanto addu'a ya juyo ya tofa mata.
Gaba daya dabara ta kwace masa ya rasa yadda za'ayi, Kawai sai yayi dialing number Mamah, har ya fidda ran zata dauka sai kuma yaji tace "Ameer Lafiya" yace "Ba Lafiya Mamah muna hanyar AKTH Seemby zatayi delivering" Jim Mamah tayi kafin tace "Allah ya sawwake" daga nan tayi hanging Ameer Sam beji dad'i ba ya leka Seemby da take sauraron su don wayar na hands free ne, itama shi take kallo, a tare suka d'auke kai, ya sake dialing number Maamah, tayi picking tana cewa "Meye Kuma?" Yace "Wai da cewa nayi ki tawo pls" tayi dariya "Ashe inada amfani Ameer? Sau nawa ina saka maka doka kana tsallakewa saboda ka isa? Saboda haka ni yanzu inada inda sani sai..." Yayi saurin katse wayar, dai dai nan kuma suka shigo hospital, Nurses ne suka shiga da ita dakin haihuwa, ya shigo shima ya rik'e hannunta gam, a Hankali tace "Ka kira min Ammi na please" ba musu ya dauko wayarsa yayi dialing number ta, kamar jira take tayi picking dama tana Sane da cewa yau EDD din Seemby ze fara, tace "Seemby ba lafiya ko?" Sai da yayi murmushin da zata iya jiyowa don bayason ta damu yace "she's fine amma myna hospital zata Haihu" bata jira jin komai ba tace "Gani nan tawo wa" tayi hanging. Bayan Yan mintuna kuwa sai ga ta, a time din Seemby ana can ana cin kwakwa.
A daya bangaren Maamah tayi dialing number Afaf, tana picking tace "Afaf naga matar Ameer zata Haihu ke Kuma Ba labari" Afaf tace "Yo ya taba kwana a room d'ina ne?" Mamah tace "Bangane ba" Afaf ta marairaice tace "Ni Ba abinda ya taba had'a mu dashi" Mamah ta dafe kirji tana salati tace "Me yasa baki taba gaya min ba?" Afaf tayi shiru, Mamah ta Dora " Shikenan Karki damu idan be baki Bebe ba zai baki takwara ai" Afaf tace "kamar yaya" Mamah tace "Idan matar ta Haihu sunan ki za'a saka".....




*Tab! Wai sunan Afaf sai kace ita tayi mata nakudar, me Kuke gani*


Cute❤

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now