Mowar miji (Borar Danginsa)

1.2K 69 3
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

20

Sai 10:00pm suka koma hotel, Simbiat ta haye gado ta kwanta hadeda lumshe ido tana tuno abubuwan da suka faru a ranar, she really enjoy the day, Ameer ma gadon ya hauro ya kwanta hadeda janyota jikinsa yace "Baza kiyi wanka ba Babe? You most be tired, in kinyi wanka zaki d'anji dadi" Simbiat tayi murmushi tareda kissing lips d'insa tace "Zanyi mana, amma gobe ma zamu fita ko?" "yes" Ameer yace yana sauka a gadon, toilet ya wuce ya had'a musu ruwan wanka, yazo ya dauki Seemby kamar babe ya shiga da ita......bayan sun fito sai da Ameer ya musu oder cake da smoothie, da kansa yayi feeding d'insu, bayan sun kwanta har Simbiat tayi bacci wayar Ameer tayi ringing, yasha mamaki ganin number Mahmoud, kamar bazeyi picking ba, Sai kuma ya mike ya fito daga room d'in, kasa ya sauka ya zagaya garden ya zauna bakin pool yana dialing number Mahmoud din, bayan Mahmoud ya dauka gaisawa sukayi, Mahmoud yace "Ameer meke damunka ne, ka kama ka tafi kabar Afaf, to wallahi Mamah har gida tazo ta dinga fad'a" dariya Ameer ya dinga yi, lallai Mamah tanada k'arfin hali, Mahmoud yaji haushi sometimes Ameers use to take things for granted, Amma wannan issa serious case tunda Maamah taji haushi, kuma ai isn't proper Ameer ya tafi without her knowledge, tsaki Mahmoud yaja yace "Look Ameer, you have to come back home, ran Maamah ya baci sosai fa" murmushi Ameer yayi wannan karon yace "Mahmoud zamana acan yafi, Maamah bata barina na samu peace of mine a gida ka sani,so also Afaf she's always creating problems, batason zaman lafiya tsakaninta da Simbiat" shiru yayi kuma yana jiran me Mahmoud zece, Mahmoud ya numfasa yace "Haka ne, buh at least you have to let her know you're going somewhere, bawai ka tafi ka barta cikin tunani ba, hankalinta ya kasa kwanciya, yanzu haka bata San inda kake ba...."  "Wait....so Maamah bata San inda nake ba? Please Mahmoud don't let her know,Simbiat tana bukatar kwanciyar hankali, kuma kasan bazata samu a gida ba, buh anan Alhmdlh tana samun kulawa", Mahmoud ya daga kafada, yasan gaskiya Ameer ya fada, Amma dole ya sanar da Maamah ya samu Ameer a waya, ko zata samu peace of mine,hanging yayi ba tareda ya kara cewa komai ba.
Da yamma Mahmoud ya shirya ya wuce gidansu Ameer Maamah tana zaune a parlour as usual tana kallo, Amaal kuma tana solving wani a problem, zama yayi a kasa, a ladabce yake gaida Maamah, ta answer ba yabo ba fallasa, ya nisa yace "Maamah dama zuwa nayi na fad'a miki na samu number Ameer na U.S"  a tare Mamah da Amaal suka dago suna kallonsa, Maamah ta kasa fahimtar halin data shiga a lokacin murnar an sameshi ne ko yaya? Yayin da Amaal takaici ya cikata, ta dade da sanin Ameer yana Florida, Seemby ta fad'a mata Amma bataso Maamah ta sani, shikuma wannan yazo ya b'ata plan d'inta, ta dinga wurga masa harara kasa-kasa, k'arfin hali Maamah tayi tace "Mahmoud nagode,zan kirashi yanzu" godiya shima Mahmoud ya mata ya mik'e yana kallon Amaal yace " 'yan Mata ya dai?" Tayi potting mouth ba tareda ta kalleshi, yayi murmushi ya fice.
Maamah ta kalli Amaal tace "Ke miko min wayana na kira d'an banzan yaron nan" Amal ta marairaice tace "Maamah Dan Allah ki barsu suyi koda week ne sai su dawo, kinga Aunty Seemby wannan ne zuwanta na farko" harara Maamah ta watsa mata tace "Munafika kawai, ai dama na dade da fuskantar kinsan inda yake tunda naga baki damuba,ido kawai na zuba miki....zaki tashi ki dauko min ko inje da kaina?" Jiki a sanyaye Amaal ta tashi ta wuce stairs.
*Florida*
Ameer ya fito daga toilet yana goge jikinsa da towel, bed ya k'araso yana kallon Simbiat data k'ura masa ido kamar meson gano wani Abu ya daga mata gira yana murmushi yace "Yadai?" Murmushin itama ta mayar masa tace "You look cute when you smile" ya sake murmushin yana dagota zuwa jikinsa yace "And you're looking gorgeous when you're sleeping" taji dadi ta fara blushing, ya dinga mata dariya wai harda rufe face d'inta, ya sunkuya yana kissing forehead d'inta yace "kiyi sauri kije kiyi wanka,don in na rigaki shiryawa ficewa zanyi na barki" ta narke masa tana shagwaba tace "Allah inka tafi ni kuma Nigeria zan gudu" ya mik'e ya dagata cak ya kaita toilet yace "Ayi wanka Lafiya" ya fito, a gurguje ya shirya don yau yanaso su kaiwa Imraan ziyara, tun randa sukazo rabonsa dashi. A gurguje yasa itama Simbiat ta shirya, dake ana sanyi baby pink colour sweater har ta wuce mata gwuiwa ta saka da wani skyblue pencil jeans, sai pink shawl datayi rolling kanta dashi, Ameer sai kod'a kyanta yake, though bawani heavy makeup tayi ba Amma ta mugun yi masa kyau, Sai da yamata pictures kala-kala sannan suka fito, hannunsa cikin nata suka fito a hotel din, taxi suka hau Ameer ya masa bayani yanaso ya kaisu *Bendervil Beach*,dake cikin kissemme ne basuyi wani tafiya me nisa basuka k'arasa, awww....Simbiat ta dinga jin dadi ganin different types of birds da tayi, beach din issa White sand beach, shelling and paddleboarding is one of the activities to be enjoy at that beach, Simbiat ta tsuguna ta zira hannunta cikin beach din tana wasa da ruwan while Ameer yana tsaye yana mata snapping pictures, kafin daga baya ya dawo suka da ita suka fara selfie, basu wani Dade ba kuma suka wuce *AMC Disney spring*, Masha Allah Simbiat taga different abubuwa, da hau lilo kala-kala irin su seesaw and the rest, daga nan ma Museum  suka wuce taga kayan tarihi kala-kala, Ashe suma turawa suna ajiye kayan tarihi, ta dinga mamaki?, bayan sun bar gurin hanyar gidan Imraan suka nufa, suna cikin taxi wayar Ameer tayi ringing, ya Ciro da sauri,he's expecting kiran Imraan dama, duuumm kirjinsa yayi wani mugun bugawar daya sashi dafe side d'in zuciyarsa, Simbiat ta dinga kallonsa tana mamakinsa, ta Dora hannunta kan nasa daya kuma a bayansa tana shafawa, da kyar tace "Heartthrob lafiya, wa ya kiraka?" Ya kakalo murmushi bayason ta damu yace "Karki damu kawai". Mamah ganin ta katse be dauka ba bae hanata cigaba da kiran saba, hankalinsa ya tashi sosai, yace driver ya kaisu  *Ramada by Wyndham kissemme downtown hotel*, Seemby ta kalleshi tasan, something is happening bayason dai fada mata ne, haka kawai taji gabanta na faduwa.sai da Ameer ya tabbatar hankalin Simbiat ya kwanta sannan ya sulale ya bar dakin bayan ta shiga toilet, garden ya k'arasa gabansa na faduwa ya fara dialing number Mamah, tana fara ringing ya katse da sauri,baze iyaba! Baze iya kiranta yanzu ba, musamman ma da akace ranta a bace yake dashi, yana kallo wayar tanata ringing be dauka ba, jin karar shigowar message yasashi saurin daukar wayar, ae saida zuciyarsa ya kusa fashewa saboda Abinda ya gani *Ameer ko ka dawo Nigeria gobe ko kuma na tsinema kazama abun kwatance, mutane su dinga tirrr da d'a irin ka, wadanda Allah be bawa haihuwa ba su dinga hamdala su fara tunanin wata haihuwar ba alheri bace*, yana gama karantawa ya ajiye wayar hadeda dafe kansa dake juya masa, yafi k'arfin 30mnts a zaune kafin ya mike ya fice daga hotel din gaba daya.....

Cute💖

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now