Mowar miji (Borar Danginsa) 23

1.4K 87 24
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab Shukrah😍

   _Don't forget to votes and comments if you really like the story_
    _This is one of my favourite chapters... Enjoy it please.... Ghen ghen ghen_

23

Washe gari tare Simbiat suka fita da Ameer, gidan Ammi ya kaita, murna kamar zatayi me, Ammi dake kitchen tayi saurin fitowa tana dariya tace "A'a Simbiat ce a gidan namu kuma da sassafen nan?" Seemby ta turo baki tace "Kai Ammi gidanku ko gidanmu? Gidan fa Abbah nane" Ammi ta rik'e baki tace "Lallai Seemby abun harda gori" ta karashe tana zuwa gaban Simbiat, dariya Simbiat tayi ta rungumeta tace "Ba gori nake miki ba Ammi na,kece naga kamar kina mamakin ganina,to ba wani matsala bane, Ameer ne yace tunda muka dawo sau daya nazo ya kamata nazo na yini" cireta Ammi tayi daga jikinta tajata ta zaunar da ita kan kujera tace "Masha Allah haka nake son ji, sai dai kinyi sa'a Rahienert ta tafi Lagos jiya" Simbiat ta zaro ido tana mamaki tace "Ah haba, amma Rahienert ko ta fada min? Kuma fa munyi waya jiya ma" Ammi ta wuce kitchen tana cewa "Ai tace batason gaya miki yanzu ne, cards kawai zaki gani, kinsan saura 2weeks bikin Aneesah" Seemby tace "Nidai Ammi gaba daya kun wareni gefe bakwa gayamin komai ko? Nayi fushi Allah" Tea da pancake Ammi tazo ta ajiyewa Simbiat a gabanta tana dariya, tace "Ya babyn?kina cin abinci kuwa? Hope kunyi scanning?" Kunya duk ta rufe Simbiat sai kawai ta kwanta ta juyawa Ammi baya harda rufe fuska, Dariya Ammi ta dinga yi, kafin ta mike ta wuce room d'inta, sai da Seemby ta tabbatar Ammi ta shiga room d'inta sannan ta tashi ta fara shan tea tana kallon Television.
   Gaba daya ranar hira sukayi tayi da Ammi, amma Sam Simbiat bata fadawa Ammi matsalarta ba, though Ammi tasan tanada damuwa don ta karanceta gaba daya, ta kara sanyi sosai duk da dama can tanada sanyin, Sosai ran Seemby yayi fari ta dinga jin kamar kar ta koma gidan Ameer, amma tasan hakan ba me yiwuwa bane. Sai 6:00pm Ameer yazo ya dauki Seemby, a Maroosh suka tsaya ya siya musu cake da ice cream suka wuce gida.
Washe gari as early as 6:00am duka mutan gidan Ameer suka tashi harda Afaf, tazo ta kame a parlour tana kallonsu daya bayan daya sunata zirga zirga bak'in ciki kamar ya kasheta ganin yadda Ameer yaketa wani lallaba Simbiat, dining area suka wuce Seemby ta zubawa Ameer fried sweet potato and sauce da kunun tsamiya, ya zauna yana mata murmushi, zama itama tayi tana mishi hira har ya gama, wall clock ya kalla 7:20am ya tuna yanada wani contract da ze karba yau, dole ya fita da wuri, da sauri ya mik'e ya mikarda Seemby ya rungumeta yana shafa lips d'inta, yace "Babe zan wuce, kimin addu'a" tayi masa murmushi me kyau tace "Allah ya kiyaye hanya" ya answer da "Ameen"  kafin yayi mata light kiss a forehead da lips d'inta ya saketa da sauri ya fice. Yana fita tazo da sauri ta wuce upstairs don tasan in ta tsaya Afaf bazata barta haka ba saita zagar mata iyaye.
Karar wayar Afaf yayi dai-dai da fitowar Simbiat, tayi saurin d'auka ganin message daga Jimoh ba k'aramin faranta mata yayi ba, ta karanta kusan 4times tana murmushin mugunta, ganin Simbiat ta fito daga kitchen yasata kyalkyalewa da dariyar mugunta, Simbiat duk sai ta tsargu ta fara bin jikinta da kallo, meye abun dariya a jikinta to? Ta tambayi zuciyarta sai duk jikinta ya mutu ,ita da kanta tasan  Afaf tanada kirki kawai bak'in kishi ke damunta, Sam batajin dad'in irin zaman da suke, kuma rashin kula Afaf da Ameer keyi ma ba k'aramin damunta yake ba ,to meyasa ma familynsu bazazu k'i taba, an fifitata kan 'yar uwarsu , a hankali taja  k'afarta ta koma d'aki , bakin  gado ta zauna tana tunanin makomarta, wannan auren Sam baya mata dad'i wallahi soyayyar Ameer kad'ai ke zaunar da ita gidan, amma da tuni anyi ba ita, tanason Ameer batajin ko Ammi zata iya rabata dashi...amma Afaf also needs his love and care , tasan bata isa tasa Ameer yaso Afaf ba ,bama tada courage din  sake tunkararsa da batun a karo na biyu kawai sai ta fashe da kuka, ya ilahie! Ya zatayi da ranta. Afaf kam dialing number Jimoh ta fara, Jimoh tayi picking da sallama kafin tace wani abun Ameer ya shigo parlour da sallama tayi saurin katse wayar ta bishi da murmushin mugunta, shi kansa yayi mamakin wannan murmushin amma sai ya Fuske ya aje wayarsa kan centre table kawai ya wuce room d'in Simbiat, a fili Afaf tace Alhmdlh ta d'auki wayar da sauri har rana cin karo da tea flask, bata  damu da ruwan zafin daya zube mata a k'afa ba ta shige room d'inta da gudu jikinta har rawa yake ta shiga messages d'insa, sai da ta toshe bakinta don kartayi ihun murna , ta samu abinda take so ...account number d'in Simbiat kenan Ameer yamata transfer kud'i last week, bata b'ata lokaci ba ta fara duba account balance d'insa 5.8mil. Masha Allah, toilet ta shiga tayi banging k'ofar harda saka key, duk Kudin account din tayi transfer zuwa na Simbiat... Takoyi babbar sa'a don wayar Simbiat a kashe yake ,ta fito ta boye wayar cikin kayanta ta dawo parlour ta zauna kamar wani abun be faru ba. Har Ameer yayi nisa a titi ya tuno wayarsa ...ina  ya barta? Dakin Simbiat zuciyarsa ta fada masa yayi saurin juyawa don yanada  amfanin da zaiyi da ita...da sauri ya shigo parlour Afaf ta bishi da harara ...Simbiat na toilet ya mata knocking yana cewa "Love ina  kika ajemin wayana sauri  nake" tace "wayarka kuma? Nikam banga wayarka ba...anya ma kazo da ita room d'innan ?" Ya dafe kansa yana kallon wall clock yace "Kan bed d'in ki na ajiye Simbiat" tace "Gaskiya ban ganiba" tana daga cikin toilet d'in, Sam be tuna parlour ya barta ba ya fito kawai ya wuce office. Da gudu Afaf taje ta d'auko wayar ta shige room d'in Simbiat, da kanta tace a ranta Gaskiya inada sa'a danko bata sameta a room d'in ba,ta boye  wayar a bedside drawer harda saka key ta fito da saurin dai-dai nan Simbiat ta fito daga toilet... Indai ba gizo idonta yayi Mata ba tabbas Afaf ce ta fita daga room d'in, ta shiga bin ko Ina da kallo ganin bataga canji ba yasata d'aga  shoulders d'inta kawai ta wuce closet don shiryawa.
Sai 4:00pm Ameer ya shigo gidan room din Seemby ya wuce kai tsaye a time din kuma ita tana kitchen, fitowa yake k'ok'arin yi idonsa yakai kan wayarsa dake kasan table din dake tsakiyar room d'in, ya fara murmushi lallai Simbiat wannan wani irin wasane? Dazu yanada abinda zeyi da wayar tace bata room d'inta, dama shi yasan kan bed d'inta ya bar wayar, ya dau wayar ganin tarin message's yasashi saurin fara dubawa, yawanci daga company ne, sai kuma yaga wani da G.T Bank, dubawa ya fara, duumm! Kirjinsa ya bada wani sauti ya zaro ido yana dafe kirjinsa yace "What?Seemby? Meyasa tayi haka?me zatayi da kudi meyawa haka? Meyasa bata tambayeshi ba tayi transferring duk kudinsa to account d'inta? A lokaci daya yake jerowa kansa wadan nan tambayoyin, yana k'ok'arin fitowa a room d'in Seemby ta shigo, ta wara ido tana masa murmushi tace " Bansan ka shigo ba" ganin yadda idonsa ya kada ya koma ja yasata zuba masa idonta sosai tana kallonsa babu annuri ko kadan a face d'insa, kawai sai taji gabanta ya fadi, jiki a sanyaye ta k'araso inda yake, ta kai hannu zata ta bashi yayi saurin matsawa gefe, a hankali yace "Where's your phone" tayi mamaki me hakan ke nufi?  Batada gut din cewa wani Abu kuma, haka taja kafarta dakyar ta wuce wardrobe, nan take ajiye wayarta don bata wani dameta ba, in kaga ta d'auko to wani muhimmin kira zatayi, dauko wayar tayi ta miko masa ta tsaya tana kallonsa, da kansa ya kunna wayar aiko sai ga alert ya shigo, ya bud'e da sauri yana dubawa, ya ilahie! Ya dafe kansa daya mugun Sara masa lokaci daya kuma yaji kirjinsa ya buga, numfashinsa ya fara yin sama, ya zauna gefen bed yana kara rik'e kirjinsa yana kokawa da numfashinsa, ai da gudu Seemby ta k'araso ta rik'e shi har ta fara kuka, ta dinga shafa kirjinsa tana tofa masa duk addu'ar da tazo bakinta, ture hannunta Ameer yayi, har sai da tayi baya ta bugi bedside drawer wayarsa da tata suka zube k'arasa, ta bisu da sauri ta dauko, idonta ya sauka kan message din dake kan wayarta alert na 5.8million naira daga gurin Ameer? Ta zaro ido tana dafe bakinta, irin wannan message din ta gani jikin wayar Ameer, anyi transfer 5.8mil. Zuwa account d'inta.zuciyarta ba karamin bugawa take ba ta fashe da kuka, sai yanzu ta fahimci abinda ke faruwa, ba Ameer yayi mata transfer kudi ba haka ma ba ita tayi ba, to waye? afaf? Tabbas Afaf ce , sai yanzu ta tuno time din da ta fito wanka taga Afaf ta fice a room d'inta da sauri, ta fashe da kuka, ko Ameer ze kasheta koda kuma hakan ze kawo karshen zamansu bazata fada masa Afaf ce ta k'ulla wannan sharrin ba, don ko na komai Afaf yar uwarsa ce, yin hakan ze iya zama silar rugujewar zumuncinsu. Ganin jini na fita ta hancin Ameer ba karamin daga hankalin Simbiat yayi ba, ta dinga jijjigasa tana kuka, batada k'arfin d'agashi bare su tafi hospital, Mahmoud ya fado mata, jikinta har rawa yake ta dauko wayar Ameer ta kirasa, Dan da nan ko yayi picking ta fada masa yayi sauri yazo Ameer ze mutu, daga nan tayi hanging.
Befi minti 10 ba sai ga Mahmoud ya shigo gidan, da gudu ya haura stairs ya shige room d'in Ameer, sosai shima hankalinsa ya tashi ya dagashi da sauri ya sauko haka ma Seemby hijab kawai ta zira ta biyo bayansa,mota suka shiga a tare ya ajiye Ameer a baya inda Simbiat ta shiga itama, Mahmoud ma ya zagaya ya shige driver sit yaja motar da gudu suka bar anguwan, Aminu kano suka wuce, Doctors suka karbe da sauri aka wuce emergency dashi, T.P.R&BP test aka fara masa ai kam blood pressure d'insa really rise, both systolic da diastolic sunyi rising, Doctors sun sha mamakin irin wannan hawan jinin, don yana faruwa ne normally ga person in shock, may be mutuwa akayi masa, haka suka dinga tunani, Simbiat kam tunda akace hypertension din ze iya taba masa zuciyarsa, ta dora hannu aka ta dinga ihu, Mahmoud kansa ya daure gaba daya, rannan Simbiat ce ke hypertension yau kuma Ameer? What's happening? Bashida answer shiyasa ya matso kusada Simbiat ya fara bata hak'uri, amma ko kallonsa batayi ba ta cigaba da rusa kukanta.
Sai 8:00pm Ameer ya farka har a time din Simbiat bata zauna ba, Mahmoud kam yana gefen bed yana kallonsa, Da salati Ameer ya farka ya fara waige-waige, idonsa ya fada kan Simbiat data zuba masa ido, yayi saurin d'auke kai, ya Kalli Mahmoud ya sakar masa murmushi, Simbiat jiki a sanyaye ta k'araso jikin gadon ta dafasa tace "How are you feeling now?" Ya cire hannunta a jikinsa duk da bashida kwari sosai hakan be hanashi masifa ba, a tsawace yace "karki kara tabani, and you get out from this room right now" ya k'arasa yana nuna mata kofa, tace "Dan Allah kayi hak'uri, wallahi is not my fault" ya watsa mata harara yace "I don't care,all I want is you get out yanzu, kuma ba gidana zaki wuce ba ki tafi gudanku" ba Simbiat ba har Mahmoud sai da maganar ta daki zuciyarsa ya mike da sauri yana kallon Ameer daya juya baya,Simbiat ta fashe da kuka ta fice daga room d'in da sauri tayi banging k'ofar......



*Ya ilahie! Ameer me kake haka? Simbiat ce fa, your only source of happiness, your life, your love ...your everything, a mother to your Babe*
   Wayyo Seemby kiyi hak'uri
😥😥


Comment pls
Your comments will really encourage me, it'll give me strength really

Cute😍💖

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now