Mowar miji (Borar Danginsa)

1.6K 80 3
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍


05

Dai-dai sanda  Ameer ya fito daga toilet Maamah ta shigo tana binsa da harara tace "Ameer yaushe na fara wata sa dai wai?" Yayi k'asa da kansa kawai dan yasan yayi lefi, ta k'arasa taja right ear d'insa tace "bance maka Afaf tana Neman ka ba,shine kabarta tana zaman jiranka? Tanada gurin zuwa fa amma ta zauna jiranka ka b'ata mata lokaci ko?" Ya marairaice yace "Maamah ni inason Afaf ta gane  niba yaron ta bane,ya zata dinga nunamin isa kawai saboda tanada ke! Nima fa inada abunyi ya za'ace sai naje na saurari shirmenta aurenta takeson nayi nace na amince just for you Maamah ya kamata ta kyaleni innaji ra'ayin ganinta I'll surely go for her ba saita Nema ba" Buge bakinsa Maamah tayi cikin b'acin rai tace "kaga Ameer idan ina magana kana mayarmin zan mugun b'ata maka,Afaf tanada ni of course nikuma na isa da kai right? " yayi nodding kansa tace "To ka shirya kaje ka sameta yanzu inba haka ba wallahi na lahira sai ya fika jin dad'i useless kawai" ta sakeshi ta wuce abinta. Dafe kai kawai Ameer yayi tunda bashida zab'i Maamah ta isa kamar yadda tace, ahankali ya mik'e ya shirya ya d'auki car key d'insa ya fice saidai ya fara lekawa side d'in Maamah ya mata sallama don ta tabbatar zaije kafin ya fice a gidan. A week din kuwa kamar yadda Daddy yace suka fara nemawa Ameer aure ,gurin Air Marshal Abdur-razaq suka fara zuwa wato mahaifin Afaf yaji dad'in maganar kawai ya kira Uncles d'inta suka tsayar da wata biyar a matsayin lokacin auren, koda sukaje gidan Me iyali ma wata biyar d'in suka tsayar, nan da nan aka fara shirye-shirye on both sides, Maamah da kanta ta shirya ta tafi Dubai ta had'awa Afaf kad'ai lefe na gani na fad'a don akwati 24 tamata  wato 2dozen , sosai Ameer yaji haushi amma bashida yadda zeyi da Maamah don son Afaf a cikin jininta yake bayajin ko Amaal tanama irin son da takewa Afaf, kasancewar yanada aiki da yawa a company kuma bayason barwa wani yasa ya tura Umaimah ( k'anwar best man d'insa ce  Mahmoud) can England ta had'o wa Simbiat Lefe 1dozen ammafa duk kayan ba na banza. Biki ya rage saura one month amma Ameer be cewa Afaf komai ba, da daddare ta sami Ummi a room d'inta ta marairaice tace " Ummi Ameer baya sona da yawa haka? Har yau bece komai ba gashi saura one month " Ummi ta janyota jikinta tace "Afaf ko Ameer yak'i Allah yak'i uwarsa sai ya aureki wallahi, karki soma min asarar hawayenki kinji ko" Afaf ta daga kanta kawai tana k'ara lafewa jikin Ummi.....Ummi ko waya ta d'auko tayi dialing number Maamah rai a bace ...Maamah na picking Ummi tace " Yaya Maryam kuzo Ku karb'i kayanku Afaf ta fasa wannan auren" cikeda b'acin rai da mamaki Maamah ta zaro ido kamar tana gaban Haj.Safiyya tace " Me yayi zafi haka sister? Ina Afaf d'in bata wayar pls inji menene matsalar" Dan tsaki Ummi taja ta sawa Afaf wayar a kunne ,Afaf tayi k'asa da murya yace "Maamah" Maamah a rud'e tace " lafiya Afaf ? Ameer ya miki wani abun ne?" Afaf ta fashe da kuka tace " bashi bane tunda akasa ranar auren be tab'a Nema na ba,ni na Dena sonshi ma" Maamah tace " Haba dai Afaf bazaki dena sonshi ba  indai  Ameer ne nice maganinsa ki barni dashi har k'asa zansa ya baki hak'uri kinji? Yanzu kina wani Abu ne?" "A'a" Afaf tace " yawwa kiyi maza ki shirya kizo Ameer ya baki hakuri" Maamah tace ,da sauri Afaf tayi hanging ta fad'awa Ummi yadda sukayi ta mik'e da dan gudunta ta shige room.
Maamah kam Afaf na hanging tafara Neman wayar Ameer yayi picking da ladabi yayi mata sallama, bata answer ba tace "kana jina Ameer duk me kake ka aje kazo gida yanzu ina nemanka"  ya zaro ido yace "Maamah meeting zanshiga yanzu contract d'in nan dana  dade  ina Nema ne ya samu" taja tsaki tace "And so fucking what? Will you come or I should come?" Besan yadda akayi ba kawai jin wasu  zafafan hawaye yayi suna sauko mishi yace da sauri "No Maamah you don't have to... Am on my way" da sauri ya fito office din suka kuwa karo da Mahmoud, ya mik'a masa hannu kawai Mahmoud ya rik'e yana examining face d'insa ,ransa a bace yake to meya faru? , k'ok'arin zare hannunsa yayi Mahmoud ya damke sosai yace "Meya faru" ya lumshe ido kawai yace "Mahmoud you should take over everything, the meeting is starting 12:00pm and saura minti 4 ma,I don't thing I'll be there" Mahmoud kallonsa kawai yake yace "Kai Ameer giya kasha kome? Contract d'in da kake Nema 5yrs back sai yau Allah ya baka kace zaka tafi bazaka zauna ba"  murmushin k'arfin hali kawai yayi yace "Maamah ke Nema na ,I have to go" ya zare hannunsa kawai ya wuce shi, har ya fice daga company Mahmoud kallonsa yake da mamaki kafin ya girgiza kai kawai ya wuce.
Kusan tare suka shigo gidan da Afaf ,tayi parking kusada inda yayi ko kallo be isheta ba ta wuce shi balcony yana magana da Tj , Maamah na parlour tana jiransu ta karaso ta kwanta jikinta tana gaidata da fara'a Maamah ke answer wa tana rubbing hannunta a fuskar Afaf, da sallama ya shigo parlour, Maamah ta mik'e tana nunashi da hannu tace " Come closer"  ya k'araso tace " Sonake yanzu ka durku'sa ka bawa Afaf hak'uri " Da sauri ya d'ago yana kallon Maamah kafin ya tsurawa Afaf dake ta masa murmushi ido...bakinsa har rawa yake yace "Ni ? Maamah....." Saurin dakatar dashi Maamah tayi ta hanyar  daga masa hannu.





Cute😍

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now