Mowar miji ( Borar Danginsa) 30

1.1K 75 4
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

_yeeee today is the beginning of another year, may the blessing of Allah be with us through out the year.. Ameen_
 

30

Da sauri Maamah ta shige room d'inta, wayarta dake ringing ta dauko murmushi tayi ganin sunan wadda yake kan screen d'in, she's willing to call her dama, *Gaji* (Friend din mamah ce da suka hadu a umarah, itama Gaji batada matsala a duniya data wuce in-law d'inta), Mamah tayi picking da sauri, a daya bangaren akace "ya ake ciki? Sun tafi?" Mamah ta k'ara fadada murmushin ta tace "May be ma sun shiga plane fa, amma har tsawon wani lokaci zai dauka be dawo normal self Nashi,ina jin tsoro fa kar ya sake shi da wuri ya yiwa yarinyar mutane illa" Gaji tayi wata dariya tace "Haba mana, believe me Wallahi Sai ya dade be sake shi ba na Saba amfani da Wannan maganin ae, ni nayi mamaki ma da baki fadamin Wannan case d'in ba since, da tuni an wuce gurin" Mamah ta sauke numfashi tace "Kedai Bari kaina ne ya Kulle ai" daga nan suka gama hirarsu sukayi hanging. A can airport kuwa tsayiwar befi 30 mnts ba sukayi plane d'insu ya daga dasu Germany, Afaf sai wani shige wa Ameer take wai sanyi takeji, though Ameer isn't himself but yaki sakewa da Afaf, yana ji tayi wrapping jikinsa da hands d'inta, yayi shiru yana sauraron karatun Qur'an ta cikin wayarsa.
A bangaren Simbiat ko ganin har ba'a di salatil asr Ameer be zoba duk tavi ta daga hankalinta, ko abincin kirki bata civa, ga twins ma sai kuka suke suna ta wutsilwutsil da kafafunsu, shigowar Ammi yasata saurin dagowa tana wiping tears, Ammi ta fahimci tana cikin damuwa ma tun dazu ganin yadda dazun taketa faman duba wayarta, zama Ammi tayi tace "Simbiat har yanzu baki samu wayar Ameer din bane?" Simbiat tayi saurin girgiza kai, Ammi ta dafa shoulder d'inta tace "karki min karya mana, Ameer bezo ba Kuma baki samu wayarsa ba, Kiyi hak'uri zaizo insha Allah", nodding kanta tayi tana wiping tears tace "Toh" Ammi ta mik'a mata baby girl tace "Kiyi feeding d'inta yanzu, sannan ki bud'e abinci kici", karban baby tayi ita Kuma Ammi ta mik'e ta fita.
Side d'in Daddy Ammi ta wuce, yana zaune yana karatun news paper, kallon face din Ammi yayi da duk ta nuna alamun damuwa yace " Lafiya dai?" Ammi ta zauna tace "Har yanzu Ameer be zo ba Kuma Number d'insa baya shiga" Daddy yayi Jim alamar tunani kafin yace "Ko zuwa zanyi in duba shi?" Ammi tace "Eh da sauri" yayi murmushi kawai ya rufe news paper din ya fice itama tabi bayansa.
Sai 8;00pm su Ameer sukayi landing a airport, taxi suka nema ya kaisu nearest hotel, suna shiga Ameer ya wuce toilet yayi wanka, time din daya fito Afaf ta shiga. A tare sukayi dinner basa hira Sam Wanda hakan ya dan damu Afaf, sanda suka kammala Afaf ce ta gyara gurin, ta karkade bed tana kallonsa tace "Bacci fa?" A takaice yace "Ba yanzu ba" tayi murmushi ta k'araso inda yake ta haye kan laps d'insa tana shafa side burn d'insa tace " Haba dai! A jin ka Zan iya bacci ba kaine?" Jim yayi kamar Ba zeyi magana, ranta ya Dan sosu, can Kuma taji yace " kije ki jirani in gama abinda nake" ta karbi wayar Hannunsa a shagwabe tace "O"o ni sai kazo mun kwanta" ya dinga kallonta kamar yana son gano wani Abu, ta marairaice tace "Dan Allah" dagata yayi a jikinsa shima ya mik'e, direct kan bed ya kaisu suka kwanta suna facing juna kafin a hankali Afaf ta matsa jikinsa ta rungume shi, lumshe ido yayi yana ji tana rubbing hands d'inta all over his body, kafin Kuma ta saka lips d'inta ta kama Nasa tana tsotsa, a hankali shima ya fara shafata, daga nan Kuma Afaf ta samu yadda take so ...{ *Wayyo ina taya Seemby kishi wollah* }.Seemby gaba daya ta kasa runtsawa tunda ta kwanta take juyi, ta rasa abinda yake mata dadi a duniya, bata taba tunanin Ameer ze iya juya mata baya ba, to akan me? Ta tambayi kanta, a iya sanin ta dai batayi masa lefi ba, hasali ma cikin farin ciki suka rabu dashi, har asuba bata samu tayi bacci ba, koda ta idar da sallah addu'a tayi Allah ya saka mata dangana akan Ameer tunda Mamah tace vazai dawo gareta ba.

Germany

A tare Ameer da Afaf sukayi wanka haka sallah shi ya musu jam"i, sukayi addu'a kafin Ameer ya mik'e ya fice reception, gaba daya wani iri yake jin kansa kamar dai akwai wani Abu daya rasa a rayuwarsa. Afaf tana ganin ya fita ta dauko wayarta, number Mummy tayi dialing tana picking tace "mummy na samu Ameer yadda nake so,da alama dai ya manta da waccan mayyar" Mummyn ta tace "alhmdlh.. Though tafiyar da akayi ko sallama Ba a mana ba" Afaf ta shagwabe tace "Kai mummy ae tafiyar bazata ne, ni kaina bansan dashi ba, Maamah ce  ta shirya komai da kanta, abun mamaki Wallahi" Mummy tace "Na San komai Afaf, kedai kar Kiyi wasa da damarki ki koya masa sonki kafin ya dawo hayyacinsa kinji" Afaf tayi dariya tace "Consider it has been done Mum", jin motsin mutum a bakin k'ofa yasata saurin hanging, tasaka murmushi akan face d'inta tana kallon Ameer daya shigo tace " Sweetheart we're have you been since na leka ban ganka ba" yayi murmushi yace "naje reception ne, amma kamar waya kike ko?" Tayi rolling eye balls d'inta tace "eh da kawata ne Seemby" da sauri ya maimata "Seemby" ta zaro Masa ido tace "Kasan sunan ne?" Yace "Yeah the name seems familiar" cikinta ya juya, kar Mutumin nan ya dawo dai-dai yanzu fa, sai taga Kuma ya daga shoulders d'insa yana murmushi ya wuce toilet.

3 days later

Yau kwanan twins 6 amma har yau ba aji Ameer ba, Seemby tayi kuka har ta gaji, tun ta nayi a boye har ta fara fitowa fili, Daddy tun ranar Kwana 2 yaje gidansu Ameer akace Daddynshi baya gari, don haka yasa Jafaar yaron friend d'insa ya siyo masa big two rams da sa Babba. Shirye-shiryen suna ake a gidan kamar kowa bashida damuwa a ransa, yan uwan Daddy duk sunzo daga Maid haka yan uwan Ammi na Kaduna da jimeta.Ranar suna tun safe aka dora tukunya a gidan su Seemby, sai savga ake, Seemby kam tana daki duniyar gaba daya tayi mata zafi, tunanin dalilin da zaisa Ameer yaki zuwa ganinsu duk ya hanata sukuni, tana haka Aunty Fareeeda Sister din Ammi ta shigo, hannun da Seemby tayi tagumi ta cire tayi kasa da murya tace "Meye haka Seemby? Har yanzu fa baki shirya ba" Seemby ta fashe da kuka tace "Ni Ku rabu dani pls, Meyasa bazaki duba halin da nake ciki fa, kwalliya ae bata kama ni ba" Aunty fareeda ta zauna ta rik'o hannunta tace "Seemby so kike kowa yasan halin da kike ciki kenan ko?" Ta girgiza kai, Aunty ta Dora "To ko dole ki saki ranki kiyi walwala Seemby, Allah ze kawo karshen komai soon insha Allah" ta k'arasa tana wiping Mata tears, kafin ta tashi da kanta ta had'a Mata ruwan wanka ta rakata toilet ta fito, Ammi da kanta ta wanke twins ta shirya su, a time din gidan ya fara cika, don ina iya hango su Ameenert, Sadíyyáä,da Amrath na zbi, Amzeey, sa"adath, Ummu Zainab,  memcyluv da Aunty Ameena Kaura duk sun jeru suna cin rengem.

A Germany kuwa yau gaba daya Ameer wani iri yake jin kansa, gaba daya fever ya dañneshi ya kasa ko tashi kan bed tun bayan wanka da yayi yake kwance yana kallon Afaf tana ta zirgazirga, cikin tafiyar daukan hankali Afaf ta k'araso inda yake, kwantar da kanta tayi kan kirjinsa tana shafa lips d'insa tace "Me yake damun Prince d'ina?" Yayi murmushi kawai bece komai ba, ta kara shafo face d'insa tace "Prince me ke damunka?" Yace a takaice "Am having slight headache, buh ze warke karki damu", Gyara kwanciyar ta tayi a jikinsa tace " Nidai bana son kana damun kanka, in Kana bukatar wani Abu you let me know" ya fara shafa ta kawai Ba tare da ya kara cewa komai ba. Can tace "kodai tunanin gida kake?" A hankali yace "Bana tunanin komai idan Ba ke ba Afaf, I love you so much babe" dadi kashe Afaf da sauri tace " I love you more than you love me sweetheart ".

A gidan suna kuwa su zahra Alhassan dakyar suka shawo kan Seemby ta ware itace harda shiga filin rawa, sosai akayi shaani,Daddy ya yanke decision tunda an kasa samun wayar Ameer Bari a sakawa yaron *Muhammad* yarinyar Kuma *Fateema* (Wato sunan Manzon Allah S.A.W da diyarsa Nana Fateema), haka akayi ta sha ani har bayan magrib taro ya watse anata sanyawa yara alvarka. Sai bayan isha Amaal Sister din Ameer ta kira Seemby, ta fada mata tana exams ne a school shiyasa bata zo ba, Seemby Sam bataji tana jin haushin Amaal ba, sai ma godiya da tayi mata sukayi hanging, Amaal kam kunya ne ya hanata zuwa ba exams ba.




Cute💖💖

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now