Mowar miji (Borar Danginsa)

1.3K 85 2
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

*Mistake*
_Nayi mistake jiya ko ku tuna min ko?, I write Imraan instead of Jameel (Abokin Ameer na Florida)...actually i just don't know what comes over me, ....am sorry you change the name pls....thanks for following me_

21

Travel agency Ameer ya wuce kai tsaye,ya Neman musu visa, besha wahala ba kuma ya samu, sai da ya tsaya a *Woodsby's cafe* ya musu ordering *Beef tips with noodles, da meatloaf with gravy*, bayason ma Simbiat tasan Maamah ne tace su dawo, sai da ya tsaya a masjid yayi sallah kafin ya koma hotel, a reception suka hadu da Jameel Wanda sukayi waya yace ya jirasa,sun Dade suna hira sanda Ameer yace gobe zasu koma ba karamin mamaki Jameel yayi ba, beyi tunanin haka ba ya kalleshi sosai dama yaga alamar damuwa a tare dashi yace "So soon Ameer, I guess something is worrying you deep down your heart, please Tell me" Ameer yayi k'ok'arin kakalo murmushi ya dora kan face d'insa yace "Nothing is worrying me Jameel am just tired, I need rest" ya k'arasa yana juyawa alamar yanason tafiya, Jameel ya janyo shoulder d'insa yace "Look Ameer, stop pretending mana, nasan akwai matsala sai dai kuma idan bazaka fada minba" Wannan karon Ameer ya fitoda damuwarsa, amma yasan bazai iya fada masa ba, they're not that closed, they are just friends, sai ya daure yace "Issa personal issue Jameel, buh everything is going to be okay soon insha Allah" Jameel beji dadi ba Sam, Shi a tunaninsa yakai matsayin da Ameer ze fada mishi damuwarsa,they're friend's of two years, zuwa yanzu yaci ace sun yarda da junansu sosai, sai ya daga shoulder's d'insa trying to full away his thought , yace "Ameer Allah ya kawo sauki to, nagode though baka kawo min ziyara ba" murmushi Ameer ya sakeyi, he's just tired of this conversation, he's tired and tired of everything, ya daure dai yace "Am sorry yau nayi niyyar zuwa ai, as ave told you earlier tafiyar bazata ne, amma zan dawo ai sooner or later" daga nan sukayi shaking hands, Jameel ya fice while Ameer ya haura stairs.
Simbiat tana zaune gefen bed tana waya da Ammi ya shigo ya mata sending smile yana k'ok'arin zama kusada ita, zama yayi ya janyota jikinsa yana shafa gashin kanta, shidai yasan yana son Simbiat, yana sonta over , fiyeda yadda uwa take son d'anta baya fatan rabuwa da ita kuma, tausayinta duk ya shikashi Sam batada damuwa a Florida gashi gobe zasu koma, ya rahman! Yace a ransa yana dafe kansa, besan ma Seemby tayi hanging wayar ba sai da yaji tana tapping shoulder d'insa, ya dago da sauri sai kuma ya sakar mata murmushi yana mik'ewa not allowing her to say something, abincin ya dauko musu suka fara ci kowannensu tunani fal zuciyarsa, a haka suka kammala suka mike a tare suka wuce toilet, wanka sukayo da brush suka fito,Sai da suka kwanta ya dago kanta daga jikinsa yace "Babe we're going back home tomorrow insha Allah" gabanta ya mugun faduwa she don't want to go back kuma, tafi son nan bawani fargaba, kasa cewa komai tayi ta maida kanta jikinsa, duk jikinta ya mutu, kasa cemata shima yayi, shiru ya ratsa room d'in a haka bacci ya d'auke su.
   Washe gari as early as 7:00am suka gama shirinsa na tafiya Seemby kamar zatayi kuka tace "Yaushe zamu dawo kuma" ya mata murmushi yace "Soon insha Allah, Yanzu ma a company aka nemeni fa, mu da zamuyi month, zamu dawo definitely" murmushin itama ta masa taja trolley har k'ofar hotel, taxi suka hau Ameer yace a kaisu *Savion's place* suci wani abu kafin su wuce tunda basuyi break ba. Fried plantain yaci ita kuma taci sweet potato mash suka wuce Airport a gurguje.
11:03pm Flight d'insu ya sauka a airport, Number Mahmoud Ameer ya kira ya fada masa sun sauka, bayan kamar 20mnts Mahmoud yazo daukansu, cikin mota Mahmoud sai bawa Ameer labarin fadan da Mamah tayi ranar da taje gidansu yake,duk takaici da kunya suka addabi Ameer ya kasa cewa komai, itako Simbiat sai murmushi take, a haka suka k'araso gidan, Afaf tana parlour as if tasan suna dawowa a lokacin, ta bisu da wani matsiyacin kallo tana murmushi Wanda suka kasa fahimtar ma'anarsa, wanka sukayi suka kwanta, saidai Ameer ya kasa bacci fargaba duk ya hanashi sakat yasan ba karamin Aikin Maamah bane tazo har gida gobe ta musu wankin babban bargo, juyawa yayi ya kalli Simbiat dake baccinta peacefully ya dora hannunsa kan cikinta daya d'an taso ya dinga shafawa kafin ya matso da fuskarsa saitin cikin yace a hankali "Babe can you hear me? Hope you're fine and okay!you  Know that Daddy loves you more than expectations, your love is unstoppable to me, you're my everything sweetheart, daga haka yayi kissing cikin ya koma ya kwanta.
  Washe gari misalin 8:40am suna breakfast sai ga Maamah kamar an Jefota ta dinga binsu da mugun kallo, jikin Simbiat har rawa yake ta durk'usa kasa tace "Sannu da zuwa Mamah ya hanya?" Maamah ta watsa Mata kallon tsana tace "Bansani ba" Ameer ya marairaice yace "Maamah ai da baki zoba, zamuzo anjima fa" ta zaro ido tana dafe bakinta tace "Ni! Ameer ai ban isa ba tunda dai kasa kafa ka bar kasar ma gaba daya without my knowledge ai ban isa kazo inda nakeba" ya shafa kansa yace "Maamah tafiya ne ya zomin a bazata, kuma na nemi number ki ban samu b...." Da hannu Maamah ta dakatar dashi, tace "Ni zaka rainawa hankali Ameer? Nace ni zaka rainawa hankali?" A tsawace take maganar, sai kuma tayi murmushi ta nuna Simbiat tace "Wannan bakar munafikar ce ta koyama karya hala?" Ameer yayi saurin cewa "Mamah please stop insulting her, batada lefi fa, nine me lefi kuma nine d'anki ni zaki yiwa fada" Maamah ta rik'e baki mamaki duk ya cikata tace "Akan wannan zaka fadamin magana Ameer?, lallai wuyanka ya isa yanka Ameer,kasan Allah sai na kawo karshe wannan aure soon" daga haka ta wuce room d'in Afaf wadda tunda Maamah ta shigo ta fito a idonta akayi komai, gwalo tayiwa Simbiat ta juya tabi bayan Maamah.Simbiat dafe kanta kawai tayi ta koma ta zauna, Ameer kam yafi k'arfin minti 2 a tsaye, besan ma wace kalma zeyi amfani da ya bawa Seemby hak'uri ba, a hankali ya durk'usa a gabanta, ya riko hannunta ta fisge da sauri tana binsa da mugun kallo, kara k'ok'arin riketa yayi ta mik'e a fusace ta nunashi da yatsa a tsawace tace "Ka rabu dani malam karka kara tabani, duk kai ka janyo min komai ai" daga nan ta fashe da kuka ta haura stairs da gudu.
Yau kwana biyu da zuwan Maamah gaba daya Simbiat ta canjawa Ameer bata kulashi bata girki dashi, bata bari ya tabata, ko dakinta ma bata bari ya shiga, yauma kamar kullum Ameer ya dawo daga office, room d'inta ya wuce directly tana zaune da Qur'an a hannunta, ya zauna a gabanta yana kare Mata kallo ta rame sosai kamar yadda shima ya rame, bata ko kara kallonsa ba tun kallon da ta masa na farko haka kuma bata fasa karatun ba, zama yayi tayi a gurin har bayan minti 5 sannan ta idar, mik'ewa tayi ta maida Qur'an din kan study table ta haye kan bed ta kwanta taja blanket ta rufe har fuskarta, a sanyaye Ameer ya biyota gadon ya yaye bargon, ta mike da sauri idonta har rufewa yake saboda masifa tace "Sau nawa zan ce maka ka dena shigo min room? Ka tashi ka fita wallahi" kallonta kawai yake, Ashe ma ta iya masifa amma bata yiwa Afaf, ta fusata ta tureshi daga kan bed din har yana bigewa da stool data ajiye gefen bed, ya bud'e baki zeyi magana ta fashe da kuka tana turasa daga room d'in, bata bar turasa ba har saida ta kaishi parlour sannan ta dawo tayi banging k'ofarta. Afaf dake tsaye tun sanda Simbiat ta fara masifa ta fashe da dariya tace "Ikon Allah ni Zainab ina ganin Abu,Abu baya ganina a gidan nan, namiji ba aji!wai!" Ai da gudu ta koma room d'inta ganin Ameer ya nufota da sauri, a tare suka shiga room d'in, Ameer ya sawa kofa key, ya fara matsowa inda take, ai ko ta fasa kara tana yin hanyar toilet, yayi saurin fisgota ya matse bakinta yace "Yaushe na fara wasa dake Afaf?" Afaf ba baki sai idanu data firfito dasu waje, ya cigaba "Kece Annamimiyar data hadani da Mamah ko?" Ya sake mata bakin yana son jin wani abu a bakinta, ta dinga maida numfashi tana goge lips d'inta da hannu, yace "Ba dake nake magana ba" a tsawace, Afaf ta durk'usa kasa tace "Dan Allah Ameer kayi hak'uri, ni bani na fada mata ba, ita tazo bakwa nan fa" ya dinga binta da mugun kallo yace "Gate man ya fad'a min kin fita, ubanwa ya baki izini" da sauri tace "Ummi ce ba lafiya naje, kayi hak'uri Dan Allah" sai da taso bashi dariya, ya maze ya fice da sauri, yana tunani Ashe ma karamar yar iska ce ita, zeyi maganinta soon.......




Cute💃🏻

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now