Mowar miji (Borar Danginsa)

1.4K 74 6
                                    

👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

19

Sai bayan magrib Ameer ya koma room d'insu, a time din Simbiat tana waya da Amaal ne, zama yayi yana kallonta har ta gama kafin ya dawo kusada ita ya hade rai yace "Meyasa kika kira Amaal idan ta fadawa Maamah fa?" ba tareda damuwa ba Simbiat tace " To meye a ciki? Ba gwara haka ba? Ai na fada maka na gaji mukoma ka nemi yafiyar Afaf komai ya wuce" ido Ameer ya tsareta da yana imagining sake bawa Afaf hak'uri a karo na biyu a rayuwa, chaiii...this will never be possible, ko wancan ma ai Maamah ce ta matsa ya bata hakurin, sai kawai ya mik'e ba tareda ya kara cewa komai ba ya haye bed ya kwanta hadeda lumshe idonsa, Simbiat ma mik'ewa tayi ta hauro kan bed din, ta kwanta ajikinsa kanta a saitin kirjinsa har tana jiyo heartbeat d'insa, tasan dole ya shiga wannan halin tunda bayason Afaf, amma bashida yadda zeyi da yawuce  yayi hak'uri ya karbe a amatsayin matarsa tunda ita tana sonsa, babu shakka zata masa biyayya idan ze nuna mata kulawa, sama Simbiat tayi a jikinsa fuskanta dai-dai da nashi, ta tsura masa ido tana k'ok'arin samo Kalmar zata fada mishi, shima idonsa yasa cikin nata, da alama jiran jin me zatace yake, ta daure tace "honeybun ai kana sona ko?" Shiru ya mata, ganin bashida niyyar kulata yasa ta cigaba "Dan Allah ka daure ka rage kiyayyanyan Afaf a ranka, ka sauke haqqinta dake kanka for my sake please" nan ma shiru ya mata, gaba daya kuma maganganun suka k'are Mata itama sai tayi shiru ta koma ta lafe a jikinsa,sai anan ya motsa, yasa hannayensa duka ya rungumeta sosai, shiru ya ratsa room d'in, Wanda kuma ya bawa bacci daman sace Seemby.
Washe gari, seven suka kammala shirin su don tun asuba Ameer ya fadawa Simbiat ze kaita different places, yanaso tasan tazo Florida, a tare suka sauko daga stairs, tayi gaba ta bar Ameer yana gaisawa da ma'aikatan hotel din, *Single Creek regional park* suka fara zuwa, gurin yayiwa Simbiat kyau sosai, tasa hannu ta rufe bakinta tana karewa park din kallo, green is bae...gurin yasha grass carpet ga pool kala-kala, ga wani kamshi da sanyi na musamman da yake tashi a gurin, komawa kusada Ameer dake ta mata dariya ganin ta kasa rufe bakinta tayi tace "Flame let take some snaps" Ameer yaji dadi Simbiat tana farin ciki, be cika son photo ba amma haka ya tsaya ta dinga musu pics kala-kala, 1hour kawai sukayi spending a gurin suka tafi, Simbiat a cikin taxi ta kalli Ameer tace "please dear muje wani gurin kuma, ban gaji da yawon ba, Gaskiya Florida yanada kyau" Ameer ya janyota jikinsa yace "Na sani ba, dama nace miki you most enjoy it been here, Florida yayi sosai,ko kinaso ki dawo nan da rayuwa?" Ta dago tana masa murmushi tace "How I wish it'll be possible in dawo din, surely zan dawo and lemmi tell you buh don't laugh at me pls" ta karashe kamar zatayi kuka, yayi Mata nodding kai assuring her he'll not, ta cigaba "Idan na dawo Florida da rayuwa sai after five..five years zan dinga zuwa ganin gida" duk yadda Ameer yaso mazewa kasawa yayi sai ya fara dariya, sai da yayi me isarsa kafin ya dawo da kallonsa gun Simbiat data cika faam, yace "Babe to Ammi fa? Ko idan kin dawo nan mantawa da kowa zakiyi?"  Sai anan ta tuno Ammi, wai! Ai bazata iya hak'ura da Ammi ba, never in her life tana duniya dai tayi koda month ne bataga Ammi ba bare kuma 5years tayi saurin cewa "Sai na dinga aikawa tana zuwa after every 2weeks at least" murmushi Ameer yayi kafin yace wani abu yaga sun zo dai-dai  *Brevard zoo* sawa yayi me taxi ya ajiyesu suka shiga,  wow! Seemby tace, cage din monkey suka fara zuwa Ameer ya durk'usa ya dauko banana cikin wani basket a bakin cage din, barewa yayi ya fara feeding monkey din, Simbiat kam bata komai sai Aikin snapping Ameer, daga nan suka wuce gurin birds suka duk suka dinga feeding dinsu, sosai Seemby tayi enjoying Zoological garden din, ta dinga farin ciki, haka suka dinga daukan pics da Animals kala-kala, nan ne ma suka Dan bata time don sunyi kusan 3hours, daga nan kuma  *Reptiles discovery center* suka wuce, they've seen a lots of reptiles there, Seemby just can't describe how she feels, yau kawai yasa taji bata son ma komawa gidan data damu a koma, suna barin gurin kuma suka wuce Wani karamin masjid dake kusada gurin don yin sallar magrib kuma, bayan sun idar suka fito, Ameer ya kalli Simbiat yace "Babe kin gaji?" Tayi rolling eye balls d'inta tace "Bazan taba gajiya da yawo a Florida ba" murmushi Ameer yayi mata yace "Okay then... Cinema muka nufa yanzu" farin cikinta is undescribable a wannan lokacin, ta rik'e hannunsa gam, tace "Mu tafi to" daga nan suka nemi wani taxi din suka hau, sai da sukayi nisa ya tuna ko abinci basu Ciba yau duk, bayan breakfast da sukayi, ya kalli Simbiat data maida kanta jikin glass tana kalle-kallenta yace "Babe are you not hungry?" Bata dagoba bare ta kalleshi tace "Am not" yayi murmushi yasan farin ciki ya hanata ji, Yanzu kuma tasan inda suke heading bazata yarda su tsaya suci ba, yayi deciding kawai saci a can sai yayi mata shiru yana kallonta, lokaci lokaci take dauko wayarta tayi snapping gurin daya burgeta.
Dai-dai *Tourchstars cinemas* suka tsaya, fitowa sukayi daga taxi suka shiga ciki, Masha Allah! Simbiat tace da suka k'araso gurin, hatta chairs na gurin na daban ne masu azabar kyau, ta dinga karewa gurin kallo most of Wanda suke gurin couples ne, zama sukayi Ameer ya musu oder vanilla ice cream, sosage  roll and popcorn, basu wani dade da zama ba koma aka fara showing movie, aww....movie yayi kyau, Simbiat bata San tace "So romantic... How I wish..." Ba, sai da Ameer ya tabota yace "What?" Sai anan ta tuna me tace ta rude cikeda kunya ta cusa kanta a jikinsa tana dariya kasa-kasa...


Cute💞

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now